Uncategorized

ABDUL JALAL PART 1 HAUSA NOVEL

Share please
More comments more typing……………..

Ina alfahari daku masoya wannan novel
Irinsu
Jamila
Zakiyyat
Ummu hanif
Mabruka
Zainab
Da wannan tsofaffin Fatima zahras
Da duk members Na ABDUL JALAL NOVEL FANS
Wanda na fada da Wanda ban fada ba nasan daku ina alfahari daku

????????????????????
[8/31, 8:26 AM] Safiyya: ????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????

_ABDUL  JALAL_
       (2020)

  _WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_
(Daddy's girl)

           PAGE-  19

PART 1

_Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam)
Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa’azantarwa, ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa.
Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi

Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode.

Domin Samun karanta wannan littafin yi magana ta what’s app akan wannan lambar

07063065680
Kokuma addanna wannan link din domin samun novel din

????https://chat.whatsapp.com/EtB4KI52K0v5FQc2ELhidL

I want comments not stickers or just thanks????????????????
Your comments give me courage

    -My First Novel-

Malamai ne suka jeru suna shirin janyowa Jalila inda zata karanta
Itakam tayi shiru ta kurawa camera ido haka nan taji gabanta na faduwa dukda tasaba zuwa musabuka amma takejinta wani iri

Jalal ne ya kurawa TV ido gani yake kaman shi Jalila take kallo so yake ya tabbatar itace kuwa a jikin allon TV kokuwa kamrun dayasha ce tafara gaya masa karya(giya)
Ita kam Ilham kara shige masa take tana kuma zuba masa Wayne tana mika masa
“Ilham ki kyaleni please”
“Yaya J why?”

Tayi maganar tana kuma kwanciya a jikinsa
Shikam yakoma kaman wani karamin yaro
“Bana so Ilham ki kyaleni kwanciya zanyi kaina ciwo yake”
Dan dagashi tayi ya koma ya kwanta akan kujerar yana kallon TV kasa²
A hankali Ilaham ta mika hannunta tana shafa sajensa
“Sannu Yaya J”
Gyada mata kai yayi

“Ilham karki kuma saka turaren nan inzakizo inda nake banaso”
Yai maganar a hankali
“To na dena”
Tv ya kuma kalla Jalilan ce dai sedai wannan karon annurin fuskarta ya gushe ta dai²ta nutsuwarta aka janyomata inda zata biya
A hankali tayi bismillah tafara karanto Qur’ani cikin sauti me dadi
Ture Ilham yayi daga Jikinsa ya lumshe idonsa jin sautin karatun nata yake yana ratsa ko ina na jikinsa yana saukar masa da nutsuwa Ji yayi kasalar tana sakinsa duk yayinda ya bude Ido seyaga kaman Jalila shi take kallo jinsa yake kaman ba Shiva
Ilham hannu ta kuma mikawa zata taba shi ya daka mata tsawa
“Ke wace irin banzar yarinya ce waima tukuna me kikemin anan gurin ne tashi kibar min daki kafin in zaneki banza kawai”
“Haba Yaya amma
” bazaki fitan ba kenan kalli Tv duk rawar kanta kalli yadda take karatun Qur’ani gwanin burgewa keko sha³ baki iya komaiba se hauka get out from my room”
Idonta ta kai duba kan Tv Jalila tagani tana zuba kira’a kaman ba itace me shegen surutu da Neman magana ba, wani abu taji yazo ya tokaremata zuciya wato tun dazu da ya kurawa Tv ido ita yake kallo kenan
Wani mugun kallo taimasa
“To ai gara ni inazuwa Islamiyyar kai………..
Bata rufe bakiba yasaka kafafuwansa ya take nata kafar wani irin ihu tayi da karfi kuma yaki dagawa
” Dan girman Allah kayi hakuri, wallahi bazan kuma ba”
Kara takesu yayi
“Dan ina daga miki kafa ina nan a Jalal dina da kikasani, yanzuma Sa a kikaci da wallahi sena zaneki da belt, tashi kifita wawiya kalli rigar jikinki sokuwa kawai”
Da kyar taja kafa ta fita kafarta se zugi takeyi ta koma dakinta ta hau gado ta kama kuka
Wani uban tsaki ya ja yanemi guri ya zauna
Tashar da suke haska musabakar su Jalika sun tafi talla dan haka
ya dauki cup din giyarsa ya cigaba da sha yakuma zubawa ze sha aka kuma hasko Jalila haka nan se ya aje giyar hannunsa shima ya kuramata ido, yanayin Jalila ne ya nuna kaman bata da nutsuwa
Aka kuma janyomata karatu amma tayi shiru ta tafi tunani kowa ita yake kallo
Jikinta ne yayi sanyi jitake kaman wani abune ke shirin faruwa, mafarkanta datakeyi yan kwanakin nan ne suke fado mata a rai taji gabanta yacigaba da faduwa.
a hankali tayi ajiyar zuciya ta Dora inda aka janyomata da karatun ta cikin birgewa

Bacci ne yafara fusgar Jalal dan haka anan gurin ya zube ya lumshe ido yana sauraren karatun Jalila har bacci yayi awon gaba da shi

Da safe Jawwad ne yazo ya tarar dashi yana bacci a parlour a kasa kan carpet ga kwalbar giyarsa yasha fiye da rabi
Girgiza kai Jawwad yayi
“Allah ya shiryeka Jalal”
Yasa hannu ya kwashe kwalbar da kofin ya fita dasu ya dawo ya tashi Jalal don yasan be salla ba balle ya karya
Hannu ya kai ze tasheshi yaji kansa yayi zafi, bayansa ya Dan bubbuga a hankali Jalal ya bude ido ya mayar ya lumshe
“Ka tashifa gari yayi haske kayi salla kazo mu karya”
Jalal ne yake tunano abubuwan dasuka faru jiya da daddare gaskene kokuma mafarki yayi ji yai kansa yakuma sarawa

“Kaina ne yakemin ciwo sosai Jawwad”
“Sannu ka tashi in muka karya seka sha magani”
Da kyar ya lallabashi yaje yayi wanka yai sallar asuba, Jawwad ya dakko musu Abinci

Ilham CE ta fito tana taka kafa da kyar mummy ta kalleta
“Meyasameki kike taka kafa da kyar”
“Dutse na taka jiya a garden”
“Subhanallah bakiji ciwo ba dai ko?”
“A a banjiba kafar ce dai kawai take ciwo”
“To ko asibiti za a kaiki a duba kafar”
“A’a mummy zata dena ne Insha Allah”
“To shikenan ni zan fita ne zanje ganin likitan Ido, ga breakfast can na gama in wancan Dan zeci yazo ya dauka kema kije ki dau naki”
“To mummy adawo lafiya”
“Allah yasa”
Mummy ta fita

Jalal ne ya dakko wayarsa ze kira daddy yaga message ya shigo wayarsa Dan haka ya bude message din bakuwar lambs ce

  "Barka da safiya jarumin      
    maza fatan kana lafiya        
   Zanso ace a halin yanzu 
   Muna tare ina kallon                  wanna kyakykyawar fuskar
  Amma lokaci na nan zuwa
   Dazamu kasance tare kaji          Dadinka masoyina 
         From ur lovely bae"

Wani uban tsaki Jalal yayi
“Nasan Ilham ce zataci kaniyarta zata gane innin sa,’anta ne”

“Ya dai meyafaru ne kake surutai haka”?
Jawwad ya tambaheshi
“ba komai ci abincinka kawai”
Ya mike ya nufi cikin Gida tundaga parlour yake kiran sunan Ilham amma bata nan dakinta ya nufa yana zuwa ya tarar tana dakinta tana karyawa
A firgice ta dago tana kallonsa

“Uban meye wannan kika turomin a waya wai meyasa ba kyajine Ilham”
Kallonsa tayi cikin rashin fahimta
“Wane sako kuma ni ban turomaka komai ba”
Ransa ne ya kuma baci wato raina masa hankali zatayi gadan² ya nufi inda take da niyyar ya ci kaniyarta
Ta mike tsaye tafara kuka tana
“Wallahi Yaya bansan laifin danayiba”
Yana karasowa Inda take yaji tana warin wannan turaren na jiya kansa ne ya Sara yaji yana Neman ya fadi, da sauri ta taho inda yake
“Yaya menene?”
“Dalla tsaya karki karaso inda nake”
Bango ya daddafa yabi kofa ya fice da kyar ya koma part dinsa Jawwad ne ya ganshi ya rike kai yana dafa bango
“Subhanallah Jalal kanne dai”
Jawwad yafada yana riko JALAL
“Jawwad kaina kaman ze fashe”
“Bari mu tafi asibiti ina key din motarka?”
“Kaga kyaleni bazani wani asibiti ba”
“Meyasa meye amfanin ka zauna a Gida baka da lafiya”
Guri Jalal yanema ya kwanta ji yake duniyar tanata jujjuyawa
Kai tsaye cikin gidan Jawwad ya tafi ya nufi part din daddyn Jalal yasameshi a parlour yana breakfast
Suka gaisa Jawwad yagaya masa halin da Jalal yake ciki, tare da daddy suka taho gaba daya part din Jalal
Suka tarar dashi a kwance yanata juyi akan gado ya rike kai Juyin duniya ya tashi su tafi Asibiti yace baza shi ba kunsan mutumin da taurin kai
Se wani likita aka kirawo yaimasa allura se yasamu yayi bacci

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button