NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL BY MAMUHGEENOVELS

NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL

NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL BY MAMUHGEE

Rintse idanuwansa dasukai jajir yayi kafin ya miqe ya fita yauma da kansa ya ja mota a irin tuqin da Babu Wanda yataba ganinsa yayi ya Isa gidan Zinat Dake haukace tagama hargitsa gidanta koina bataga gwalagwalan Na’ima ba data ajiye ga siddika batanan ta gudu ga takardun asibitin Na’iman ma sun nata
Siddika ta tattara ta gudu.

Haukace take tanajin kamar zata Kama da wuta sbd sune dukiyar Na’iman datake taqamar zasu zama natan tayi arzki dasu Amma Rana tsaka ace ta rasa wlha bazata yardaba neman siddika zata tafi saita nuna Mata ba’a irin wannan gangancin da ita.

Tsallaka Ms Na’ima Dake kwance a qasa tana bubbuga kanta tayi cikin tsananin Azabar abinda takeji suna Mata yawo cikin Kai
Jin kafar mutum ta tsallakata yasata cafke kafar da sauri tana cewa”

Kece Laylah,
Kece Laylah,
Meyasa kikaci Amanata bayan Ina kaunarki da gaskia…
Meyasa?

Haqori tasa ta cafke qafar da wani irin cizo Mai azabar gske.

Ihu Zinat keyi tana dukan Na’iman da qafarta daya Amma Taki saki qafar ga jini sai fesowa yakeyi Sbd ba qaramin kafa Mata hakoran tayiba suka shiga qafar sosai.

Agogon Kan gefen gadonta ta fizgo da qarfi tareda bugawa Na’iman a Kai take azaba tasakata sakin kafar tana somewa agurin.

A haukace ta fito daga gidan ko gani batayi sbd jinin da kafarta ke fitarwa Sosai ga tashin hankalin da siddika ta sakata a haukace ta fada motarta tana tayarwa motar Jamian tsaro tsayawa gaban motarta Dake kofar gidan.

Wata motarce ta Parker siddika da A Abdoul Suka fito sai alokacin gaban Zinat din yayi mummunan faduwa dan da farko Bata tsororaba tunda tasan Babu wani dalilin zuwan hukuma gurinta Amma ganin siddika tareda A Abdoul ya tabbatar Mata da komai.

Reverse tafara Yi da motarta cikin tsananin gudu sbd batada damar yin gaba tunda agabanta suke tanayin Bata Suka bita da motacinsu a guje

TURAKI daya iso gidan Tuni siddika harta janyo Na’iman Dake sume tamkar Babu Rai tareda ita ya qaraso ya dauketa gabaki daya yakai mota tareda rufewa yashiga yaja motar yabar gurin.

Sosai Zinat ke gudu da motarta cikin reverse sbd tasamu ta tserewa jamian ta hau titi,

Kwana zatasha da mugun speed
Tayoyin Suka qwace Mata motar tayi cikin wata sabuwar transformer Dake street din take kuwa transformern tafara yayyafin wuta suna zuba Kan motar
Hankali tashe tafara kokarin bude motar dukkanin jikinta na rawa tana ihun a taimaketa Azo abude Mata ta fita Amma kowa yakasa qarasawa sbd wuta tafara cin gaban motar tata,

Tana gani tafara sakin ihu tana bubbuga glass din motar,

Dole Jamian tsaron aka fara kokarin cetonta Amma Sam wutar Taki Bari kowa ya matsa sbd transformer na barin wuta motarma naci Dan Haka kowa ma guduwa yafarayi da motarsa Daga gurin ga ihunta da bubbuga glass dinta anaji Ana gani tana konewa da ranta cikin tsananin azaba
Tun Anajin ihunta har aka dainaji Haka Wutar ta cinyeta qurmus kafin akashe a fiddota.

Asibiti aka Kai Ms Na’ima itama sbd yin nasu binciken asalin akan qwaqwalwarta.

Anne da idonta ta ringa tsiyayarwa da Na’ima hawaye sbd tana cikin mawuyacin hali.

Laylah ma kusan sai dataiwa mum din tata kuka sbd tausayi,

Ga Abbanta daya taba hankalinsa uku akansu,
Rabi na Kan baby, rabi nakan mum rabi Kuma Yana kanta sbd itama har lokacin takasa dawowa daidai duk da ta sakawa kanta tawakkali yanzu fatarta abba da Momy su samu lafiya,
Har gwara Momy ta farfado sbd wutarta batai yawan ta abbanba.

A Abdoul ne ya tsaya aka rufe case din Zinat da Na’iman akan rasuwarsu Sa’adah tunnda Zinat din tabisu inda ta aikasu din.

Bincike Mai kyau tsafta ya tabbatarda Ms Na’ima qwaqwalwarta tagama juyewa Amma Basu cire ran dawowarta daidaiba Dan Haka tana Jin sauki aka sallamota gida.

A sasshen Anne take itama wannan karon dakin Sa’adah yakoma nata siddika itace Mai kula da komai nata sbd yanzu komai nata datakeyi kallo daya zakai Mata kasan tana matsalar qwaqwalwa.

Tsananin tausayinta yasa kaunarta Mai girma wanzuwa a zukatansu,

Anne har cikin ranta take Jin Na’iman sbd ba qaramar qaddarar jarabawa bace mace Mai girma kyakkwa ace kanta a juye yakeba,

Siddika Takoma tamkar uwar data haifeta takejin Na’iman sbd duk da tasamu matsalar dukkaninsu suna cikin gata da kwanciyar hankali da kauna daga kowa.

Yanayin matsalar ta me Na’iman sai tazo Mata da qaunar Laylah Babu Wanda takeson zama dashi kokuma yabata maganinta Tasha ba gardama kaman Laylan.
Shi Turaki qarfi da yaji Abbah take cemasa kaman yanda taji Laylan na fada.

An sallamo Baby Sa’adah kaman yanda ta roka Abban ya sakawa babyn Dan haka sai alokacin farin ciki da walwalar gidan tadawo
Abbah ya fidda asalin tsananin kaunar dayakewa ‘yarsa danma baya kwana guri daya dasu.

Dazai koma Babu yanda baiyi da laylanba su kebe taqi sbd Anne da kamar ta saka Mata ido sbd gyaran da ake Mata Wanda Bata samuba na aure
Dan Haka Haka ya lallaba ya koma yaso tafiya da Na’ima sbd asibiti da za’a kaita Amma taqi yarda ta matsa koina idan bada Laylah da baby Sa’adah za’ai tafiyarba
Dole ya kyaleta kafin Laylan ta tashi dawowa saisu dawo tare.

Momy tana samun sauki sosai sbd kullum Laylan na tareda ita a asibitin danma Anne ta Hanata kwana asibitin sbd Kar a daukowa baby Sa’adah sanyi shiyasa iyakacinta wuni kullum tadawo.

Momy tunda tasan Sa’adah ta tafi tabarta Babu Wanda yayi tunanin zatai dangana da karfin zuciya irin Wanda tayi saima kurawa baby Sa’adah Ido datakeyi Koda yaushe tana kallonta amatsayin Sa’adahnta datana jinjira.

Baby Sa’adah nada wata uku Suka Gama zamansu a Nigeria suka tattara suka koma Amma Saida Suka fara zuwa kaduna itama taje tayiwa iyayen Ruky gaisawa bayan su Turaki sunje gurinsu tun farkon al’amarin sun musu baya da duka sauran abun daya kama.

Itama alkhairi tayiwa iyayen Ruky din sosai kafin tabaro.

Sbd samun sassauncin komai na dawainiyar data hau kanta Momy da abbanta da haryanxu baya komai bayan Dan numfashin da shima sai can daqyar yake fita anan wata babbar asibiti Atlanta akai kwantar dasu.

Ms Na’ima ma kwanansu hudu da zuwa yatafi da ita nata asibitin itama sukai admitting dinta akan za’a dorata Kan treatment data fara dawowa daidai za’a sallameta sai aqarasa treatment din a gida.

Cindy tunda Suka dawo itada sofia aka Rasa waye yafi tsananin kaunar baby Sa’adah wadda yanzu kamanninta da Abbanta yake fita sosai sbd farace tas ta dauko farar fatarsa da idanuwansa harma da hancinsa.

Tunda suka dawo sai yanzu tasamu cikakkiyar nutsuwar kanta data gidan sbd yanzu itace Matar gidan.

Masu aikin gidan sunanan kaman yanda suke ada Cindy da Siddika dan Haka yanzu gidan komai anatse cikin kwanciyar hankali musamman batada wata damuwa akansu Momy sbd asibitin akusa take koyaushe ta tashi zuwa takeyi gurin momyn wadda zuwa yanza tana magana saidai komar koyaushe Bata iya kallon Laylan Sosai Amma wannan karon sbd kunyar ne da fargabar fuskar Sa’adahnta datake gani akan fuskar Laylah badan komaiba sai Dan koyaushe burin Sa’adah inganta rayuwar Laylah ne gashinan ta tafi tabarsu daga ita har Laylan basuda kowa yanzu sai juna.

Ita baby Sa’adah kuwa lokaci daya Allah ya dauki tsananin kaunarta Mai qarfi ya jefa a zuciyar momyn saidai Bata iya nunawa sosai sbd gudun zaqewa tunda tasan irin yanda suka taso da Laylan,
Ga Yan uwanta ko a waya Babu Wanda yataba Kira yaji yanayinta shikenan dai ta tabbata batada kowa sai Laylahn sai kuwa Mahmoud idan Allah ya tada kafadunsa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button