Uncategorized

ABDUL JALAL PART 1 HAUSA NOVEL

Ilham tarasa abinda yake mata dadi yan kwanakin nan takasa gane inda Jalila tasa gaba shin da gaske Jalila tana son Jalal, kokuwa, amma in tana sonshi ya za ayi tagaya masa wannaan miyagun maganganun,
Amma kuma ya akayi Jalila take gaya masa maganganu son ranta amma be dau wani mataki akanta ba, Wanda ta tabbatar ita bata Isa tayi masa haka ba,
Kenan shima yana son Jalila, tunda take gaya masa maganar data ga dama amma ya kyaleta
“Kan uba karyane wallahi ina wani shirmen hakan ze faru”
Tai maganar a fili
“Ko mami zan kira in gaya mata abinda yake faruwa, yanzu ina gaya mata ni zatayiwa fada tace laifinane, kuma baze yiwu in gayawa Nana ba tunda Yar uwattace za a iya hada kai da ita a cuceni, yanzuma watakila bakinsu daya”
Tayi nannauyar ajiyar zuciya to ni yazanyine?
Ko gidan malamin nan zanje da kaina innemi yaseera ta rakani(kawar Ilham ce) hakama za ayi inje inji ya za ayi aimin maganin wannan tantiriyar
Da wannan shawarar da zuciyarta ta bata ta samu nutsuwa

Halima ta kalli Jalila
“Jalila inani inasaka wannan kayan masu tsada”
“Leemart to meye a ciki, ba wani kaya masu tsada, sedai in abun hannuna ne bazaki karba ba”
“A a Jalila ba haka bane,”
“To in ba hakabane kawai ki karba”
“Nagode Jalila, Allah ya faranta miki kaman yadda kikayimin”
“Ameen leemart”
Jalila ta koma daki ta kira Ummi a waya tagaya mata abinda tasamu a result dinta Ummi tayi murna sosai, sannan tace
“Jalila ya yanayin zamanki a kano? Naji muryarki cikin farin ciki ina fatan komai lafiya?”
“Komaiafiya Ummi, bakiga Mayan da Abba ya siyo mana ba,”
“Masha Allah, haka nakeson ji, yacigaba da hakuri da rayuwa Jalila,”
“To Ummi insha Allah, Ummi da weekends insha Allah Hanan zasu kawomin ziyara”
“Dagaske baby”
“Dagaske Ummi, dazu Yaya Abdallah ya gayamin”
“Allah sarki gaskiya suna kaunarki Jalila, Nima next week insha Allah zanzo, daga nan zan wuce garinmu”
Haka nan se Jalila tayi jikinta yaysanyi
“Ummi tafiyar tana nan Ashe zakiyi,?
“eh tana nan zanyi insha Allah”
“To Allah ya kaimu, next week din”
“Ameen ki gaida mutan gidan”
“Zasuji insha Allah”
Nana ta Dan kalli Jalila
“Yanaga jikinki yayi sanyi”
“Nana banason tafiyar nan da Ummi zatayi”
“Haba Jalila, Ummi yakamata tayi tafiyar nan yana da kyau taje taga danginta”
“Hakane Nana”
“Yawwa to kidena tayarda hankalinki, kiyimata addu a kawai”
“To Nana”
“Yawwa babyn Ummi”
Daren ranar Ilham batayi baccin kirkiba se tufka da warwara kawai tekeyi, kamar ta janyo safiya tayi domin taje gurin malamin nan
Washe gari da safe wajen karfe goma Ilham ta shirya tacewa mummy zataje gidansu
Ummi tace seta dawo, tana fita ta tafi gidan su yaseera, suka gaisa da Maman yaseera sannan ta wuce dakin yaseera, ta tarar yaseera ta shirya ita take jira ko zama Ilham batayiba suka fita ita da yaseera sukayi gidan malamin nan

Share please
More comments more typing…………………………..

????️????️????️????️????️
[8/31, 8:30 AM] Safiyya: ????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????

_ABDUL  JALAL_
       (2020)

  _ STORY & WRITTEN BY AISHAHUMAIRA_
(Daddy's girl)

           PAGE- 36

PART 1
Share please

_Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam)
Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa’azantarwa, ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa.
Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi

Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode.

Domin Samun karanta wannan littafin yi magana ta what’s app akan wannan lambar

07063065680
Kokuma addanna wannan link din domin samun novel din

????https://chat.whatsapp.com/EtB4KI52K0v5FQc2ELhidL

Special thanks to my group members ina Alfahari daku comments dinku na bani karfin gwiwa
ABDUL JALAL NOVEL FANS
Love u all guys ❤❤❤❤❤

      -MY FIRST NOVEL-

Ilham ce da yaseera gurfane a gaban malamin nan, malamin ya kalli ilham sannan yace
“Ya kikazo keka dai yau ina babartaki?” Ilham ta Dan gyara zama
“Malam akwai matsalane fa”
“Matsalar me?”
“Malam, nifa na fara gajiya da wannan wahalar danakeyi akan Jalal, ina ta nawa kokari amma, wata Matsala na kokarin kunno kai, duk wannan wahalar danake yana kokarin fara soyayya da wata yarinya daban, hankalina duk a tashe yake”
Malamin ya numfasa ya kalli Ilham sannan yace
“Anya kuwa dagaske kike yafara soyayya, a aikin damukayi akansa bana tunanin ze iya fara soyayya cikin sauki, har se burinku yacika,”
“Malam nifa tsoro nake, kar inje shirin ya rushe gaba daya”
“Hakane in dai ba wancan sharadin ne ya afkuba, to aikin damukayi masa yana tareda shi har yanzu, koda kuwa yayi soyayya da wata, sedai in wancan sharadi ya karya”
“Wallahi ji nake kamar kawai in aiwatar da me gaba dayan tunda har yanzu yaki yadda ya soni, balle ya aureni”
“Wannan kuma ya rage naki sekije kicigaba da kokari, ko be sokiba daya aureki shikenan aiki ze kammala”
Yaseera ta kalli malamin
“To yanzu malam babu yadda za ayi da wannan shedaniyar yarinyar, tunda akwai yiwuwar ya iya fara soyayya”
“Wannan kuma Ku zakuyi wannan aikin ni nayi muku kokarin da yakamata sekije ki bada himma, zanyi bincike akanta, muga abinda za ayi akanta”
“To shikenan malam zanje in cigaba da kokarin”
“Yayi kyau, abinda ake ciki zan sanarda ke”
Suka mike suka fito yaseera ta kalli Ilham
“Wai Ni kuwa Ilham wace wannan yarinyar”
“Hmm wallahi kanwar abokinsa ce wata Mara mutunci da ita, yaseera yarinyar nan bata da mutunci Sam, idan banyi wasa ba fa zata bata min aiki, kinga rashin mutuncin da take masa amma ko kallonta ba yayi balle ya dau mataki, kuma da nice na gayamasa abinda take masa da tuni ya hukuntani”
“Kince sonshi take, kuma kince tana masa rashin mutunci, anya kuwa son nashi takeyi”
“Nima abinda nake ta tantama kenan, amma nafi tunanin borin kunya suke a gabana amma sonshi take, kinga a yadda nagansu kuwa ranar a gidansu, wallahi bantaba tunanin haka kishi yake ba se ranar”
“Wai ma inane gidansu”?
“A gidansu Nana take fa cousin dinsu ce”
“Muje gidan inga wace ce, inga iya rashin mutuncin nata se mu San ta inda zamu bullo mata”
“To shikenan mu karasa, ki ganta,”
Hannah ce kwance akan gadonta tana zancen zuci, “mace kamarni ace Jalal yake wulakantawa, ga yadda maza kemin layi amma akan wannan Dan tahalikin, nake wahala har wani cewa yake ko ze aure baze aureniba, na tabbatar ranar Dana kirashi wannan kanwar tasa ce ta daga har take zagina, zanyiwa Jeje aikinsa sannan itama kanwartasa senayi maganinta, nita zaga saboda tana son Jalal, zata ga tsiya, indai Hannah ce ta taro daidanta”

Nana ta fito ta tarar da Jalila a kwance akan kujera tana danna waya
“Jalila zan Dan fita, zanje bayan layi ne Maama ta aikeni”
“To sekin dawo”
Fitar Nana ba dadewa aka turo kofar palourn ba ko sallama, mutane taji tsaye akanta
“Dan Allah ina Nana”?
Shiru tayi ba tako daga kai ba, balle ta ga suwaye
” magana fa nake miki”
Ba ta dago kanta ba tabada amsa
“Taje akoya mata sallama, inzaka shiga guri”
Yaseera ta kalli Ilham, sannan tace
“Yi hakuri Dan Allah, salam alaikum”
“Wa alaikum salam warahmatullah”
Jalila ta amsa sannan ta tashi zaune
Ta dubesu ta danyi murmushi
“Sannunku da zuwa bismillah ga guri Ku zauna”
Ilham se wanj hura hanci take
Jalila ta Dan kalli Ilham sannan ta maida idonta kan yaseera
“Nana ta Dan fitane ba nisa tayiba yanzu zata dawo insha Allah”
Yaseera ta danyi murmushi,
“To mungode”
Suka samu guri suka zauna
Jalila tace
“Ilham ya kike,? Ya Gida”
Ilham tai mata wani irin kallon up and down
“Da nazo nayi miki maganane? Kokuma ke a dole sekinshiga harkata”
“Ko in shiga harkarki ko kar inshiga harkarki babu abinda zaki kareni dashi ko ki rageni dashi, tunda ba abunda nake nema a gurinki nayi hakanne kawai Dan sauke hakkin addinina, ke Yar uwatace musulma, kuma makociya, muna da hakki akan juna shinake kokarin saukewa kawai, bawai wani abuba”
Tabdijan yaseera a zuciyata tace “lallai wannan yarinyar yar duniya ce tana da baki, gashi komai nata abin birgewa yanayin yadda take magana kawai ya isa ya dau hankalin mutum, ga iyayi kuma dajin maganarta kaga shgwababbiya gashi ta iya juya ido in tana magana” yaseera kallon Jalila kawai take
“Bakuwa bari in kawo miki abin tabawa kafin Nanan ta dawo, naga Ilham se wani cika take tana batsewa bansan menayi mataba”
Jalila ta mike tana tafiya a gayance ta nufi fridge
Lallai dole Jalila ta tafi da imanin duk Wanda yai tarayya da ita dukda Ilham tace mata bata da mutunci amma tana ganin hakan duk cikin iya takunta ne
Lemo Jalila ta kawo musu da ruwa sannan ta kira Nana a waya, ta gayamata tayi baki, Nana tace mata takusa karasowa tana daf da Gida
Yaseera ta kalli Jalila
“Nagode Yar uwa”
“Bakomai yiwa Kaine bakin Nana ai baki nane”
Ilham bata kuma cewa komaiba, tunda Jalila takuma gaya mata magana, sema haushin yaseera daya kamata ganin yadda ta zage suna hira da Jalila kamar sun saba
Ana haka Nana ta dawo,
“Yawwa ga Nana nan ta dawo”
Nana ta kalli inda su Ilham ke zaune
“Yaseera dama talaka na ganinki gaskiya akwaiki da zumunci”
“Yanzunma unguwa mukaje nacewa Ilham mu biyo mu gaisa kwana biyu bamu haduba”
Nana tace “hmm kin kyauta ya Gida ya kwana biyu?”
“Lafiya kalau”
Jawwad ne yayi sallama a palourn suka gaisa dasu Ilham
Sannan ya kalli Jalila
“Baby yunwa fa mukeji kuma munji ki shiru, Jalal ze sha magani beci abinci ba”
Kallon Jawwad tayi ta danyi murmushi
“Aini yau banyi girkiba, in kuma kunajin yunwa to kuzo kuyimin wanke² wani yayi gyaran kayan miya” murmushi Jawwad yayi ya nufi hanyar kitchen Jalila ta mike tabi bayansa, Ilhaam kam Dan bude baki tayi
“Hmm Yaya Jawwad manyan”
Nana ta fada tana Dan murmushi
Ita dai yaseera ta jinjina yadda Jalila take gudanar da
al amuranta cikin nutsuwa, lallai indai da Jalila, Jalal yake
Shirin fara soyayya to se Ilham tayi dagaske, don Jalila bazata sha wahala gurin sace zuciyar duk Wanda taso ba
Jawwad ne yake bubbude kwanuka a kitchen
“What are you looking for?”
Yaji muryar Jalila a bayansa, juyowa yayi ya kalleta
“yunwa fa mukeji baby” yai maganar yana kwaikwayon JALILA
“Yi shiru karkayi kuka jeka zan kawo”
“Inyi kuka sekace wani baby, Babyce me kukan allura, kuma nasan in tanajin yunwa ma setayi kuka”
Dariya sukayi gaba daya
Wanda hakan yayi dai² da fitowar Maama tana kallonsu ta window kitchen, kwafa maama tayi ta nufi parlour
Su yaseerana suka gaida maama ta amsa musu sannan tace ma Nana taje tacewa Halima tana kiranta, tajuta ta koma dakinta
Su yaseera suka mike sukace zasu tafi, dama ba ziyarar Allah da annabine ya kawosu ba Dan ILHAM ta nunawa yaseera Jalilane, suna shirin tafiya
Jalila suka fito ita da Jawwad, suna dariya, Ilham ta kallesu taja uban tsaki
Jalila ta kallesu “har zaki tafi, yaseera, mungode ki gaida Gida, Ilham ki gaida mummy”
Ilham bata kula Jalila ba itama Jalila bata damuba Dan tasan ILHAM ba amsawa zatayiba, tai waje da kayan abincinsu Jawwad
Nana ta kalli Ilham
“Haba Ilham, Jalila tana miki magana amma kin wani shareta”
“Kinsan bana son rainin hankali, kuma kinsan halintane dan haka ni bana shiga sabgar mutum inaga hankali be isheshiba”
“Kut lallai Ilham amma kinsan da a gabantane dase ta gaya miki wadda tafi takin zafi”
“To yanzu tunda bata nan seki rama mata”
Ilham ta fada tana Harar Nana
“Rufamin asiri, ina ni ina iya shigarwa Jalila fada ai sedai inyi kallo”
“Ya fiye miki”
Haka Nana tarakasu ILHAM had bakin gate suna tafe suna fada,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button