Uncategorized

ABDUL JALAL PART 1 HAUSA NOVEL

“Tsinanniyar yarinya ta jamana duka ta gudu shegiya azzaluma wallahi ban yafe ba”
Cewar wata daliba aikuwa a fusace siyama ta juyo

“Allah ya isanki ta biki haba lubabatu ai ba matsa bakinki tayi tace kiyi magana ba kuma Jalila ba shegiya bace”

“Nafada wallahi ban yafe ba”
Lubabatu ta maimaita
“Ke nima ba yafewar nayi ba wallahi wannan azabar dukaa itakuma ta gudu”
Wata dalibar tayi magana Siyama na kokarin tarewa Jalila wasu suka hayayyako mata ana haka Sega Jalila ta dawo gaba daya sukayi tsit saboda sunsan hali indai bakine Jalila akwai baki
Ba’a kada ita a fanni surutu
“Yanaji ana surutu amma ina shigowa naji anyi tsit”
“Aminiya ba komai hira kawai mukeyi,
Amma fa malam Naziru yace yau in yakamaki kashinkj ya bushe”
Siyama ta fada tana dariya
“Hh base ya ganni ba ai bazan bari mu haduba indai yaune”

Ilham ce ta sha kwalliya kaman ka saceta ka gudu se karairaya take ta shirya abinci a Warmer’s ta nufi part din
Jalal ba kowa a parlour dan haka ta aje a parlour ta karasa bedroom dinsa
Dogon wando ne ajikinsa se vest ya na gefen gadonsa yana ta busa shisha
Sallama tayi da mamakinta taji ya amsa, a hankali ta tako gabansa cikin iyayi tafara magana
“Yaya dama mummy ce tayi girki tace in kawo maka”
“Ina abincin”?
Yai maganar kaman ba yaso
“Yana parlour”
Gyada kai yayi
“Thank you”
“Amma zakaci ko?”
“Maybe”
Shine kawai abinda yace seda ta juya zata tafi ya daga kai ya kalleta
Ganinta yayi kamar wata balbela, gashi se wani kariraya takeyi sam bata da wani shape se tsawo amma fara ce tas
Murmushi yayi a ransa yarinya Karama amma ta iya wannan shirmen ya Dan ja tsaki
Itakam fita tayi tana addu’ar Allah yasa yaci abincin nan

Kamar yadda Jalila tafada har aka tashi bata hadu da malam Naziru ba sunyo ayari guda yan ajin su daba yan ajinsu ba kowa na kokarin bin hanyar gidansu,
Anzo layinsu lubabatu suka tarar da yayan lubabatu a bakin hanya da abokansa se shan sigari suke ga tarin karnuka a gabansu kaida kagansu kaga yan daba
Jalila tare suke tafiya da su lubabatu seda sukazo dai² inda matasan nan suke Jalila secewa tayi
“Tab Siyama kinsan wani abu
ga irinsu Jalal da gayyar abokanan Sa baki kullum cikin hayaki, kalli yadda bakin yayan lubaba yayi saboda zukar taba lebensa duk ya zazzage,
Ni bansan ya akayi bakin Jalal bezama haka ba wai shantu”

Wata ashar yayan lubaba yasaki yayo kan su shida abokanansa tareda karnukan kankace meye wannan ayarin yan makaranta sun watse ba kowa a hanyar
Jalila ta dinga dariya yan mata manya da kanana sun zage sun kwashi gudu
Sukace gaskiya gobe insha Allah se mun kai karar yarinyar nan gurin malam aja mata kunne
“Jalila lafiya kike ta haki haka ?”
“Bakomai Ummi karnukan bakin anguwane suka biyomu”

Jalal ya bude Warmer’s dinda Ilham ta kawo yaga cous² tsaki ya ja lallai ma yarinyar nan tasan bayacin wannan abun amma shine aka kawo masa rufewa yayi ya tafi gidansu Jawwad Dan samun abinda zeci a can
Ya tarar Jawwad yatafi masallaci dan haka ya nemi guri ya zauna yana jiran dawowarsa

Wayar Jawwad ce ta dinga ringing ta cikawa Jalal kunne Dan haka yaje ya dauka da nufin fadawa me kiran me wayar baya nan
Ya daga wayar yasaka a kunnensa

“Hello yayana “
Shiru yayi be amsa ba
“Yaya Jawwad yanaji kayi shiru bakajine?”
“Bashi bane”
Ya bata amsa a takaice
“Au Ashe Kaine ya akayi kafasa tafiyar,
Kacigaba da rashin ji kana biyewa abokan banza wataran se sun jaka inda zasu kasheka”

Share please
More comments more typing……..

????️????️????️????️????️
[8/31, 8:26 AM] Safiyya: ????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????

_ABDUL  JALAL_
       (2020)

  _WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_
(Daddy's girl)

           PAGE-  18

PART 1

_Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam)
Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa’azantarwa, ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa.
Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi

Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode.

Domin Samun karanta wannan littafin yi magana ta what’s app akan wannan lambar

07063065680
Kokuma addanna wannan link din domin samun novel din

????https://chat.whatsapp.com/EtB4KI52K0v5FQc2ELhidL

I want comments not stickers or just thanks????????????????
Your comments give me courage

          -My First Novel-

“Da kasake ka tafi da yanzu ka gane illar hawayen iyaye”

“Kinmanta kashedin danayi miki game dani ko? Har yanzu baki fasa min shishigi ba ki ji da rayuwarki, ba ruwanki da rayuwata”
Ya katse wayar ya aje tare da fadin
“Jarababbiya kawai, ko ina ruwanta dani oho, zan sauke mata wannan taurin kan”

Jawwad ne ya dawo ya tarar dashi
“Yunwa fa nakeji, find something for me to eat”
“Kamar me kake so”
“Komeye ma amma banda tuwo
Yarinyar nan ta kaimin abinci nazata wani abun kirkin ne ashe wannan abinne dabana ci saboda tsabar ta rainani aikuwa zan koyamata hankali”

“Ai kai abunda baka ci dayawa wanne daga ciki”
“Kaga ni abar wannan maganar me kukayi yau”
“Nima banci abincin ba alala sukayi yau”
“What alala kuma,”

Ya Dan girgiza kai
“Kasan itama bana ci”
“Anyway bari in canza kaya muje restaurant se muci”

“Kar ka kaini inda za abani abunda za bata min ciki kasan bana son jagwal gwalo”
Murmushi Jawwad yayi

“Jalal kaima yakamata ka canza kayan nan kasaka manyan kaya”
“Nifa bana son wannan kayan nauyin isa ta suke da zafi”
“Please dan Allah kasa manyan kaya”

Jawwad ya fada yana Ciro masa wata hadaddiyar Shadda coffee colour yaita lallaba shi har ya yadda ya karba ya canza kayan yasaka shaddar nan,
Ba karamin kyau Jalal yayi a cikin kayan nan ba manyan kaya ba karamin fito da kamalar namiji yake ba Jawwad yaita koda shi, yana masa hotuna yana yaba masa yayi kyau,
Haka suka shirya suka tafi restaurant cin abinci

Jalila ce a office din malamai ta inda suka shiga ba ta nan suke fita ba suna mata fada akan rashin ji
Saboda ankawo kararta akan jiya ta tsokanowa yan uwanta dalibai yan daba, masu zaginta sunayi irinsu malam Naziru, masuyi mata nasiha sunayi ita dai Jalila shiru tayi batace komai ba suka gama ta tashi ta koma aji tanata cika tana batsewa
Ba a jima ba malam Naziru ya shigo ajinsu da hanzari yana kiranta
“Jalila zancen musabakar nan ne ya taso wadda za ayi a Abuja sati me zuwa insha Allah”
Wani irin mugun kallo Jalila tayi masa tai masa banza
“Jalila da ke nake fa kije ki jadadda hadda abun yazo mana a bazata dukda nasan bani da damuwa akanki”
“Ba inda zani kunemi me zuwa karkuje inja muku magana, yaza ayi kamata taje musabaka “

Tafada tana hade rai
Sekuma ya Dan sha jinin jikinsa
“Wai meye hakane Jalila ana magana kina wani zance daban ina miki magana”
Mikewa tsaye tayi tare da kara hade rai

“Nace fa bazani ba anemi wasu suyi ni bazani ba,”
Ta dau Jakarta ta bar ajin
Office malam Naziru yakoma yana mita
“Kajimin ja’irar yarinya nizata cewa bazata je musbaka ba wai anemi me zuwa”
Malam Yusuf ne yace
“Banga laifinta ba nan kuka sata a gaba da fada bama kai se yanzu kuma bukatarku ta taso kuce tazo tayi muku,
irin wannan yaran nasiha ake musu ba zagi ba duk abu suna da irin baiwarsu”
“Hmm ni ba wannan ba tunanin mafita nake kasan ta da taurin kai abune me wahala taja ga malam baya nan”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button