Uncategorized

ABDUL JALAL PART 1 HAUSA NOVEL

Doctor salis ya koma inda aka kwantar da Jalila, ya dan tsura mata ido, ta rame sosai akan lokacin daya fara ganinta, idonta a rufe ga oxygen da aka samata, a hankali numfashinta yake sauka, sedai bugun zuciyarta ne har yanzu be daidaita ba, kallonta ya cigaba dayi, dukda ta rame amma setayi kyau, goshinta kwance da gashi, ga girarta itama a cike take da bakin gashi, doctor salis y shagala sosai da kallonta, tareda tunani2 daban2 akan Jalila, yaji an taba shi waigowa yayi, yaga Abokin aikinsane, wanda zeyi night, suka gaisa
“Salis har yanzu baka tafi ba? ai nazata katafi tun dazu”
“A a doctor ban tafi ba,”
“Dare yayi sosai fa, yakamata ace ka tafi”
“eh anan zan kwana” doctor Khalid ya kalleshi
“naga kai kayi dutyn yamma”
“Eh, ina da patient ta mussaman” Salis ya nunamasa Jalila
Gyada kai doctor Khalid yayi, yai gaba abunsa
Da sassafe Nana ta tashi ta kintsa, Halima ta dama kunun gyada dan Jalila na matukar sonsa, har Abba ya tashi ya shirya Maama bacci takeyi, suka kintsa suka tafi Asibiti, Jawwad ya kira lambar Jalal har ya gaji amma Jalal be daga ba, yaso yaje ya kuma dubawa ko yadawo, amma da wuri suka fito, dan gari da sauran duhu, dan haka be samu damar komawa yaduba ko Jalal ya dawoba,
Suna zuwa asibiti, Jawwad ya nemo doctor salis, doctor salis yace su kara hakuri har yanzu bata farfado ba, amma za a gwada Jinin Abba kona Jawwad wanda yayi zasu dauka, domin sakawa Jalila, aka duba jinin Jalila da nasu, amma babu wanda yazo daya dana Jalila, cikin damuwa Jawwad yace “to yanzu meye abunyi?”
Doctor Salis yace ” A yanzj gaskiya mu a lap dinmu bamu da irin Jinin ta, sedai inmaka kwatancen Asibiti wani abokina kaje can, in akwai kace nina turoka sesu baka,”
Abba yace “to hakan yayi kyau,” doctor salis ya dakko wani takadda yayi rubutu, yabawa Jawwad, Abba yace “

salis, baze yiwu muganta ba ne?”
Doctor yace “Abba ka kara hakuri tana, karkashin kulawa ta mussaman bazaka samu ganinta ba amma insha Allah zuwa anjima in akasamata Jinin zamu fito da ita”
Abba yace “to shikenan, Jawwad muje ka ajiyeni, zan yi wani abunne, kai seka wuce ka karbo jinin, insha Allah anjima kadan zan dawo”
Suka tashi suka fito, Jawwad yace Nana tazo su tafi tare ba yanzu za a fito da Jalila ba,
Maama ta tashi, ta duba bataga Abba ba, taji gidan tsit, ta fito palour taga halima tana aiki, “Ke halima Abban Jawwad ya fitane”
Halima ta dan risina
“Eh hajiya sun fita gaba dayansu, sun tafi asibiti”
Wani dogon tsaki Maama tayi, ta koma dakinta
Halima tabi bayanta da kallon mamaki, tacigaba da aikinta,
Karfe tara Jalal yai parking motarsa a kofar gidansu Jawwad ko daga ina yake oho, da sauri ya nufi part din Jawwad, amma yaje ya tarar Jawwad baya nan, gashi kuma wayarsa ba caji balle ya kirashi, yana fitowa yaga halima tana gyaran harabar gidan
“ina Jawwad ya tafi”? ya tambayeta, cikin isa
“Suna Asibiti an kwantar da Jalila”
Kallonta yayi sannan yace “me yasameta”
“Nima bansaniba amma a asibiti ta kwana”
Daga haka yafita waje ya hau motarsa, ya nufi asibitin, dan yasan asibitin dasu Jawwad ke zuwa, yana zuwa ya tafi office din doctor salis, Jalal yayi sa a, doctor salis yana nan be tafiba,
Ya mika masa hannu suka gaisa, Jalal ya kalli doctor salis
“Wani patient su Jawwad suka kawo?”
“haba kacemin baka saniba? Kanwarku ce fa, wadda Jawwad ya hanani ce Baby”
“me yasameta?”
Jalal ya kuma tambayar sa
Doctor salis ya gyara zama, ya zayyanewa Jalal rashin lafiyar ta ta, Jalal yace “Yanzu ina Jawwad din yake”?
“eh sun tafi neman jinin da za a saka mata, daana Abba dana Jawwad duk beyiba, nima nawa baze mataba dana wa zansaka mata,” Jalal ya kalleshi ya dan tabe baki, sannan yace “Meye blood group dinta? “
“Meyasa kake tambaya”
Hade rai Jalal yayi,
“Meye kuma na tambayata, kaima kasani patient din Jawwad nawane”
Doctor salis yace “Allah yabaka hakuri, O+ ne”
Jalal yace “irin nawane, a dibi nawa akai lap, inba matsala a saka mata” doctor salis yace “to shikenan muje lap din”
Sukaje aka duba, jinin Jalal, irin natane, kuma anyi gwaje2 amma jininsa lafiya kalau,
Kafin a dibi Jinin ya kalli salis yace “Wannan sirrine tsakanina da kai, ko Jawwad bana son yasan nina bada jinin, dukda nayine saboda Allah, kuma saboda Jawwad, amma bana son yasani, kace masa kawai wanine yazo yabada jininsa sadaka”
“To shikenan, bazan gaya masa ba Insha Allah, yanzu ka zauna se su diba”
Jalal ya zauna aka dibi jininsa, suna gamawa ya mike, aikuwa jiri ya debeshi, yakusa faduwa, lap attendants dinne suka rirrike shi, aka maidashi ya zauna wani ya tambayeshi
“Kaci Abinci kuwa?”
Jalal ya girgiza kai, dan rabonsa da Abinci tun jiya da safe, youghurt akasamo aka bashi ya dan yasha, ya dan huta sannan ya mike, shi yanzu so yake ya tafi, bayason Jawwad yazo ya tarar dashi anan, Doctor salis se sannu yake jerawa Jalal, Jalal ya kalleshi “Muje ka kaini inganta”
Doctor salis yace “A a Jalal tana karkashin kulawa ta musamman, baze yuwu ka gantaba”
“kamar yaya, ganinta zanyi nace ba wani abuba” Jalal ya fada a tsawace, ba shiri salis yayi masa Jagora zuwa inda Jalila take,
Jalal ya dan tsorata da ganinta, ta rame sosai, ga oxygen a hancinta, gefe kuma ga drip, a hankali numfashinta yake fita, dan girgiza kai Jalal yayi, yai waje dan ko sallama beyiwa Salis ba yayi waje abunsa, motarsa ya nufa ya hau ya tafi gida,
Jawwad suka dawo Asibiti shida Nana, sun samo Jinin amma doctor yasanar dasu an samu Jinin, wani yabada nasa sadaka, kuma yayi dai2 dana Jalila an samata, Cikin damuwa Nana tace “wai har yanzu bata tashiba?”
Doctor Salis yace, “kiyi hakuri zata tashi ne, ana samata jininne, Insha Allah, zuwa magariba zaku iya ganinta”
Ajiyar zuciya Jawwad yayi yace “to shikenan, magungunan ban samosu duka ba, sedai in nafita inkuma dubawa”
Doctor yace ba matsala, daga nan su Nana suka tafi gida,
Jalal kam kwanciya yayi, ya kama bacci, dan ya gaji matuka, dukda yunwar da yakeji, gajiya ta hanashi neman Abinci, baccinsa yake sosai, Jawwad ya shigo yaje part dinsa ya tarar Jalal na bacci, se yazata ko giyar ya sha, ya nemi guri a dakin Jalal yayi sallar azahar.
Nana koda ta koma gida, batabi takan Maama ba ta shige tayi wanka tai sallar azahar, sannan ta nufi kitchen, ta dakko Abinci, tana zuwa palour ta tarar da Maama zata fita unguwa, Nana ta kalleta “Maama fita zakiyine?”
“Eh zanje kasuwane zan karbo kaya,”
“Adawo lafiya”
Daga nan Maama bata kuma cewa komai ba balle ta tambayi yame jiki, ita kanta Nana abun setaji ba dadi, taga Sam Maama bata kyauta ba, haka ta wuce ta zauna ta fara cin Abincinta a palour, Halima ta fito daga dakinta tace “Nana ya jikin Jalila kuwa” Nana tace mata da sauki, daga nan tacigaba da abunda take.
Jawwad yana nan yana zaune, har Jalal ya tashi daga bacci, becemasa komaiba shima be kulashiba, ya shiga toilet yai wanka, sannan ya zo ya zauna ya kalli Jawwad
“ya akayine ina ka tafi, da sassafe?”
Jawwad yace “kai zan tambaya ina ka tafi, tun jiya ban ganka ba, wayarka kuma bata shiga”
Jalal ya gyara zama “mmmm to na danje wani gurine,?”
“wani gurine? , bashi da suna”
“Eh bashi da shi” Jalal ya bashi amsa,
Jawwad yace “Shikenan”
Jalal yace “Kai yunwa nakeji, zomuje inci Abinci, ban karyaba, ga rana tayi banci abincin rana ba, nasan gidanku an gama Abinci”
Jawwad ya kelleshi
“Can inda kaje basu baka abincin ba”?
“Eh basu banba, dan Allah ka tashi inajin yunwa sosai fa”
“Me dafawar an kwantar da ita a asibiti”
“Wa kenan?” Jalal ya tambayeshi kaman besan meyafaruba
“Baby mana an kwantar da ita a asibiti, a can ta kwana”
“Allah ya sawwake, ya labarin Ummi fa?”
Jawwad yai ajiyar zuciya, “shine dalilin dayasa ta kwanta a asibiti, Abba aka kira, aka gaya masa wanine ya bige Ummi, kuna ya dauketa ya tafi da ita, tunda taji haka ta fadi, mu mundauka ma ta mutu a jiyan nan”
Jalal ya gyara zama, ya dakko sigarinsa ya kunna, ya busa hayakin sannan yace “waye ya kira Abban yagaya masa?”
“nima bansaniba ina tunanin, ko daga tashane da yabada lambarsa yace in ansamu bayani a kirashi”
Jalal yace “Hmmm” yacigaba da shan sigarinsa, Jawwad ya kalleshi
“anjima kadan zan koma semuje tare ka ganta,”
“inga wa?”
“ka duba Jalila mana,”
“da kyar ne inje, ai nace Allah ya sawwake”
“haka zakace?” Jawwad ya tambayeshi
“yeah” yafada tareda busa hayakinsa sama Jawwad yaji haushi, dan Jalal ko a jikinsa, ya mike ya fice ya barwa Jalal dakin, yana fita Jalal yai murmushi
Jawwad kenan dan uwana na kaina, wani lokacin akwaika da rashin hakuri
Jawwad yakoma gida, yasamu abinci yaci, ya tambayi Nana wai ina Maama, ta gaya masa ai ta fita kasuwa, abun yabatawa Jawwad rai amma yai shiru bece komai ba.
Seda akayi sallar magariba sannan Maama ta dawo, lokacin Abba ma yadawo, yakuma bibiyar report din daya kai gurin yansanda, ko ansamu wani labari akan wanda ya bige Ummi, amma wunin ranar yagama yawonsa ba wani labari,
Maama salla tayi kawai, taje ta dauki Abincin Abba ta kaimasa part dinsa, taje ta ajiye masa, amma bece mata komai ba ta kalleshi
“Abban Jawwad ka dawo bana nan ko? Wallahi fita ce ta kamani”
A fusace Abba ya dago “dole fita ta kamaki Zainab, tunda ba yarki ce a kwance a Asibiti ba, yarinyar nan tun jiya an kwantar da ita a Asibiti, babu tabbacin zata farka daga suman da tayi, amma koda wasa baki taka kafa inda take ba, ina sane da duk abunda kikeyi, ni bazanci amana ba, dan uwana ya nunamin soyayya, bazan iya wulakanta masa yaba, amma kema kin haifa, Wallhi zainab akan Jalila zan iya rabuwa da kowaye, bakeba har yayan cikina, ita nake kallo inji dadi, Aliyu baya raye amma har yanzu Alkhairinsa muke mora, kije kiyi harkarki inyi tawa, ko kije ko karkije dubata hakan baze sauya komai ba, ki dauke Abincin ki, ki fita karki kara zuwa inda nake!!! “
Jawwad yai sallar isha i ya koma Asibiti yasamu, doctor salis yana tambayarsa ya jikin Jalila, ya gayamasa sunfito da ita, an bata daki, daga yanzu zuwa kowani lokaci zata iya farfadowa, amma a tanadi Abinci, dan in tafarka a samu a bata, daga nana yagayawa Jawwad lambar dakin da aka kai Jalila, yana zuwa dakin da mamakinsa yaga Jalal a zaune, a can gefe yana shan sigarinsa, gefe kuma ga Jalila a kan gado ana samata ruwa, tana kwance.
Jalal ya kalleshi yai murmushi
“Sarkin fushi, ya akai na rigaka, zuwa”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button