NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL BY MAMUHGEENOVELS

NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL

NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL BY MAMUHGEE

Wannan zancen mafarkin Mahmoud ne kawai da firgicin ciwo daya taso Masa mudai muyi Mai fusshemu
Kisake tabbatarwa Sa’adah Babu inda zata da wannan yarinyar hakama yau idan nakoma Zan sanarwa honourable dasu Alhaji Qarami da wannan Dan uwan Mahmoud din Dake can nijar shima zansa Alhaji Qaramin yakirasa Kan zuwansu commissioner neman auren Sa’adah din tunda sun takura akan basason asaka dogon lokaci Dan akwai tafiya agaban yaron zuwa Greece dakuma Sa’adah din zaije shine Dan batada hankali take cewa zata tafi da wanni.
Kisani idan Kika Baki rufe ido kin tsaya akan al’amarin ba Haka zata dage ta lalata rayuwarta akan wadda ba’a da tabbacin menene ya sameta,
Zan tafi zuwa gobe Inshallah zaa karba komai nasu.

Har umma Jamilan ta dauki keys din motarta da Jakarta ta fita ta wuce momy taba motsaba sbd batasan abinda zata fada ba komai na duniya ya isheta
burinta daya kawai Sa’adah tayi aure tasan ko ahaka ta rasu tabar Sa’adah din a inuwar aure da Wanda zai kula da ita.

Bayan tafiyar umma Jamila Bata tashi daga inda takeba saida akai Kiran magriba ta miqe tashige dakinta ta nufi toilet tayo alwala tazo ta fara Shirin sallar magribar.

Da daddare bayan sallar ishai Sa’adah ta kamo hannun Laylah suka fito Palo sbd yafi iska dakin akwai zafi sosai sbd hadari.

Momy dake zaune palon tana amsa wayar Kawu saidu Dan uwan Abban daya daya rage Masa Yana can nijar daga nema yayi zamansa can ya Gina nasa iyalin Yama zama Dan can din
Yakirata ne akan Kiran da akai Masa na maganar neman auren Sa’adah wadda yake Bata hakuri akan bazai samu damar zuwaba saidai lokacin auren zaiyi kokari yazo ta amsa Masa da to kawai sbd zumuncin dama yanzu sai ahankali kowa nasa yasani shiyasa jikinta yaqara sanyi sbd ganin dai su Sa’adah din gwarama ace basuda dangin uba tunda shikansa uban gashinan Babu Wanda yanuna damuwa akansa bare Azo garesa baresu yayansa,
Itama nata ‘yan uwan matuqar Sa’adah ba auren Mai arziki tayiba duk kaunar dasuke Mata zasu iya juya Mata baya itama.

Numfashi ta sauke tana kallon yanda Sa’adah din ke yiwa Laylah Dake kwance lamo a gefenta firfita tana duba saqon daya shigo wayarta.

Dauke kanta tayi daga kansu tana tasowa ta dawo gefen Sa’adah din wadda itama tayi zufan tadauka wani maficin tafara yimata firfitan ahankali itama.

Juyowa Sa’adah tayi ta kalla momyn da fuskar sanyin jiki ta bude Baki ahankali tace”

Momy meyasa bazaki sawwaqawa kankiba kibari natafi da Laylah sbd kema barinta gurinki damuwace agareki,
Umma Jamila nason daukan Laylah ne taje da ita gidanta
Tayaya Laylah zata iya wani aikin bauta a wannan yanayin matuqar baso ake ta qarasa juyeba,
Shin duk ranarda Abba ya farfafo yaganta ahakan kina tunanin sai qara Jin nadama ko tausayin halinda Kika shiga?wallahi Momy tsanarmu zaiyi duk mu duka duk ranarda ya farka ya ganta depression ya kusan haukatata gabaki daya.

Momyn batace kalaba saidai sauraron Sa’adah din datake kawai tana shiga nata tunanin Dan tunda Abba yabar gidan yake asibiti Takoma koyaushe cikin tunani take
Tarasa Ina zata Kama a rayuwar,
Ta rasa Yaya zatabi tacinye wainnan jarabawan da ake jarabtarta dasu.

Washe umma Jamila tana zaune babban palon gidanta tana zubawa Mai gidanta Honourable Atiku tsohon member house of Rep coffee aka kiransa Ana sanar dashi labarin zuwan AB TURAKI Nigeria Inshallah washe gari….

Tashi yayi daga jinginen dayake a kujerar 2seater cikin sauti Mai tsagwaron neman tabbaci da mahimmancin labarin garesa yace”

Ayi Mana booking tickets tun a Lagos zamu tarbesa Inshallah zamu samu ganinsa saimu shigar da proposal dinmu Dan idan ya iso Abuja zaiyi Mana wuyar gani Amma dai na tabbatarda zai iso anan garin sbd Amininsa Dake asibiti
Amma dai ayi Mana arranging tafiyar Dole zamu tarbesa a Lagos din musamu ganinsa acan.

Yana kashe wayarsa numbern uban gidansa ya nema ya Danna Masa Kira cikin qanqanin lokaci ya isar Masa da zancen shima take yace ayi Masa Shirin zuwa Abuja shikuma acan zai tafi samun appointment na ganinsa.

Wani yawu umma Jamila ta hadiye Jin tabbacin zaizo ganin Mahmoud,
To idan dagaske fa Zainab take maganar Mahmoud ya bawa AB TURAKIn auren Laylah,
Innalillahi wainna ilaihirrajiun
Da kuwa sun shiga uku sun lalace,
Yanzu ga Sa’adah Amma zai bada Laylah?wane so yakewa uwar wannan Laylah ne da ko aciwo ya zabesu akan zainab da ‘yarta
Aikuwa zata dakatarda neman Sa’adah tagani idan da gasken AB TURAKin Zai karba tayin auren Aminin nasa,
Idan kuwa ya amsa wallahi Sa’adah zasu basa a Laylah bazasu yarda wannan Aljannar duniyar ta kubuce musuba ta sauka gurin wadda batadama dangin rabawa arzikin idan taje,
Gwara Sa’adah taje Koda wulaqanci tasamu cikinsa ta Haifa musu abinda zai gaje duka dukiyar da TURAKin ya Tara da mahaifiyarsu Anne Amma basuda magajinta,
Dukiyar da su kansu basusan iya abinda suka mallakaba Amma Babu magada
Ga duniya tasaka idon ganin ko Anne din ko Turakin waye zai gaji dukiyar wani tunda ita shikadaine ‘danta sai ‘dan yayarta datake riqo Wanda shima yazama babban mutum
Shima Turakin ita kadai garesa magajiya sai Matarsa da itama kanta batasan iya adadin dukiyar data taraba ta qarqashin mijin nata shiyasa ma Bata damu da rashin haihuwaba Dan kuwa a duniya ita kadaice tasan ba haihuwace bayayiba lafiyar saduwa da macece baida ita Dan kuwa tsawon shekarunsa da aure Bai taba muamalar aureba da mace ko matarsa koma ba matarsaba.

Kasa hakuri tayi cikin zurfafa tunani tafara korowa Hon Atiku bayanin komai na Bawa Turaki aure da Mahmud yayi kafin kwanciyaresa saidai take ta nuna Masa Sa’adah yabada ba Laylah ba
Ya saki fuska Yana sauraron zancenta cikeda shiga tunani shima kafin yace”

Tabbas ayanda akasan kusanci da Amintarsu tun suna yara zaiyi wuya Turaki Bai karba aurenba duk da Tai Masa qanqanta Amma kasancewar yanayin ciwo na Mahmoud din zai iya amsar auren saidai mun dage da addua ya amsa Dan hakan Kamar wani saukar rahamane garemu gabaki daya.
Miqewa yayi Yana cewa”

Bari kiga nafita zansa Aminu yaje yau akai sadaka duk Ina mabuqata suke Allah ya yardar Mana wannan al’amarin.
Ficewa yayi Yana fitarda wayarsa yasaka Kiran Aminu PA dinsa
ya fice yabar umma Jamila cikin tsananin zurfin tunani kafin daga baya ta miqe tayi daki ta dauka wayarta takira babbar yayarsu daya hajiya Karima Dake Abuja tafara koro Mata bayanin abunda kenan
Take Haj Karima tace a tabbatarda anyi delay din neman auren Sa’adah din har aji daga bakin Turakin maganar auren idan zai karba kokuwa aa kafin tace aturo Mata Numbern Kawu saidu yayan Mahmud din dasuke uwa daya uba daya subi ta hanyarsa Dan kuwa shi zasu turawa Turaki akan mganar tunda Yana ganin girmansa.

Da yamma kiransu commissioner yashigo wayar Hon Atiku
Yafara musu Yan kame kamen baya Nan tafiyar gaggawa ta kamasa
Sai suka nema Alhaji Qarami Wanda shima tuni Haj Karima takirasa shikam Kai tsaye yace musu Subari sai Hon Atikun yadawo daga tafiya
Da Haka suka fara Wala Wala da zancen neman auren
Hakama umma Jamila ta ringa yiwa hajiyar commissioner din labarai dabam dabam sunata Jan al’amarin.

MAMUH

????????????Kuyi following Dina Dan samun posting akan lokaci dama sauran novels Dina complete ????????

Mamuhgee @Arewabooks

????????????????????
KUFAN WUTA
Safiyya Huguma

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button