Uncategorized

ABDUL JALAL PART 1 HAUSA NOVEL

Share please
More Comments typing……………………

????️ ????️ ????️ ????️ ????️
[9/30, 9:37 PM] Ayshercool: ????????????????????????????????????????????????????????????
????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????

_ABDUL  JALAL_

  _WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_
(Daddy's girl)

           PAGE-  53

PART 1

_Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam)
Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa’azantarwa, ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa.

A har kullum ina jinjina da godiya ga masoya wannan novel nawa, comments dinku da addu oinku ina jin dainsu matuka, ina godiya kwarai dagaske,
Domin sharhi, gyara, kokuma shawara a nemeni ta what’s app akan wannan lambar wayar
07063065680

           _My First Novel _

Kasa motsawa Jeje yayi daga inda yake, ji yayi kaman an daddaure shi, yama rasa me zeyi, babu alamun wasa a cikin maganganun yarinyar she has a full confidence, yana hango tsantsar bacin rai dakuma kwarin gwiwa a kwance a idonta, da sauri ya nufi cikin hall din, dan zeso yaga mezatayi
Jalila komawa hall din ta tarar Jalal na shirin yanka cake din, ga gifts da yan uwa suka dinga bashi da abokanansa, da sauri ta koma gefe ta kira Jawwad tai masa magana, sannan ta fita harabar gurin ta nufi motarsu ta bude boot din ta dakko kwali Hannah se rawar kai take ta kafa ta tsare ta janyo wani cake gaban Jalal tanaso lallai shi ze yanka yaci. Announcement sukaji MC yanayi
“Babban yaya, kuma Man of the day, mun samu sanarwa yanzun nan, ance dan Allah ka dakata da yanka cake din nan your sisters want surprise you, zamu zuba ido muga wannan surprise din”
mamaki ne yakama Jalal, sisters kuma wanne kenan. gaba daya hankaline ya koma kan kyakyawar budurwar da take tunkaro stage din, tana taku cike da iyayi da izza kai kace yar wani basarake ce, tana tafe Nana na binta a baya hotuna wasu suka fara yi musu, Jalila ko a jikinta ta karaso kan stage din, Jawwad ya tareta da murmushi, ya kamo hannunta yasata a tsakiyarsu, Nana kuma ta tsaya a gefen Jawwad, ture cake din gaban Jalal tayi ta aje kwalin gabanta, ta fito da wani katon cake, wanda ya sha ado da launin ja da fari, tana gama bude cake din mutanen gurin sukace “Wow” shikam Jalal mamaki ya hanashi magana kallonta kawai yake,
Hannah tace “A a am sorry sister, gaskiya ba za ayi haka ba, wannan cake din naki ajeshi zakiyi, se yafara cin na friends dinsa, yakamata amana kara mussaman ma ni, ko Jalal” Hannah ta karasa maganar tana kallon idon JALAL cike da salon yaudara da jan hankali, Jalila tai murmushi cikin muryarta me cike da shagwaba tace
“gaskiya Yaya Jalal cake dinmu zakaci, kannenka kafin kaci na soyayya” ihu aka dauka ana ta daukansu hoto dan wasu sun zata budurwarsa ce, kodayake abun da mamaki dan sanin halin Jalal na jin kai baze barshi yai budurwa ba, shi mamakine yakama shi
Saboda tsabar gulma yaushe Jalila tafara cemasa wani yaya, shida a bun kirki ma baya hadasu, shine hada wani kawo cake tace ya yanka, ko duk salone na ta bakantawa Ilham, Jawwad aka kira, ya sauka ya tafi amsa waya, Jalal ya kalli Jalila ga Hannah, sannan ya daga kai sukayi ido hudu da Ilham da ta kafe shi da ido, taketa hura hanci, ture cake din Jalila yayi, ya janyo wanda Hannah takeso ya ci, gurin yayi tsit ana kallonsu, ya kalli Jalila yaga yadda ta tsira masa ido, a hankali ya matso da fuskarsa daf da tata yace mata
“ya dai, na canza mikine kikemin wannan kallon? ” banda Jalila, na kusa dashi ma basa iya jin meyace, itama a hankalin tace masa “koka canza din kasan ba birgeni zakayi ba, sedai ka birge makakku irinka, dakuma waccan mummunar kanwar taka jarababbiya, shawara zan baka, dan Allah karkaci cake din nan” “kema ba kyan ne dake ba ai, dan Ilham tafiki kyau meyasa ba kyaso inci cake din, kinfini son rayuwata ne?” ya karasa maganar da wani murmushi na rainin hankali, itakuma tana kallonaa
Hasken camera ne keta haskasu kota ina MC yace “Wannan soyayya haka, atemaka abar manashi ya yanka cake din nan, Jalal me masoya da yawa, jin abunda MC ke cewa yasa Jalila dan ja da baya kadan, gaba daya abun duniya ya addabi Jeje, dama Jalal yanada budurwa ya akayi hakane, amma be taba gaya masa ba, anya wannan shedaniyar yarinyar zata bari komai ya tafi dai2 ga yadda tasa se bata lokaci ake, yana cikin wannan tunanin yaga Jalal ya yanka cake din dasukeso yaci, tafi gurin ya dauka, ana rera masa HAPPY BIRTHDAY TO YOU
Ya yanko cake din har ya kai bakinsa, se yafasa, ya ga gadda Jalila ta kafeshi da ido, ya waiga ya janyo hannun Hannah ya doshi bakinta da cake din, nan da nan ta firgice, amma dayake yar duniya ce seta maze ta rike hannunsa tana murmushi,
Jawwad ne ya dawo kan stage din ya kalli Jalal sannan yace “ya dai an yanka cake bana nan, gaskiya se an sake yankawa, kuma nasu baby za a yanka” ya janye hannun Jalal, ya dakko cake din gurin Jalila, yakama hannun Jalal suka yanka cake,
amma Hannah ta tsargu da irin kallon da Jalal yake mata, dan har tafara tunanin kodai Jalal ya gane me suke kullawa ne.
Ilham kam data san abunda ze faru kenan a wannan gurin da batazoba, domin ranta yayi matuka a baci, an cimata zarafi, kalli abunda Jalila tayi mata, ga abunda sukayi itada Jalal, bayan ita tunda tazo gurin kota kanta bebi ba, gakuma Hannah, yadda ya wani riko hanna ze bata cake, tsabar sun raina mata hankali, bama Jalila tafi uban kowa raina mata hankali ga yadda suke nema su hade fuska kaman zasuyi kiss itada Jalal, abunda ita be taba yi mata ba kuma tana ikrarin ita ba son Jalal take ba, dan haka a fusace ta mike ta bar gurin, ko takan kawayennata bata biba, taje ta hau motar data zo da ita ta fizgeta da gudu, tana tuki kaman mara hankali, idan ta tuno Jalila seta ji zuciyarta kaman tayi bindiga, bata san lokacin da ta fara zubad da hawaye ba, tafara tunanin takanwa zata fara Jalila ko Hannah
Jalal ya yanka cake din gurin Jalila yaci yabawa Jawwad a baki, aka cigaba da cashewa, Jalila tanata lura da cake din nan karsu dauka su bashi. Nana ce ta janyo hannun Jalila zuwa kasan stage din can gefe, ta kalli Jalila tace
“Jalila kinsan wani abu kuwa?”
“A a se kin fada”
“Ilham fa ranta ya baci, abunda kukayi keda Jalal, ta tafi gida a fusace”
“niba wani abu a raina game da wani Jalal, da ta kwantar da hankalinta niba abunda zanyi wannan makakken, nayine kawai saboda Jawwad, kuma da wani dalili, kinga ina zuwa” ta wuce ta bar Nana a gurin, tana dubawa taga babu Jalal a gurin, hankalinta ne ya tashi, se abokansa dasuketa rawa a gurin, dubawa ta shigayi amma bata ganshi ba, da sauri ta fita harabar gurin tana lekawa, hangoshi tayi akan wata mota acikin duhu, suna bashi giya, yana sha yana dariya, gashi Hannah ta manne a jikinshi kaman zata shige jikinsa, da gani yafara fita hayyacinsa, gefe Hannah ta koma tana waya, daga baya kuma ta bar gurin da wayar a hannunta, dan haka Jalila ma da sauri ta dauki wayarta ta kira Jawwad
“Yaya kai sauri, kafito ka dauke Jalal, kaman akwai wani abu da ake shirin yi masa kai sauri dan Allah” tana gama wayar ta nufi gurin motarsu ga tarar da direbansu manu yanata goge2 mota, da sauri tace
“Manu dan Allah temakamin zakayi, zomuje ka gani, ba musu yabita a baya, suka tsaya dan nesa da inda Jalal yake a cikin wannan duhuwar, ta kalli manu tace” zan dauke hankalin wancan, dan Allah ka dauke ABDUL JALAL, ka kaishi gida”
“Amma me…….
” Manu kawi ka tafi da shi dan Allah, zan dauke hankalin wancan matashn, daka daukeshi ka tafi dashi, inkunfita waje ka kirani a waya, tana gama fadin haka ta nufi inda Jalal yake, matashin dayake gefensa yanakuma dura masa giya taje ta kalleshi
“sannu dai yaya na”
“Yawwa yan mata ya akayine?”
“Temakamun nakeso kayi”
“Akan me fa?” kaga kudin motana na yar, dan Allah kozaka rage min hanya kokasa wani a abokanka ya ragemin hanya”
“haba yan mata kamanki ace an rasa me kaiki gida hakan be dace ba, bakece budurwar Jalal ba”
“A a niba budurwars bace brother na ne, dan Allah yi sauri dare yanayi” matashin ya kalli Jalal yace “Man kajirani anan karkaje ko ina, ina zuwa yanzun nan” ya kalli Jalila “bari in kira wani a waya, yazo ya kaiki”
“A a kaga muje kawai ka biyamin kudin motar se in tafi”
“A a be kamata ki hau napep ba muje” har sunfara tafiya ya tsaya ya juyo
“to ni mene tukuicina”
“karka damu, se abunda kakeso shi za a baka” ya washe baki “to shikenan muje” shiya shiga gaba tana binsa a baya
Manu yana ganin sunyi gaba yai maza yaje ya rungomo Jalal, gaba daya jikinsa ya saki dan a mugun buge yake, tangadi kawai yakeyi, ga Jalal da nauyi amma haka manu direba ya daukeshi, dan babu abunda Jalila zata sashi yakasa yimata, saboda mutuncin datake masa, ya kinkimi Jalal yasashi a mota ya kunnata ya bar gurin.
Jalila kam suna shiga hall din, taga matashin ya doshi wani gungun yan shaye2 ta shige cikin mutane, Jawwad ya kirata amma bata dauka ba, ta koma gefe ta kirashi
“Baby kina ina, naduba ban gankiba, kuma banga Jalal dinba”
“Yaya Jawwad ka fito kaida Nana mu tafi mu hadu a can waje, kuyi sauri” ta kashe wayar ta fita, tasamu wani guri ta tsaya can nesa da hall din, tana nan tsaye ta hango wata arniyar bakar jeep ta shiga harabar gurin, ba a fito daga motar ba, kuma ba a bude ba taga Jeje, ya fito yazo gaban motar ya tsaya, aka sauke glass din motar, wanda ta ganine ya sata zare ido, baban faruk ne da yadinga cin mutuncin Jalal ranar, saboda ya gaisa da dansa meye hadinsa da Jeje? Bata gama tunanin ba taga motar tajuya ta mike titi, shikuma jeje yabar gurin, Jawwad yazo yai parking a gabanta ta shiga da sauri, tana cewa “yaya yi sauri mubar gurin nan” da sauri yaja motar suka bar gurin
Jawwad yace “Baby nifa ban ganeba wai meye haka kikeyi ne? Nifa dole in koma gurin nan saboda Jalal, Jalila tace
” Jalal yana gida ai, manu direba ya tafi kaishi gida”
“meyasame shi? Ya akai ni ban saniba, tukuna ma naji kince wai wani abu ze sameshi”
“da wasa nake dama sonake kazo mutafi” dagajin abunda ta fada kasan karyane, amma yai shiru ya kyaleta. Suna zuwa gida Jawwad yai parking din motarsa, ya tafi gidansu Jalal.
Su Jalila na shiga cikin gida suka tarar su Maama ma sun kwanta, Jalila batace ma Nana komai ba itama bata cemata ba, Jalila ta shiga tai wanka, tai kwanciyarta jinta take sakayau hankali kwance, amma idan ta tuno fuskar baban faruk data gani tareda Jeje, se abun ya bata mamaki matuka,
Jawwad na zuwa ya tarar da Jalal a kwance kaman matacce, an kwantar dashi akan gadonsa, girgiza kai Jawwad yai ya fito ya koma gida, yana son yayiwa Jalila tambayoyi amma by now yasan ta kwanta bacci.
Tashin hankli, tas mutumin ya dauke Jeje da mari, “baka da hankali ne, har gurin nan naje ka tabattarmin da komai ze tafi dai2, mahaukacin inane kai, kaikamin alkawarin zaka tabattar da cikar burina amma meyasa haka, na kashe kudi akan wannan shirin, an tanadi komai, a daren yau naso akaishi gurin nan da kwayoyi suke, a ajiye mugayen makamai da yan mata, muyi ikrarin yana musu fyade, sannan mu shuno hukumaa suzo su kamashi, a wulakanta shi a gaban uwarsa ta zubda hawaye fiye da yadda tasani nasa tawa uwar, kuma saboda hauka kabari damar nan ta kauce mana, in baka saniba har cin hanci na bayar cewar in ankama Jalal asashi a cikin ya’n fashi yadda, ko ubansa zeyi amfani da dukiya gurin kubutar dashi, se sun wulakanta se fiye da rabin dukiyarsa ta girgiza, sannan saboda jakanci kabari ya gudu”
“Wallahi oga KB na tsara komai, yaran naka ne basuzo da wuriba, muka nemeshi muka rasa, kuma har gadinsa nasa ayi aka bashi giya da kwayoyi a ciki wata hatsabibiyar yarinya ce ta hana shi cin cake din nan, muka samasa kwaya, amma muka neme shi muka rasa”
“hatsabibiyar yarinya ta hanashi cin cake” oga KB ya maimaita, “wacece ita yar uban waye ita da bakuyi maganinta ba” “Wallahi oga ban santa ba nima a gurin nafara ganinta” “tasan sirrinmune?”
“a a ba wanda yasani ko Hannah da take mana aiki bata sani ba”
” ina bukatar ganin hotonta sannan ka ganomin yar uban waye, tashi ka bani guri maza2 tashi ka tafi bana son sake ganinka a gabana, kuma kaima zakaga abunda zanmaka, zan nuna maka sakamakon gaza cikamin alkawarina, tashi kabani guri”
Jiki a sanyaye Jeje ya tashi ya bar gurin, abun duniya ya isheshi, bacci sam ya gagari Jeje, se tunani yake, yarasa menen mafita.
Maganganun da Jalila tayi dazune suka dawowa Jeje, anya ba ita ta dauke shiba, kodai tasan sirrinmune, hakane ma to amma waya gayamata? to amma taya karamar yarinya kamar wannan zata iya dauke Jalal, shikam tiger wani irin banza ne haka, har yabari Jalal ya gudu, to amma mutumin dayake a buge taya yaya ze iya guduwa, to waima wacece wannan yarinyar? Anya bada tiger aka hada bakiba Jalal ya gudu?.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button