Uncategorized

ABDUL JALAL PART 1 HAUSA NOVEL

Karfe takwas na safe Abba da Jawwad suka hadu a palour zasu kuma fita, Maama ta Kalli Abba
“wai Dan Allah yanzu fita zaku kumayi, ko karya bakuyiba, nasan wallahi wani gurin tai tafiyarta amma duk ka daga hankalinka”
Abba ya kalleta
“kina tunanin, zata iya tafiya wani gurin batareda sanin yarta ba, bari in tunamiki abunda kika manta, Maryam da Jalila amanar dan uwana Aliyu ce dasu Inna, idan naci wannan amanar Allah baze barniba, dolena innemo abunda yasamu Maryam dan na tabbatar, da taje lafiya, da komai lafiya nasan, komae ake ciki, zata gayamin”
“kai kake ganin hakan amma a gurin su aikata irin wannan ai ba wani abun damuwa bane, ai abun kunyane ta koma garinsu da yarinya bayan basu san tayi aureba, kodayake su ina suka san wata kunya”
“Ya isheki haka Zainab, Wallahi zan bata miki rai fiye da yadda kike tunani, akan cin zarafin matar Dan uwana, babu bawan da ya isa ya kuskurewa kaddararsa,”
Jawwad ganin sa’ insa na neman barkewa tsakanin iyayennasa, se ya kewaye ya tafi dakinsu Nana, ya tarar da Jalila ta dora kanta akan cinyar Nana, tana zubda hawaye, yayinda Nana take bata hakuri, karasowa yayi ya tsuguna
“Baby baki dena kukan bako? Dagowa tayi ta kalleshi, sannan ta sunkuyar da kai, kiyi hakuri yanzuma fita zamu kumayi da Abba Insha Allah zamu gano inda take, ki dena kukan nan kinji, ze iya kawo miki matsala”
Ta dan Jinjina masa kai, ya Kalli Nana yace “Nana dan Allah ki tabbatar taci Abinci”
“to Yaya Insha Allah” daga haka ya mike yafita cike da tausayin Jalila,
Yana fitowa palour yaga ba kowa dan haka ya fita harabar gidan ya tarar da Abba a zaune a cikin motar yana Jiransa, Jawwad ya shiga motar ya kunna suka fita,
Har la’asar babu wani kyakykyawan labari, dasu Jawwad suka samu game da Ummi, kuma har yanzu wayarta bata shiga, haka suka gaji suka dawo gida, koda Jalila taga sun dawo, da sauri ta tashi, ta fita domin sanin me ake ciki, Abba yasa aka kiramasa Jalila, Jalila tazo, ta durkusa a gabansa
Koda taji Abba yafara dayi mata nasiha ta karaya ta kuma fashewa da kuka
“Shikenan na rasa Ummina, Ummi dama haka zakiyimin, kikayimin wayo kika tafi kika barni, yanzu ba Abee ba Ummi”
Jawwad yace “haba Jalila duk bagamuba, kuma Ummi fa bacewa akayi ta mutuba tana nan da ranta, kuma mun bada cigiyarta gurin” ‘yansanda, insha Allah za a sameta, kidena kuka”
Daga Abban har Jawwad din Jinsu kawai take, dan bata san me suke fada ba, hankalinta sam baya kansu, dan wani abune yazo saitin zuciyarta ya tsaya, shibe fitaba, shi be komaba,
har magariba, Jalila kaman wata mara hankali, batun Abinci dama babu shi, dan ko ruwa bata zubawa cikinta ba danba Yadda Nana batayi da itaba amma taki cin komai, banda aikin kuka ba abunda take, ga gefe cikinta da ya kulle saboda rashin Abinci,
Bayan sallar Isha’i kaman me tabun hankali ta mike ta nufi part din Abba, ta tarar dashi da Jawwad da Maama a palourn sa, tsayawa tayi tana tunanin to intaje mezatace masa,
Wayar Abba aka kira, yasa hannu yadaga, yayi sallama sannan yadanyi shiru
“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un ya furta” Jawwad ya kalleshi a kidime “Abba lafiya kuwa?”
“Jawwad, wai Ummin Jalila wai motace ta bigeta kafin sukarasa garinsu, ta sauka yin salla, kuma wanda ya bigetan yasata a mota ya tafi da ita”
Da jin haka Jalila ta kwalla kara, sekuma ta kame a tsaye, gaba daya suka juyo suka kalli inda take tsaye, idonta a kafe a kansu, mikewa Jawwad yayi da sauri ya nufi Inda take amma ko motsawa batayi ba, kuma ko kyafta idon batayiba, Yana tabata ta tafi zata fadi, da sauri Jawwad ya rikota, Abba ya taso da hanzari “lafiya kuwa, meyasameta?”
Idonta a bude kar, amma bata mosti bata numfashi
“Innalillahi wa inna ilaihi raji un Abba Jalila ta mutu”
Maama na jin haka ta taso da sauri
“kamarya ta mutu?”

Share please
More Comments More typing………………………………….

Love u all my fans ina godiya, da adduo’inku, da kaunarku, Allah yabar kauna
????????????❤️❤️❤️❤️
Team Jalila su ummu Hanif kuzo jana’iza ???????????????????????????? queen ta wula

????️????️????️????️????️
[9/13, 10:27 PM] +234 816 830 7871: ????????????????????????????????????????????????????????
????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????

_ABDUL  JALAL_

  _WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_
(Daddy's girl)

           PAGE-  45

PART 1

_Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam)
Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa’azantarwa, ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa.

A har kullum ina jinjina da godiya ga masoya wannan novel nawa, comments dinku da addu oinku ina jin dainsu matuka, ina godiya kwarai dagaske,
Domin sharhi, gyara, kokuma shawara a nemeni ta what’s app akan wannan lambar wayar
07063065680
Ina godiya matuka Allah yabar kauna

   _My first novel_

Abba ne yasa hannu ya janye Jalila daga hannun Jawwad, yana jijjigata amma idonta a kakkafe, hannu Abba yasa ya rufe idon Jalila babu alamar tana numfashi, Jawwad ya kalli Abba
“Abba wai mekake nufine, ba dai ta mutu ba,” shiru Abba yayi bece komai ba, Jawwad yakuma cewa “Abba kayi magana mana,” Nana ce ta shigo palourn Abba, “lafiya kuwa Maama inajin hayaniya tundaga palour” hankalinta ya kai kan Jalila dake kwance a jikin Abba, Jawwad kuma, kaman baya hayyacinsa, da sauri takarasa inda suke “Abba meyafarune”
Maama ta kalleta “Ke meye haka ki nutsu mana, mutuwa tayi” zarewa Maama ido Nana tayi, “wallahi karyane” ta cacimo Jalila daga jikin Abba “Yaya Jawwad dagaske Jalila ta mutu, meyasameta, wallahi bata mutuba Abba kajifa ta janyo hannun Abba ta dora a wuyan Jalila, jiyayi alamun jijiyar gurin tana motsawa a hankali, ya kalli Jawwad sannan yace
” tashi maza ka fito da mota, mu tafi Asibiti, da sauri Jawwad ya fita, mintuna kadan ya dawo, ya dauki Jalila kamar gawa yayi waje da ita, kafar Nana bako takalmi tabi bayan Jawwad da gudu, Halima da ba tasan me akeba ganin an wuce da Jalila rai a hannun Allah yasa ta firgice, ga Abba ya fito da sauri shida Maama, Halima ta nufi Maama tana fadin “Na shiga uku meyasami, Jalila ne, Hajiya dan Allah meyasameta?”
“Ke dallah rabu dani, ina ruwanki dame yasameta zakiyi mata maganine, Abba yace” Halima kwantar da hankalinki, suma tayine batajin dadi, amma asibiti zamuje”
Halima a rikice tace “Allah yabata lafiya, dan Allah ku tafi dani Asibitin”
Abba yace “karki damu Halima, kiyi mata Addu a zataji sauki” daga haka yayi waje, itakuwa Maama tasamu guri tai zamanta a palour,
Asibitin doctor salis suka nufa, ba karamin gudu Jawwad yakeba, se kace ze tashi sama, Jalila na kwance akan cinyar Nana, ga sanyin AC amma tana nan yadda take ba wani canji, ko motsi batayi, suna zuwa Asibiti Jawwad ya fita da sauri ya shiga cikin Asibitin ba a dadeba segashi ya taho da doctor salis, Nurses sun turo gado, Abba na tsaye a jikin motar, Jawwad ya karaso ya bude motar ya dakko Jalila, ba wanda zece ba gawa bace, aka dorata akan gadon aka turata, zuwa cikin Asibitin, su Abba suka bi bayansu, suna zuwa kofar emergency suka tsaya, aka shiga da Jalila, su Abba da Nana suka dinga sintiri a kofar emergency tunda aka shiga da Jalila ba wanda ya fito balle su tambayeshi me ake ciki, Nana se kuka take, Abba ya kalleta “Nana kiyi shiru kinji muyi mata addu a zata samu lafiya Insha Allah” Jawwad kam yarasa meyake masa dadi, sam besan mezeyi yaji dadiba, Maama ce ta kira Jawwad “ya akayine naga har yanzu baku dawoba ta mutune”?
” A a Maama bamu saniba, sun shiga da ita emergency tunda mukaje ba wanda yace mana komai”
Daga haka ta kashe wayarta, Halima se addu oi take, tana yi wa Jalila adduar samun sauki, sun shafe awanni a gurin nan kafin doctor salis ya fito, yana share Gumi gaba daya suka nufi inda yake
Abba cikin zakuwa yace “Ya ake ciki” ya kalli Abba sannan ya kalli Jawwad
Jawwad yace “Dan Allah kayi magana mana”
Doctor salis ya nisa sannan yace
“ku kwantar da hankalinku, Alhamdilillah mun samu nasarar ceto rayuwarta cikin ikon Allah, Blood pressure dinta yayi high fiye da tunani, wanda yasa tasamu stroke, yanzu Alhamdilillah tana iya numfashi, kuma bugun zuciyarta yazama normal, sedai har yanzu bata farfadoba, zamu ajiyeta a ICU tukuna muga abunda hali zeyi,
Dan murmurshi Nana tayi tareda fadin “Alhamdilillah, Allah yabaki lafiya Jalila”
Doctor salis yace “Abba kubiyoni office akwai magunguna dazan rubuta” Abba yace to shikenan muje, suka bi doctor salis office dinsa, akace Nana ta tsaya a waje, Abba da Jawwad suka shiga, doctor salis ya kalli Abba
“Muna bukatar Jini koda leda dayane zuwa gobe insha Allah , zamu kara mata, mun gwada PCV dinta shima yayi kasa, kaman ta dade tana rashin lafiya, ya akai condition dinta ya zama worst haka lokaci daya,? Jawwad ya gaya masa komai, yayi rubuce2 yabasu magungunan da ake bukata su siyo,
Jawwad yace “doctor zamu samu ganinta kuwa”
Doctor salis yadan girgiza kai “No bazaku iya ganinta yauba gaskiya, zaku iya tafiya, in yaso gobe in Allah ya kaimu seku dawo, daga nan a duba Jinin da za asamata,” Abba yace “Kana ganin ba komai in an barta anan”
“Eh Abba ba wani matsala, za a kula da ita Insha Allah, ko wani ya zaunama bata hayyacinta bacci take, ba lallai ta farfado a yauba”
Sukayi sallama da doctor, sukaje suka biya bill dinsu, daga nan suka taho gida, a palour suka tarar da Halima, ta sha kuka, tana ganinsu tafara tambayar Abba, “Ya jikin nata”
“Ki kwantar da hankalinki ta farfado, tana baccine, an kwantar da ita”
“Allah yabata lafiya”
Abba ya amsa da Ameen, dama Nana bata tsaya ba dakinsu ta wuce, jin dakin tayi babu dadi, ta kalli gurin kwanciyar Jalila, da yanzu ta kwanta kokuma tana salla, Hawaye yazubowa Nana, “Allah yabaki lafiya Yar uwa”daga nan taje tayo alwala, tai sallar Isha’i, ko kayan jikinta bata canzaba ta haye kan gado tayi shiru tana tunani, har bacci ya dauketa,
Koda Abba ya shiga part dinsa Maama tayi dai2 akan gado tana baccinta, ko a jikinta, wanda da yartace da bataga tayin bacciba, shigewa yayi yai wanka, yafito ya dakko sallayarsa ya dawo palour dukda ya gaji matuka yau, wuni sukayi yawon neman bayanin inda zasu samu Ummi, ga wannan abu daya samu Jalila,
Bangaren Jawwad ya dakko wayarsa ya kira Jalal amma bata shigaba, dan haka ya tashi yatafi gidansu Jalal, da mamakin Jawwad, Jalala baya nan, yasan baze wuce yana mashaya ba, dan haka ya hakura, ya koma gida ya rama sallolinsa ya kwanta, se dai bacci ya kauracewa idonsa, se tunani

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button