NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL BY MAMUHGEENOVELS

NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL

NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL BY MAMUHGEE

No ba yanzu ba sai sanyin ya rage.

Marairaice fuska tayi tana Shirin sake magana ya kwantar da ita Kan gadon yana juyawa ta rumgumo qugunsa tana cewa”

Please Abbahhh..

Rungumar dataiwa qugunsa yasa yanayinsa sauyawa ya juyo Yana mata wani irin kallo daya sata sakar Masa murmushi tana jiran abinda zaiyi
Sai gashi ya ranqwafo yana kallon fuskarta ya zare singlet dinsa Dake jikinta Yana binta da wani sabon kallon har lokacin murmushine a Kan fuskarta.

Komawa sukai cikin gadon suna shaaninsu
Wannan karon ma har sai datafi jigata dan Haka ta lallaba tayi wanka da qyar ko shinta Bata busarba ta zube Kan gadonsa tana komawa bacci daga ita sai singlet dinsa dukkanin fararen cinyoyinta a bayyane suna daukan ido.

Saida baccinta yayi nisa ya zare jikinsa daga nata ya miqe ya nufi toilet daureda farin towel yashige.

*Tun cikin dare da Siddika ta sanar da ita Turakin ya dawo ta tattaro ta dawo gidan sbd shima tun Bai dawo dinba yace zaiyi magana da ita taqi tsayawa Dan Haka yanzu suna buqatan kudaden aiki sosai shiyasa Zinat ta lallabata ta dawo Dan su samu kudin aikin dayake gabansu..

Ko data dawo gidan Ana ruwan sama Dan Haka Bata nemesaba sai tunda sassefen taji bazata iya jiraba ta fito gari ko gama haske sosai baiyiba ta nufi bangarensa dayake tasan password din kofarsa ta farkon shiga Kai tsaye ta bude ta shige tareda rufowa ta nufi stairs ta Haye.

Tana tura kofar palon saman da farar lafiyayyar bra tafara cin Karo a qasa gabanta yayi mummunan bugawa
Ta bude Ido da kyau taga bra ce Kuma ta mace
Take ta kalli kofar bedroom dinsa tana fiddo qananun idonta dasuka fara rufewa.

Palon tafara rarraba Ido tasake hango rigar mace a yashe Kan kujera bayan bra data fara gani..

Wani malalacin numfashi tasaki tana cewa”

Cab,yau dai Allah yayi wahalata taqare ba sauran boyo koma wacece.

Wayarta dake hannunta tafara dagawa Kai tsaye takira Zinat jikinta har rawa yakeyi tace”

Zinat ki tabbatarda kin hada takardun ciwon haukata Dan yau wlh kisa zanyi idan anje kotu ki biyar dama Banda cikakken hankali.

Da sauri Haj Zinat Dakeda sauran bacci a Ido ta zabura zaune tana durowa gado tace”

Na’ima karkiyi komai kibari ganina zuwa Dan Allah karkiyi wani abun…

Kashe wayar Ms Na’ima tayi tareda wurgarwa ta nufi dakinsa gadan gadan ko gani Sosai batayi tsabar masifa ta bude dakin tashige.

MAMUH#

[7/10, 9:37 PM] +234 704 076 8969: Mamuhgee 52
A gidan zinat ta wuni tana saqa da warwara,
Ga Na’iman cikin baccin sai Dan fizgawa takeyi lokaci lokaci,
Kanta ya dauka zafi sosai ita kanta yanzu komai ya tsaya cikin kanta,

Na’iman takeson fara dawowa da ita saiti kafin tafara tunanin abin Yi akan Laylah tun kafin afara Ankara da halinda suke ciki.

Sai dare tabar gidan bayan tabawa siddika kyakkwan gargadi akan kula da Na’iman karta Bari ta fita idan ta farka.

*Laylah ma a daki tayi wunin ranar idanuwanta sun kumbura iya qarshe sbd kukan datasha,
Gabaki daya kewa da kadaicin rayuwa takeji gashi ta kashe wayarta sbd Kiran da Abban keyi Mata cikin damuwar halinda take ciki sbd yakasa yarda da lafiyarta kalau…

Abinci ma kasa ci tayi Haka ta wuni cikin damuwa,
Gab da magriba Anne tadawo ta tadda wannan tashin hankalin sbd zazzabin gaske daya sauka ya rufe Laylah Dake dunqule a daki jikinta na rawa.

Fada sosai Anne taringa Yi Akan su halima Basu kirataba sun sanar da ita abun dayake faruwa ta dawo..

Ba Bata lokaci ko zama bataiba ta Kira dr Meenah tace ta taimaka tadawo tasake duba musu laylan.

Koda Dr Meenah ta iso da daddare jikin Laylan yayi tsanani sosai da zazzabin,

Magani aka Bata tareda tea Mara zafi Sosai
Dr Meenah na tafiya ta ringa zuba Amai a gabaice.

Damuwa sosai Anne tashiga ta Kira Turakin a waya ta sanar dashi yace a a shirya Laylan ta fito zasuje suga wani likitan.

Da Taimakon Ruky ta shirya suka fito ta kaita har jikin motar dayake zaune Yana jiranta da kansa zai ja motar Wanda rabonsa da driving bama zai iya tunawaba.

Dr Dawood sukaje ya dubata daqyau harda scanning yayi Mata ya tabbatar musu da lafiyan babyn kalau
Bp dintane kawai ya hau sai zazzabin sosai dayake damunta da rashin qarfin jiki na galabaitan datai.

Maganin bp na masu ciki yabata Suka fito Yana riqeda hannunta Suka dawo gida.

Yanayin da ake cikine kawai yasa yabarta Takoma bangaren Amma yanajin yanayinta a zuciyansa.

A Daren kusan dukkaninsu kowa kwanan damuwa yayi sbd Babu Mai cikakken dadin zuciya..

Washe gari tasamu saukin jikinta sosai saidai gabaki daya tashiga damuwa da sanyin jiki
Babu abunda takeso bayan zuwa gida ko zata samu kwanciyar hankali kafin tadawo idan mum ta sauko sbd tasan mum bazata taba Bari ahaka ba sai tayita kokarin Daukan mataki akanta shiyasa gabaki daya take cikin sanyin jiki da damuwa..

Qarfe goma na safe Anne ta nufa Sashen Na’ima sbd dubota dakuma magana da ita sbd tasan wannan Shirun nata bayan abinda yafaru bana lafiya bane.

Siddika ce ta tarba Annen cikin tsananin girmamawa tareda sanar da ita Ms Na’iman tana bacci magani Tasha sbd ciwon Kan data kwana dashi.

Kallonta Anne tayi cikin jinjina Kai tace”

Idan ta farka kizo ki Sanar Dani Zan dawo na dubata nakuma Yi magana da ita,
Allah ya sawwaqa yabata lafiya.

Amin” Siddika tace tana kokarin bawa Annen Hanya sosai ta wucewa.

Shigowar Haj Zinat yasa Annen dan dakatawa tana kallonta.

Cikin tsananin girmamawa Haj Zinat ta qaraso tana gaida Annen cikeda biyayya tana qarawa da cewa”

Na’iman ta tashi ne?

Aa Bata tashiba ance Bata jima da komawa bacci ba Tasha magani ne,

Cikin nutsuwa da bayyanarda Mahimmancin maganar da zatai da Na’ima idan ta farka Anne tace”

Zinat ki kula da Aminiyar taki sbd nasan halinta da zafi da fitina,
Tabbas akwai rashin kyautawa aciki Amma Kuma yanayin ne duk yazo ahakan sbd Babu Wanda yayi niyar cutatar da ita ko boye Mata komai,
Tun farko itace ta kawowa kanta rashin tsayawa fahimta,..

Turaki Bai boye Mata qarin aurensa ba, nikaina ban boye Mata ba saidai Kuma itace da kanta ta zabarwa kanta waye kishiyar tata
sbd azauna lafiya yasa ba’a sanar Mata ba Dan Babu Wanda ya dauka auren Mai dorewa ne tun farko
Saidai Kuma kaddara da rabo na ubangiji ba’a tsere musu,

Laifi dai anyi Mata na rashin fadar Dan Haka nakeson rarrashinta nabata hakuri duk wannan tashin hankalin zata sakawa kanta damuwane tunda bawa baya wuce qaddararsa….

Laylah Allah yayi dai Matar Turaki ce Kuma uwar yayansa…….. Dan Allah kifara tausarta kafin nadawo
Ki Bata hakuri sosai sbd mum Mata laifi mun yarda Amma Inshallah za’a gyara komai….

Mutuwar tsaye Zinat tayi zuciyarta na neman Faso kirjinta tafado tsabar shiga tashin hankali da rudu
Amma dayake gwanace gurin riqe kanta sai Bata bayyanarba ta jinjina kai kawai sbd bazata iya magana ba bakinta rawa yake.

Anne na fita tayi wurgi da Jakarta da keys din motarta tareda dankwalin kanta tanajin kaman zata Ara hauka akaron farko…..

Wane mugun labari ne wannan takeji abakin Anne?

Kallon siddika tayi cikin tsananin tashin hankali tace”

Daidai naji Anne tace Laylah ce Matar Turaki???

Da sauri siddika ta gyada Kai cikin nata zallan mamakin da firgici Dan sai yanzu take sake tabbarda akwai masifa a kwance kenan idan Ms Na’ima ta tashi ta samu wannan sabon zancen.

Zama Zinat tayi tana fifita fuskarta da hannunta Dan wani zafi taji tanaji
Cikin shiga rudin tunani tace”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button