Uncategorized

ABDUL JALAL PART 1 HAUSA NOVEL

Maama kuma tunda ta fita zuciyarta ke tafasa kan wannan kusanci da shakuwa dake tsakanin Jawwad da Jalila, saboda gani take abun nasu na shirin komawa soyayya, idan kuwa tana Raye bazata taba bari hakan tafaru ba, dama gidan wata abokiyar kasuwancinta zataje dan haka tana zuwa a gurguje tai abunda zatayi ta fito ta tafi gidan yayarta mairo
Tana zuwa kuwa tayi Sa a tana Gida dan gantalalliya ce ta innaniha dillaliyace yau tana nan anjima tana can
Ga ta da ‘yan mata manya irinsu Sa ada da Naja da sauran mannensu amma har shabiyun rana ko wanke² ba suyiba
Daki suka shige da Maama da Yaya mairo, suka gaisa sannan
Yaya mairo ta kalleta “lafiya dai Zainab naganki haka?”
“Inafa lafiya game da wannan yarinyar ne”
“Wace yarinyar?”
“Jalila mana”
Yaya mairo tayi mutmushi
“Kice Jalila ta gurin arniya, ai jiya Naja data dawo tabani labarin komai, yarinya ta samu sakewar yin abunda taga dama,wai ta dawo gidanki da zama, narasa wace irin macece ke Zainab, ya akayi kika bari ta dawo miki Gida harta samu wannan yancin? Ashe kinshirya ganin ya’yanki sun fara binta coci”
Maama tai ajiyar zuciya
“Ni duk ba wannan ba Yaya, yaron nan fa Jawwad alamu sun fara nunamin kamar Santa yakeyi”
Zare Ido Yaya mairo tayi “ita wa din?”
“Haba Yaya mairo ya zaki dinga tambayata kaman baki San akan Wanda nake maganaba”
Yaya mairo ta jinjina kai
“Tirkashi, se yau na tabbatar da Zainab baki da wayo kina me hakan ke shirin faruwa garin Yaya?”
“Kedai bari duk yadda na kesa musu ido amma alamu sun fara nunamin hakan”
“To yanzu wani mataki kika dauka?”
“To Yaya mairo da na dauki wani mataki ai da banzo nanba”
“Gaskiyane, yanzu abunda ze faru zanzo gidan naku, zan zo in samesu, nasan abunda zanyi”
“To shikenan har na danji sanyi, wallahi”
“Karki damu kibar komai a hannuna”
Da haka sukayi sallama Maama ta koma Gida

Jeje ne ya kalli Hannah,
“Hanna akwai bukatar kara himma akan Jalal, idan mukace zamu cigaba da bin komai a hankali muna lallabashi to aikin nan base yiwuba”
“Nima nayi tunanin hakan amma me kake gani za ayi?”
“Birthday Jalal saura wata daya, a wannan lokacin nakeson mu kaddamar da komai, ko ya rayu yayi abunda mukeso, ko kuma……………….

Ilham tana kwance ta lumshe ido, da alama tana son yin baccine, wayarta ta fara ringing, yamutsa fuska tayi takai hannu da niyyar yin rejecting kiran taga sunan malam Wada a jikin screen din, da sauri ta tashi zaune taje tasawa kofar dakinta key ta dawo ta daga kiran
Suka gaisa, sannan yace
” dama batun Yarinyar nan da kikayi min magana akanta ranan ne”
“Nagane Jalila kenan”
“Yawwa ita nayi bincike akanta amma akwai Matsala…………

Share please
More comments more typing……………………..

????️????️????️????️????️
[9/12, 6:02 AM] +234 816 830 7871: ????????????????????????????????????????????????????????????
????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????

_ABDUL  JALAL_

  _WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_
(Daddy's girl)

           PAGE-  42

PART 1

_Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam)
Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa’azantarwa, ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa.

Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode.
Ina me neman afuwarku masoyana, kwana biyu banyi typing ba wayata ta dan samu matsalane
Sannan ina kuma neman afuwarku bazan samu dinga yi muku posting kullum ba saboda zan koma lectures online, Nagode da kulawa

   _My first novel_

Sassauta murya Ilham tayi sannan tace
“Malam matsala kaman yaya?
” eh nayi bincike akan yarinyar nan, amma abune mawuyaci asiri yayi tasiri akanta, zanyi kokari inga aikin dazanyi akanta amma kema sekin dage danaki kokarin domin samun nasarar kawar da ita gefe”
Ajiyr zuciya Ilham tayi,
“to shikenan malam nagode”
Sukayi sallama Ilham ta yi shiru nawani lokaci sannan tai kwafa
“indai makircine Jalila tasamu daidanta, nasan abunda zanyi”

Hanan tacigaba da kiran Jalila tana takuramata akan Jawwad, in Jalila taki dagawa tabita what’s app, duk Yadda Jalila taso ta dinga kokarin danne kishinta amma takasa, itakuma hanan kaman Jalila tana zigata, ta dage ita Jawwad takeso.
Wajen karfe shadaya na safen yau yaya mairo tazo gidansu Jawwad, tunda matar nan tazo gaban Jalila yake faduwa, dan tasan yau ranar cimata mutuncine, tunda yaya mairo bata kaunarta,
Aikuwa tunda tazo take bakaken maganganu, ita dai Jalila ta makale a daki taki fitowa
Jawwad sun gama breakfast dinsu, suna hira da Jalal, Nana ta kira Jawwad a waya
“yaya kana ina? Nazo part dinka baka nan?
“Nana ya akayine? Muna tareda Jalal”
“Yaya Jawwad, yaya mairoce take nemanka fa”
Gabansa ne yafadi
“Nana nikuma, me yafaru? Wani abun nayimata?
“wallahi bansaniba, se faman fada take niban san akan me take fadan ba, tace lallai kazo”
Ajiyar zuciya yayi
“to gani nan, ina zuwa”
Ya sauke wayar a hankali, Jalal ya kalleshi
“ya akayine?”
“wai yaya mairoce tazo tana nemana bansan me nayi mata ba, banason fadan nan nata”
Tsaki Jalal yayi
“ni wallahi kana bani mamaki, to dolene sekaje ai ba dole bane,”
“haba Jalal itama kamar uwa take a gurina fa, ya za ayi takirani naki zuwa”
“to haifarka tayi, sekayi tayi, tashi muje, akwai abunda zanyi a dakinka”
Jawwad ya Mike suka fito, suka tafi gidansu Jawwad, Jalal yayi part din Jawwad shikuma Jawwad yai cikin gida, Jawwad yana zuwa ya tarar da Yaya mairo, A palour Maama na kusa da ita, ya shiga cikin palour ya tsaya daga bakin kofa, ya durkusa yana gaida yaya mairo
“shigo mana kawani tsaya daga bakin kofa, kaman mara gaskiya, dama ba gaskiyarce da kaiba”
Karasawa yayi gabanta ya zauna ya da n risinar da kansa, sannan yace
“Nana tace kina nemana”
“eh ai naganka, takanas nazo gidan nan domin in maka Jan munne, Mahaifiyarka taje har gida ta sameni akan taga take2nka na shigewa wannan yarinya, yar gidan arniyar nan, to bari kaji kaf zuriarmu babu arna dan haka bazamu hada zuria dasuba jan kunne nake maka, karka kuskura kasawa zuciyarka zamu bari ka aureta, bamu shirya ganinka tsakanin massalaci da coci ba”
Dagowa yayi ya kalli yaya mairo
“haba Yaya, Jalila fa ba arniya bace kuma koba komai itama kanwata ce, kuma batada wani aibu”
Maama ce ta kalleshi
“au Jawwad abun har ya Kai ana maka magana kana mayarwa”
Yaya mairo ta kalleta
“ai shiyasa nace kinyi sake zainab,”
Jalila kam ga gaji da zaman daki ga shi ko karyawa batayiba, cikinta yafara kullewa ga sauran aikin gida, dazatayi, dan haka ta mike ta fito
Aikam karaf miyagun maganganun Yaya mairo suka fara dira a kunnuwanta
“muna da ya’n mata a dangi ga su Naja nan da kannenta ka duba a ciki, kasamu matar aure amma ka kiyayi kanka da fara soyayya da wannan yarinyar arniyar ragowar titi, suda basu san abun kunyaba, Allah ka dai yasan mazan da take bi, ni muslincin nasu ma ban yadda dashiba”
Gani sukayi ya kurawa kofar corridor ido suna juyawa, sukaga Jalila a bakin kofar tana hawaye
Yaya mairo ta tabe baki
“to almira da kika tsaya kina mana kuka ai ba karya nayiba”
Maama tace “to tama ce karya kike mana, aikowa yasani, nidai fatana a kyalemin yarona, ato bana son wannan shishshigin da ake masa”
Jawwad yace “haba Maama harda ke?”
Maama a tsawace tace “dalla rufemin baki,”
Yaya mairo ta juyo ta gyara zama sosai ta fuskanci Jalila
“ke ki bude kunnenki da kyau kijimu, gida dai gashi nan kinzo kin zauna, amma Jawwad karki sakawa ranki zamu bari ya aureki dan Zainab tace kusancinku da kuma zakewar dakike yayiwa kashedi nake miki yanzu, kisani ‘yar dangi’ yar cikakkun musulmai zamu aura masa, yar asali yar dangin uwa da uba ba wadda take da raunin nasaba ba, ba wanda yasan uwarki daga ina tazo ya akayi suka….
Juyawa Jalila tayi cikin kuka ta koma dakinsu, bazata iya jure wannan maganganunba, dan inta cigaba da tsayuwa za a iya samun matsala, Jawwad yabi Jalila da kallo, yana jin kukan Jalila har cikin ransa ya dawo da kallonsa kan Yaya mairo
“haba Yaya mairo, be kamata kisata gaba kina cin zarafinta ba, babu wanda Allah yayi shawara dashi lokacin da ya shiryamana kaddararmu, meye laifin Jalila anan”
Maama ce tace “wallahi ka kuma magana sena mareka, mu zaka gayawa abjnda ya dace muyi, kaika haifemu? Koka fimu sanin abunda ya dace da kai”
Yaya mairo tace
“kyaleshi ya dakeni, se insan kaji haushi”
Halima tana daga dakinta amma tana jin duk abunda akeyi, ranta ya baci matuka, bataji dadin abunda akayiwa Jalilan ba, cin mutuncin yayi yawa,
Ita kam Jalila tana zuwa dakinsu da kuka ta shiga, Nana tasan Yaya mairo ce tayi mata wani abun, dan girgiza kai Nana tayi ta Mike ta fito palour
Itama tazo ta tarar yaya Jawwad ya sunkuyar da kai yayi shiru Yaya mairo tanata surfa masa fada hadi da cin mutuncin Jalila da mahaifiyarta, ita kanta daba ita akayiwa ba seda taji ba dadi, dakinsu ta koma ta tarar da Jalila tana kuka hada sheshseheka zama tayi tana rarrashinta, amma Jalila taki yin shiru
Seda yaya mairo tayi me isarta Maama tana tayata, Jawwad ko kai bekuma dagoawa ba balle yace zece wani abu seda sukagama sannan yace “Allah yabaku hakuri za a kiyaye Insha Allah” daga nan ya tashi ya fita
Yaya mairo ta dawo da kallonta kan Maama sannan tace “to kema bazama zakiyi ba ki mike tsaye ki tsaya akan yaranki ki tabbattar kin rabasu, ba ruwanku da ita in tagaji ta tattara ta koma inda ta fito, baze yiwuba ankawo miki arniya an ajiye tana mjamala da yayanki ba”
Jiki a sanyaye Jawwad ya shiga dakinsa, yasamu guri ya zauna, ya kashingida a jikin kujera ya lumshe ido, Jalal dayasaka systems agabansa yana dannawa ya dan dago kai ya kalleshi ya maida kansa kan abunda yakeyi, Jalal gani yayi Jawwad bashi da niyyar yin magana, Jalal ya dan gyaran murya
“Me yafarune, me kayi mata?”
Seda Jawwad yaja wasu seconds sannan ya dago ya zauna sosai ya kalli Jalal
“Jalal narasa me Baby tayiwa Yaya mairo ta tsaneta haka ba”
Dan tabe baki Jalal yayi “Maybe Rashin kunya take mata”
“No Jalal, Jalila ba abunda tayi mata ta tsaneta, yanzu ma kiran datakemjn wai Maama taje ta sameta akan wai Jalila tana zakemin, wai kar insa ran zasu bari in aureta, babban abunda ya Kuma bata min rai, kiran Jalila da suke da arniya, me raunin nasaba, kuma Jalila taji, amma matar nan takiyin shiru tacigaba da cin zarafinta, ina jin kukan Jalila a cikin zuciyata”
Dan kurawa Jawwad ido yayi sannan yace
“Wannan matar bata da hankaline? Kokuma bataje Islamiyya ba, ita Jaleeelan shashashar inace ta tsaya, aka dinga zagin mahaifiyarta, Uwa tafi Uwane?”
Jalal yai maganar a hasale
“No Jawwad, nasan Jalila kara take mana amma tabbas da a wajene, bazata yaddaba, ni nasan hakan”
“Ba wata kara Jawwad kadinga gayawa yayar mahaifiyarka gaskiya, dan tana zaune a gidanku bekamata a dinga cin zarafinta ba, koni nan”
Ya nuna kirjinsa,
“koni bazan bari wani banza a gari yazagarmin uwaba, dukda abjnda ke tsakanina da mahaifiyata ba, me yasa za a dinga dawo da abunda ya riga ya wuce?”
“Haba Jalal ya kakeso inyine nayi kokarin nusar da ita amma itada Maama sun rufeni da fada”
“Mmm ba yadda zakayi, amma Jawwad mahaifiyar Jalila, Mutum ce, ba abar yarwa bace agurinmu, be kamata a ci zarafinta a gabanmu ba”
“Nasani Jalal, amma ka fahimceni, ba yadda na iya ne, nasani kowaye akayiwa haka baze Ji dadiba, Ina iyajin pain din da Jalila takeji amma ba yadda na iya, da nayi tunanin ko Abba zan gayawa, amma hakan ba mafita bane, ze kuma haddasa fitinane kawai”
“to wai ma tukuna zuwa kayi kace musu kana sonta”
Kallon Jalal yayi
“Jalal koban fada ba shakuwar dake tsakanina da Jalila, bata y’an uwanta bace kawai, Jalal ni son Jalila nakeyi dagaske aurenta nakesonyi”
Wani dogon tsaki Jalal yayi
“Wannan yarinyar mara kunya ita zaka aura, lallai kaci kai,”
“kaman ya naci kai? Meye aibunta?
“Babu kam, bayanma bata da kunya ka aurarwa Ummi yarta, wannan matar tazo tana zagin mata mahaifiya, ni danta wannan yarinyar komeyema akmata ban damu ba, amma cin zarafin Mace kaman Ummi be kamata ba, bekamata a cigaba da wulakanta taba saboda kanason yarta ba” Jawwad ya dan gyara zama sannan yace
“Jalal ina fatan komai ze daidaita insha Allah, amma ina son Jalila, so bana wasa ba”
“to shikenan Allah ya kyauta”
Cikin gida kuwa Jalila tayi kuka, har ta gaji, Nana taibata hakuri, se ajiyar zuciya Jalila take, Nana ta tashi ta tafi palour domin dakkowa Jalila ruwa, tana zuwa itama Yaya mairo tafara saukemata nata fadan, itakuwa Nana ta hade rai tana kunkuni
Jalila tana Cikin kukanne ummi ta kirata a waya, ta dinga kallon screen din har wayar ta katse, kuma kira ummi tayi amma wannan karon se ta Kai hannu ta daga
Ta tattaro nutsuwarta, suka gaisa da ummi
“lafiya kuwa naji muryarki kaman kina kuka”
“lafiya kalau Ummi banajin dadiine”
“meyasame ki?”
“Ummi ciwon marane fa kawai”
“Hmm Allah ya sawwake” tafada ba dan ta yaddaba”
Kaman an tsikari Jalila tace
“ummi yaushe zakije garin naku dan Allah ummi kije ki dawo, in dawo gurinki”
“akwai matsala kenan?”
“ummi ta tambayeta
” ba wani matsala ni dai kawai sonake kije ki dawo, bazan iya rayuwa ba kya kusadaniba, sannan na kagu inga yan uwanki ummk, “
Jikin Ummi yayi sanyi tasan akwai matsala ne take kokarin boye mata,
” Baby wayace miki idannaje dawowa zanyi? Bazan kuma dawowa ba nima a cikin ahalina zan zauna”
“haba ummi karkiyimin haka mana, wallahi ko ina kika tafi sena biyoki, bazan iya rayuwa babu ke a kusa daniba”
Ta karashe maganar tareda fashewa da Kuka, dama kukan take ta boyene dan kar ummi tagane
“is ok my dear, ina nan zuwa jibi Insha Allah, a satin nan zanje gida Nima kidena kukan haka”
Ummi taita rarrashinta, sukayi sallama
Wunin ranar Jalila a daki tayishi tana kuka, gashi ko abinci bataciba, Nana tayi juyin duniya akan Jalila taci abinci amma taki ci, haka take ma a bangaren Jawwad shi yayi breakfast amma bayan nan beci komai,
Jalal ya kalleshi
“kai nifa yunwa nakeji, kaje kace ta kawo mana abinci”
Jawwad ya kalleshi
“wakenan?”
“kafini sani ai, ni yunwa nakeji”
“haba Jalal nagaya maka halin da take ciki, ya za ayi ta wani dafa abinci”?
“Ina ruwana da halin da take ciki? Halin da cikina yake ciki ne ya dameni,”
Jawwad ya kalleshi
“toni na damu da halin da take ciki, ina ji a jikina har yanzu kuka take”
“Ko? Da gaske ka damu,? Aini ban saniba, tunda banga kana kukan ba kaima, sharokhan sarkin soyayya, kagani ka tashi kasamomin abinci”
Wani mugun kallo Jawwad yayi masa, ya tashi yashige bedroom ya bar Jalal a palour
Jalal yai murmushi ya girgiza kai
Bayan la’asar Maama ta kira Nana tasata a gaba suka fita, tareda Yaya mairo, sannan ta aiki Halima, akabar Jalila a gida,
Jawwad yaji karar motar Maama ya leka ta window palournsa yaga fitar Maama da Nana da Yaya mairo, Jalal ya uzzurawa Jawwad se ya tashi ya rakashi cin abinci, dan baze bari yjnwa tayi masa illa ba Badan Jawwad yanasoba ya tashi suka fita,
Fitarsu Nana, hakan yabawa Jalila damar yin kukanta yannda take so
Tabbas da watace ta gaya mata abunda aka gayamata yau a cikin gidan nan to da setayiwa Yaya mairo rashin mutuncin da harta mutu baza akuma yimata makamancinsa ba
Amma kash koba komai yakamata tayi al kunya ko dansu Jawwad, ga nasihar umminta data dingayi mata akan tayi hakuri dazaman da zatayi da mutane, gajiya tayi da zaman cikin gidan, zuciyarta na ayyana mata abubuwa, tasan tunda aka fara haka, lallai Maama zata dau shawarar cigaba da cuzgunamata, kuma yau da gobe se Allah dan wataran zata iya marin mace akan taba mata uwa.
Tashi tayi ta fito harabar gidan, zuciyarta na saka mata abubuwa dayawa
Ilham ce ta shigo gidan, ta hangi Jalila tsaye a wajen kofar shiga cikin gidan, ta nade hannuwa tayi shiru alamun tana tunanin wani abune,
Zuwa tayi zata wuce amma Jalila na tsaye a bakin kofar bata fito ba bata shigeba,
Seda su Jalal suka je karshen layi, sannan ya tuna yabar wayarsa, yace Jawwad yayi parking ya jirashi yaje ya dakko baxe dade ba, Jawwad yayi parking, Jalal ya sakko ya tafi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button