Uncategorized

ABDUL JALAL PART 1 HAUSA NOVEL

Alhamdilillah Jalila ita tazo na biyu a gasar musabaka da akayi tasamu kyautuka da dama kuma an karrama malamanta
Ita Jalila duk ba haka taso ba na daya taso tazo
“Duk wannan sakaran ne yajamin haka kawai naita mafarkinsa nazo musabaka ya hanani sukuni”
Haka taita mita suka kamo hanyar dawowa Kaduna suna murna amma ita haushi duk ya isheta
Har Gida motar makaranta takai Jalila, siyama tana gidan tana Jiran isowar Jalila
Ummi tana ganinta ta rungumeta tana murna, amma Jalila tai kicin² da fuska
“Lafiya kuwa babyna?”
“Ummi ta biyu fa Nazo”
Tafada kaman zatayi kuka

“Haba baby Wanda yazo na karshe kuma yace me? Daga na daya fa seke haba babyna”
“Gaskiya aminiya inkakiyi haka baki kyauta ba kullum zakiyita zuwa na dayan, hakan ma mu munyi murna”
“Yawwa ai gara kigayamata siyama, adinga godewa Allah Baby”
Ummi tayi maganar tana dungurewa Jalila kai Dan turo Baki JALILA tayi
Taje tayi wanka suka kule dakii itada siyama suna hira
“Kinsam wani Abu aminiya”
JALILA tai maganar tana kallon Siyama
“A’a sekin fada”
Siyama ta bata amsa
“Wallahi Jiya agurin musabaka naji gabana yanata faduwa ina tuna mafarkin nan danake”
“Kai Aminiya meye kuma na tunawa ABU ya Riga ya wuce kimanta kawai
Bari inbarki ki huta kishirya ranar Monday insha Allah za a koma school”
“Can ta matsemusu bazan komaba senagama hutawa ki gaida umma”
“Aminiya halinki seke tararki za aci fa in baki koma ran Monday ba”
“Hhh tab Tara sedai a ci wasu Tara ba dai niba”
Sukai sallama ta Raka Siyama kofar Gida ta dawo dakinta ta kwanta akan katifa domin huce gajiya

Mummy ce ta dawo Ilham tagaya mata ai Jalal ba lafiya suka tafi part dinsa, yana kwance akan gadonsa yana bacci jijiyoyin kansa duk sun daga dagani baccin ba dadi yakemasa ba, warin turaren Ilham yakuma shaka dukda bacci yake seda ya yamutsa fuska ya juya wani bangaren
A hankali mummy ta kai hannu ta shafa sumarsa tana fadi
“Allah yabaka lafiya son”
ILHAM ta amsa mata da “Ameen”
Se bayan azahar ya farka Jawwad ya shiga cikin gida yace Ilham ta hado tea ta kawowa Jalal,

Jawwad ne gefen Jalal yana masa sannu
“Ya kakejin jikin naka yanzu”?Jawwad ya tambayi Jalal
“nifa har yanzu yanamin ciwo, amma bakaman dazu ba”
“To ai kaima ance muje asibiti kaki ka manne a Gida”
“Ni ba wani asibiti da zanje”
Sakone ya shigo Wayar Jalal, Jawwad ya miko masa wayar

     "Barka da wannan lokaci 
       Lovely am missing ur 
       Handsome face wish to
       See u soon 
       Love u so much
       From ur lovely bae"

“Mtseww wannan wace irin jaraba ce”
Yana aje wayar tafara ringing an kira yafi sau uku yaki dagawa
“Jalal wayarkace fa ke ringing
Ka daga mana”
“Bazan daga ba in ka gaji da karar kai ka daga”
Girgiza kai Jawwad yayi halin JALAL se hakuri
Hannu yasa ya daga wayar se yaga unknown number muryar mace yaji
“Hello babyna fatan kana lafiya”
“Sorry ba me wayar bane, me wayar baya jin dadi amma wa za ace masa”
“Eyyah shiyasa naji ni bani da lafiya nima ko abokinsa ne JAWWAD”
“Dan uwansa dai”
“To amin afuwa Dan uwansa”
“Eh nine”
“Hannah ce ai masa sannu, ko zaka bani address din inzo in dubashi”
“Ohh no daga nan ma kiyi masa addu’a mungode”
“Anyway Allah yabashi lafiya amma banajin zan iya komai bayan mallakin zuciyata ba lafiya,
Ka gaisheshi please”
“Zeji insha Allah”
Jawwad ya katse kiran ya kalli Jalal
“Mutumin yaushe kafara soyayya ba labari wace kuma Hannah”
“Mtsewww soyayyar banza kai kasanta”
“Easy mutumina adena cika baki wadda takiraka din nan bakaji kalaman data fada tace agaya maka ba”
“Dan Allah ka kyaleni inji da kaina”
“Ohh sorry nadena sannu,
Yanzu za a kawo maka tea”

ILHAM kam wani tunani tayi this is another opportunity for her to use that medicine again
Tunda wancan lokacin be Ciba a abinci yanzu tasan zesha a tea
da rawar jiki Ilham ta mike taje ta nufi kitchen ta hada tea ta zuba wani maganin a ciki ta juye tea din a flask ta doro cups akan plate ta nufi sashin Jalal

A cikin bacci Jalila taji kirjinta ya tsanan ta bugawa Ilham kawai take gani a mafarkinta a hankali ta bude ido gabanta ne yacigaba da faduwa meke Ilham ke shirin yine nake ganinta a bacci na
“Laila ha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin”
Shine abinda Jalila taita maimaitawa kamar wadda aka tsikara tayi zumbur ta mike zaune ta dakko wayarta

Sallama Ilham tayi tana kokarin shigowa
Jalal ne ya Daka mata tsawa
“Tsaya a nan malama karki karaso inda nake”
“Haba Jalal wai meyasa kai ba a maka gwaninta ne”
Saroro Ilham ta tsaya tana kallonsu
“Eh naji ba amin gwaninta amma karta shigomin nan”
Mikewa Jawwad yayi ya karbo tray din hannunta
“Kiyi hakuri ILHAM kinji zedena ne nasan ba kyajin dadin abunda yake miki, nan gaba in ance yayi koda kudi baze miki ba”
Gyada masa kai kawai Ilham tayi tabashi tray din kayan tea ta koma
Gaban Jalal ya dawo ya zauna
“Bross Ilham kanwarka ce yadda kake treating dinta Sam be dace ba”
“To mekakeso in mata indinga goyata ko kuma in zauna ina mata dariya a hakanma kana ganin rashin kunyar da takemin har ta kalleni tace ni take so sa’anta ne ni?”
“Jalal Ilham itama yarinya ce, kuma so ba karya ne ba bazaka gane hakan ba se ranar da yai maka kamun kazar kuku”
“Naji labarin ya isheni haka, hadamin tea in sha”
Jawwad na cikin hada masa tea dinne Jalila takira wayar Jawwad
Murmushi yayi sannan ya daga wayar
“Sisyna am sorry nayi laifi ban kiraki naji yakike ba yau hankalina ne ba a kwance baya musabakar?”
Seda ta tura baki kaman tana gabansa
“Yaya Jawwad ta biyu fa nazo”
“Kai amma nayi murna, dole inzo Kaduna muyi celebrating”
“Wani celebrating bafa ta daya Nazo ba wai ta biyu”
“To ai kinyi kokari baby meye kuma na bata rai? Aini a hakan ma kinfiyemin Wanda yazo na daya”
“Dan Allah ka aje wayar nan, ko kabani tea din in hada da kaina”
Jalal yai maganar a fusace

“Ohhh sorry bari in hada maka”
Jawwad yai maganar yana kashewa Jalal ido
“Yayana kaida waye ne?”
Jalila ta tambaya
“Nida yayanki ne bashi da lafiya tun jiya yake fama da ciwon kai an masa allurai amma har yanzu kan bedena ciwo ba, shine zan hada masa tea yakemin masifa”
Dan tabe baki Jalila tayi

“Dama yana salla ne se ince ko beyi Azkar ba, to Wanda be salla ba ya za a tambayeshi yayi Azkar ma, kasan in mutum ya nisanta kanshi da Allah komai ma seya sameshi”
Dan kallon Jalal Jawwad yayi yaga idonsa a lumshe se yayi tunanin ko bayajin me Jalila take fada, amma tsaf yaji me tace
“Hmm Adduar ki kawai muke bukata baby”
“To Allah ya shirya ya bashi lafiya, ka kama kansa ka karanta mai bismillah kafa sha Tara se ka biya masa ma tayassara minal Qur’an”

“Godiya muke ya sayyada, Allah yakara hasken makaranta
Brother tashi ka karbi tea din”
Yafada yana Dan jijjiga Jalal
Tashi zaune Jalal yayi ya karbi tea din ya kai bakinsa ya Dan fara sha
“What!! tea naji kace”
“Eh tea zan bashi ya sha kinga yana da dumi”
“Waye ya hada tea din?”
“Ilham ce ta hada masa mana”
Jawwad yabata amsa

Dan tunani Jalila tayi
Meye yasa ta dinga faduwar gaba tun agurin musabaka har yanzu bashi taita ganin Ilham da sauri tace

“What Ilaham kuma? Karya sha tea din nan Yaya Jawwad ka karbe tea din nan”
Tafada cikin karaji

Share please
More comments more typing……

Comments dinku yayi kasa zanyi yajin typing ????????????

????️????️????️????️????️????️
[8/31, 8:26 AM] Safiyya: ????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????

_ABDUL  JALAL_
       (2020)

  _WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_
(Daddy's girl)

           PAGE-  22&23

PART 1

_Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam)
Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa’azantarwa, ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa.
Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button