KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVEL

Shafa kanta zakiyya tayi tace what are sisters for?Idan ban fada ma little sis dina Gaskiya ba wa zan Fadawa ? Dariya ayush tayi tace am not that little fah. Shekaru nawa ma kika bani ko 9 bai kai bafa.
Dungure kanta zakiyya tayi tace munji dai na girmekin Ashe.

Dan abin tausayi ayush Tayi tace sis Dan Allah Kuban key din motanki inaso inje in siyo wani abu. Zakiyya tace ki bayar a siyo miki mana yaushe muka iso garin ai akwai gajiya. Ayush tace abin is a little bit private kinga ne ai? Zakiyya tace okay bari in canja kaya muje tare mana nima dama inason inje shopping ayush tace yanzu fa kikace akwai hajiya ki bari gone sai mu fita ko? Zakiyya tace to kije dasu sahir mana kinsan birthday din sahir ya kusa he will be six years next month. Ayush tace nima ba dadewa zanyiba, gobe ba sai muyi Komai da Komai ba?

Zakiyya tace okay ba matsala amma karki Dade fa.
Ayush tace okay na wuce Toh saina dawo.

Fita tayi tana tafiya tadan kunna waka tana gyada kai abinta tana rausaya wa. Birki ta taka taji shiru kara takawa tayi still taji shiru ihu ta fara yi yayinda Motan ya fara kobo da ita akan titi.
Bata ankare ba motanta ya Shiga kasan wani trailer.

Mutane ne suka cika wajen makil ga hasken rana ya dallo wal bari yayi zafi Motan da ayush ke ciki bazaka dauka mutum zai fita ba saboda yanda Motan yayi raga raga ga ayush kwance agefe cikin jini atake akayi asibiti da ita.

Wayanta wani ya dauka wayar ma tayi raga raga. Cire sim din yayi yasa a wayarsa sweet sis ya gani Dan haka ya kira

Zakiyya zaune akan gado tana sulhu tsakanin sahir da safwan Cewa Idan suka raba Kansu kowa zai iya Shiga tsakanin su Wayanta yayi ringing ganin ayush ne yasa ta dauka da yar fara’arta amma labari da ya risketa shi ya gigitata tana kasa yin Komai.

Tashi tayi a zabure ta fice ta zauna dabas a parlour Kamar yar bori ta Cire wig dinma Ashe tanada gashi ba laifi rashin godiya wa Allah yasa ta yin karu ihu ta fara yi

Waiyo Allah na,na Shiga uku!YAZEED ka taimakamin yar mutane shikenan ta mutu !ta mutu waiyo ni Allah na.

????????

Yazeed zaune a gefen minal fuskannan babu alamun wasa hannunsa rikeda takalmi. Minal ma fuskannan babu fara’a sai zunburo baki take Wai saboda dance taci abinci kamin yaje wajen mom Idan ba haka ba tasha takalmi.

Ihu suka fara jiyo sama sama yazeed ya ajiye takalmin ya nufi kofa yana farin wannan Kamar muryan zakiyya minal ma dauko sandan ta tayi tana fadin aiko itace.

Harara yazeed ya aika mata yace Koma ki zauna. Tace Allah sai na bika ganin Idan ya tsaya fada da ita zai bata lokaci yasa ya ficewar sa.

Zakiyya suka riska sai ihu take duk ta birkice. Durkusawa yayi a gefenta a tsorace dan bai gaba ganinta a irin yanayinnan ba yace menene? Sweetheart me ya faru? Menene?

Kuka taci gaba dayi tana farin shikenan an kashemin ita an kashemin ayush. Ta mutu ! Ta mutu

Yazeed yace what? Me ya same ta? Tana…tana asibiti trailer ya taketa.

Innalillahi wa inna ilaihi raji’un ne ya kacame parlourn domin mom da Jamal ma sun fito.

Atake suka dunguma suka nufi asibiti
Koda suka isa su sahir da safwan sun jigata saboda kuka nan suka nemi Inda take akace ai har anshiga theatre da ita domin har Yan sanda sun gama aikinsu.

Zakiyya muryanta har ya fara dashewa ta fara ganin bibbiyu.

Ta zama abin tausayi idonta sun kumburo. Minal matsowa kusa da ita tayi da Dan crutches dinta ta dafa kafadarta tace Kiyi hakuri aunty zakiyya Insha Allah zata warke. Zata tashi Kiyi hakuri.

Office din likitan suka dunguma sukayi. Bayan sun shigo likitan yace ma yazeed menene alakar ka da patient ? Yace shi yayanta ne doctor din yace okay amma nikam Kamar Kaine captain yazeed ko?

Yazeed yace yeah nine Dan Allah ka fada mana halin da take ciki ajiyan zuciya ya sauke yace a Gaskiya ikon Allah ne yasa ta rayu domin kuwa a irin ciwon da taji ba’a magana yanzu de she is out of danger amma she is in coma sannan jini ya Shiga kwakwalwarta dukda Mun Cire there is possibility zata manta wasu abubuwa or zata iya samun recognition disorder.

Innalillahi wa inna ilaihi raji’un shine abinda suke furtawa.
Daga kafadan yazeed minal tayi tace tace Allah ya nasu lafiya karku damu zata warke. Amma Dan Allah inada tambaya.

Kallonta sukayi dukkansu alamun sunaji tace kowa daga wani Abu ya sameshi sai a ce ya Shiga coma yanzu mutum uku Suna coma Wai coma dinnan menene.

Likitanne yace coma wani yanayi da mutum yake Shiga Wanda yayinda wani shock ya samesa ko yayi hatsari psychological issue ne which is cause by a traumatic event.

Minal gyada kai tayi bawai Dan ta gane ba. Wayar yazeed ne ya fara ringing. Dr Mashkur ke kiransa hakan yasa ya dauka tareda sallama.
Amsawa Mashkur din yayi yazeed yace harka iso kenan?Mashkur yace da izinin Allah gani a kasata kuma a garin Kaduna.

Yazeed yace masha Allah Toh gamunan zuwa saide wani hanzari ba gudu ba ka samu extra patient. Mashkur yace oh shit ! Buddy kar abin yayi yawa mana har 3 patients.

Yazeed yace aikinka ne ai so….
Mashkur yace of course what am I here for?
Sallama sukayi yazeed yace zan kawo maka surprise. Mashkur yace and explain why na jika so sad not as cheerful as you use to be.

Dafa zakiyya yazeed yayi yace sweet zamuje dauko Mashkur kinji karkisa damuwa a ranki Insha Allah zata tashi.

Riko hannun minal yazeed yayi tareda yiwa lukman ido alamun muje ko?

……………

Mashkur ne ya fito Daga departures door a airport din Inda ya hango yazeed yana Daga masa hannu.
Runguman juna sukayi sannan suka kashe. Mashkur yace buddy irin wannan kyau Wai miye sirrine?

Yazeed yace tsaya nan gauranci ya kasheka. Lukman yace koni nan da ka ganni da aurena yanzu.
Yazeed yace wannan auran maka dashi da babu ai kusan daya. Lukman yace haka kace?yazeed yace kwarai ma kuwa Idan ba haka ba gobe muga amarya a dakinta tunda an gama Komai.
Lukman yace is that a challenge? Yazeed of course is a challenge.
Shaking Hannu sukayi yazeed lukman yace challenge accepted.

Mashkur ne yace kudai gaskiya bakuda kirki yanzu ace duk kun? yi aure babu gayyata? Sukace sorry man abunne yazo a murde.

Tsuguna minal tayi tace ina wuni. Sai a lokacin Mashkur ya lura da ita domin ta labe a bayan yazeed sai tsilla ido take. Yo tazo airport bata tana ganin jirgin sama ba sai a TV ko photo.

Baki Mashkur ya saka yana Kate mata kallon kamin yace Masha Allah tabarakallah.
Buddy wannan surprise din yayi kace kai ka tanadomin. Shine baka taba fadamin Kanada kanwa zukekiya irin wannan ba? Yazeed yace kai bawan Allah Dan yanzu ba wani buddy wannan da kake gani matata ce.
Mashkur yace matarka? Yace yup itace amaryar tawa ai.
Date saitin zuciyarsa yayi yace amma kaide baka kyautawa wallahi ya zakayi ta aure kyawawan to ni in auri me?

Finciko shi lukman yayi tare da yin tsaki ya dannashi a mota yace ni wuce mu tafi Dan Allah mutum sai surutu halinku daya da Jamal.

Gida suka nufa suka bawa Mashkur masauki yaci su abinci sai Santi yake yana kurba kunu. Daura minal yazeed yayi a cinyarsa sannan ya rada mata a kunne baby anjima da daddare kiyimin pancake. Murmushi tayi tace me yasa sai da daddare. Yace saboda banason kowa yaci. Ahankali sosai tace marowaci yace naji fa. Ta ai na manta Ashe kunnen aljanu gareka. Hancinta ya Dan gwala yace ke dinnan ko.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button