Uncategorized

ABDUL JALAL PART 1 HAUSA NOVEL

????️????️????️????️????️????️????️
[8/31, 8:26 AM] Safiyya: ????????????????????????????????????????????????????????????????

_ABDUL  JALAL_

  _WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_
(Daddy's girl)


           PAGE-  2

PART 1

_Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam)
Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa’azantarwa, ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa.

Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode.

   _My first novel_

Kallonta Nana tayi, ta ce
“kaman ya se kin rabasu, ina ruwanki dasu? kinga Jalila ba ruwanki dasu, Maaama ma tayi ta Hakura, Jalal ba ze iya rabuwa da Jawwad ba, bayan abokansa na banza ina ga Yaya Jawwad ne kawai mutumin kirki, kika sani ko Allah ya shiryeshi a sanadin sa? kawai muyi musu addu’ a.”

     Ajiyar zuciya Jalila tayi ta ce "Nana abotar Yaya Jalal da Ya Jawad sam bata dace ba,

barazana ne ga tarbiya da rayuwar Yaya Jalal mutumin dabe ji maganar Wanda suka kawoshi duniyaba ne kike zaton ze wani shiryu sanadin wan?i yau da gobe se Allah yasha giya ya kwana club yayi sa’insa da mahaifiyarsa shi kike tunanin ze shiryu sabodaa wani aboki Sam bashi da tarbiyya Nana .”

 Jalila Allah shi yasan manufar hada abotarsu duk da banbancin halayensu, kawai muyi musu addua shine mafita mukuma muyi abinda ke gabanmu."

“Nana ni kam nacji amma ban gamsu da bayanan ki ba , zanyiwa Yaya Jawwad magana,”

” to Allah yatemaka inji Nana, amma kome zakiyi karki shiga harkar Jalal.”

Ajiyar zuciya Jalila tayi ta ce “karki wani damu Yar uwata, ni dai fatana yafita shirgin yayana, bana so yazama irinsa ya lalatamin Dan uwana,
tunda shi lalataccene ma tayashi da addu a.”

“To Allah ya baki Sa’ a, nima da naso hakan”.


Sanye yake da kananan kaya, wando 3quater fari da Riga T-shirt itama fara, yayi kyau sosai, yasa hannu ya dauki turare ya feshe jikinsa dashi, ya dauki wayoyinsa dake kan mudubi da mukullin motarsa yafito.
Kai tsaye ya nufin inda akayi parking motoci, sekuma ya juya ya nufi cikin gidan.

 yanazuwa kofar parlour ya budee ya Shiga, ba sallama ba komai fuskanan tashi a daure tam babu alamar fara'a

parlour shiru se kamshin turaren wuta dana abinci da ya gauraye parlourn, gefe kuma Ilham ke kwance kan kujera 3seater tana kallon Tv.

“keee!!”
ya fada cike da gadara ,
a dan tsorace ta dago Dan batasan ya shigo ba, “Yaya Jal sannu da zuwa”

Ta fada tana kallon sa tare da yaba kyawun da yayi acikin ranta, be amsa ba yace

” Ina matar gidan nan take?”

“matar gidan nan kuma?”
ta maimaita tana dubansa
“ba kiji bane ko kuma tsabar rainin hankaline?”

Adan daburce ta ce “ai jinai kace matar gidan nan, wai mummy kake nufi?”

” Yaushe raini ya shiga tsakanina dake ne? har nake magana kina maimaitawa, akwai wata mata a gidan nan banda itane?”
Mamakinta ne yakasa boyuwa, lallai yaya Jalal abin nasa ya girmama, mummyn tasa ma bata tsiraba wai matar gidan nan? tabdijan, amma ta dake ta boye mamakinta ta bashi amsa da
“ta fitane, taje saloon”
“mtseww” ya Dan jaa tsaki , “inta dawo ki ce ta kirani a waya, ina da magana da ita.”

Bai jira mezatace ba yasa kai yafita,
“ohh God ni Ilham, yaushe Yaya Jalal ze fara sakarmin fuska ne yana kulani? kullum mutum fuska a daure Yaya Jalal whyyyy?? “

tafada tana jifa da pillon hannunta,
“I must do something!”
tafada tare da mikewa tabar parlour.


JALILA ce zaune akan carfet tana waya da umminta,
“masoyiyya nayi missing dinkifa irin sosai din nan ummina”,
“bawani nan tunda kika iya tafiya kikabarni,”
“ummina kenan kina birnin zuciyata fa”,
” ke tafi can ya mutan gidan naku kowa lpy?”
“ummi garin kano ya hadu kinsan na dade banzoba zuwan yayi min dadi”
“to hakan yayi kyau”,
“ke dazu wata kawarki tazo ta bani sako in gayamiki amma wayata babu caji in anjima mayi waya yanzu fita zany”‘
“ina zakije kuma ummi?”
“inda kika aikeni”
“huh ummina ta kaina adawo lafiya anjima zankiraki insha Allah”
“to shikenan ki gaida ya’n uwannaki ki gaidamin da halima(Maman su jawwad) kar inkirata tazata dankina gidanne nakirata to Ummi zasuji insha Allah”.

“To shagwababbiya Yar gidan Ummi wannan shagwaba haka kinfa girma JALILA Cewar JAWWAD

Murmushi JALILA tayi tare da fadin “Allah yatemaki babban Yaya ai ba a girma a gurin iyaye mussaman iyaye mata”
Murmushi yayi tare da fadin “kekam halinki yana nan baki canza ba kome mutum yagayamiki kinada amsa dai dai da abinda yace JALILA baki abun magana,
dariya sukayi gaba daya
“yace ba wannan ba tukuna yanzu dai ya studies dinki komai lafiya dai ko?”
“Alhamdilillah Yaya JAWWAD komai lafiya ina karatuna yadda yakamata,”

” to masha Allah haka akeso amma kamata yayi kiyi waec a ss2 se Asama miki admission a BUK kidawo kano gaba daya”.
“Tab to umminawa fa shikenan in batta acan”
” murmushi yayi yace haba JALILA wataran fa aure zakiyi kitafi gidan miji ko me rabawa taraba (MUTUWA!!!)”
” Kaman yadda ta rabani da banana ko ta fada idonta cike da hawaye Yaya jawwad karkamin wannan fatan, idan narasa ummina yanzu wanake dashi daze soni kaman su,
abbana yatafi yabarni bana fatan ummina ta barni, nafiso in mutu in barta”
“Haba JALILA kinga share hawayenki kinji qanwata bahaka nake nufi ba yanzu idan Abba yaji furucinki na wa kike dashi baze jidadi ba Abba yana matukar sonki ya daukeki kaman yanda ya daukemu ko kinrasa kowa ni INA tare dake kanwata har abada yayanki yana tare dake duk wuya duk dadi zan kasance tare da ke”.

   Taji dadin kalaman yayannata mutum ne nagari me kirki tayama zata bari abotarsa ta dore da wancan sakaran yabata matashi baze yiwuba dole tayi wani Abu, "Yaya JAWWAD inason in maka wata magana....

Mamansu jawwad kuwa da tazo shigowa parlourn ta riski hirar tasu ta labe tana sauraransu abin se ya kular da ita, me jawwad yake nufi da ze kasance tare da yarinyar nan duk rintsi aikuwa baze yiwu ba, dole tayiwa tufkar hanci bazata taba bari danta ya auri jalila
ba in ma sonta yakeyi danko maqiyinta tagani ze aureta tahanashi saboda gudun bacin suna ahaka dai gata kamilar yarinya tagari me da a amma babu asali me kyau ta danyi tsaki
( ???????????? tooo wata sabuwa me ummu jawwad take nufi ne)

Wayartace takama ringing Wanda yasa dole ta fito badan tagama jin hirar tasuba tare da kakalo murmushin yake Yaya da kanwarsa hira akene “wlh kuwa maaamaa, ni zan wuce zan raka JALAL wani gurine,
gaban jalila ne yafadi jin ya ambaci jalal ta dago a Dan razane tana kallonsa,
“to sekun dawo ka kula da kanka Cewar maaama”,
“sisy akwai damuwane” yafada yana kallon JALILA,
girgiza kai tayi yace to sena dawo, “safe journey”
tafada a takaice yace thank u sisy maaama sena dawo to asauka lafiya Allah yasa ya amsa yafice.

   Maaamace ta amsa wayarta data cigaba da ringing salamu alaikum tafada ta danyi shiru to shikenan inkin dawo da magariba zan turo su Nana su karbarmin to nagode,

 Banyan sallar magariba maaama ta aiki su Nana tace su shiga gidansu JALAL zasu karbo mata sako gurin mummynsa, 

da sallama suka shiga suka Tarar zata fara cin abinci, gaisawa sukayi suka fadamata Aiken
” tace to bari in dakko muku sakon” “aa tunda kinzuba abinci kigama tukuna Cewar JALILA,
Eh momy gama bari muje gurin ILHAM kafin kigama inji Nana to shikenan sekun fito.

Tana zaune a palour tana cin abinci yashigo yasamu guri ya zauna ya kalleta
“ILHAM bata gaya miki saqona ba?” “tagayamin”
tabashi amsa a takaice,
“meyasa baki kirani dakika dawoba?” nace inason magana dake “ban niyyaba” tabashi amsa

Dakin ilham suka shiga ta kwanta rub da ciki tana kallon hotunan JALAL
sallamarsu yasa tayi firgigit ta aje wayan
“yan matan maama sannunku dazuwa
“yawwa sannu” JALILA ta amsa haka kurum ILHAM intaga jalila se gabanta ya dinga faduwa tarasa meyasa,
NANA takalli ILHAM “” daddawar daki wannan zuwannaki ba yawone?”

” ke dai bari wani abu ke damuna wlh,”
” tooo menene inji Nana “
kedai bari semun hadu kawai”,

jalila tunawa tayi zasuyi waya da umminta in anyi sallar magariba tabaro wayar a Gida maybe tana can tana kirana, “Nana bari inje indawo inazaki inji Nana yanzu zan dawo tafito da Sauri

“Dubai nakeson tafiya next months
kudi zaki turamin a account”

” mezakaje kayi a Dubai?”
” aa meye kuma na tambayata ina daddy yace idan INA bukatar kudi abani to mene na tuhumata kuma”

se kajira ubannaka yadawo seyabaka sangartaccen banza yaushe rabonka da makaranta Baka zuwa karewama sokake ka tsallake kabar kasar karatun ko oho ko?

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button