NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL BY MAMUHGEENOVELS

NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL

NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL BY MAMUHGEE

Toilet dinta Kai tsaye ya nufa da ita ya duqar da ita gaban wash basin Yana buga bayanta ahankali yace tayi kokari tayi amai.

Kasawa Tai duk yanda taso yin Aman saima sake tokale maqoshinta da qayar keyi jini nasake Dan digowa dan Haka saita qarasa rikicewa gabaki daya.

Ganin hakan saiya Kuma janyo hannunta ya nufi cikin jacuzzi da ita ya sakar Mata shower akanta
Take tasake rikicewa Dan bata wanka a qarqashin shower a tub take wanka sbd tanada tsoron ruwa,,,, qanqame hannunsa Dake riqe da nata Tai tana fizgar Numfashi da qarfi cikin ficewa hayyaci tana kokarin fita showern tayi jikinsa wani irin wahalallen amai na kufto Mata ba shiri….

amai takeyi sosai tana riqe ajikinsa tsawon mintuna saidata galabaita sosai kafin aman ya tsaya sai alokacin ta dago fuskarta da jikinta dake jiqe duka ta kallesa da idanuwanta dasukai laushi taga ita yake kalla cikin yanayi na Kamar tausayawane ko mamakin jiqasa datai da ruwan jikinta Dan gabaki daya qirjinta akan jikinsa yake.

Sauke idanuwanta qasa tayi Ahankali tareda saurin saurin sakin hannunsa cikin tana matsawa baya a hankali
Idanuwanta Kan kayan jikinta dasuka Gama jikewa suka lafe jikinta sosai tareda bayyanarda kalar bra dinta Dake ciki
Tai saurin juyawa jikinta na Dan rawa har batasan lokacinda ya bar gurinba sai Jin rufe kofar toilet din taji.

Yana barin dakin sama ya nufa ya shige Bai tsaya koinaba sai bedroom dinsa gaban maganinsa Dake cikin bedside ya dauka yasha tareda zaunawa Kan sofa ya jinginar da bayansa jikin kujera Yana rufe ido Dan maganin ya fada Masa da wuri yai Masa aiki.

Daga lokacinda yasani yakuma tabbatarda shi din ba lafiyayye bane Bai taba sanin ya tudu ko yanayin kirjin mace yakeba a jikinsa sai yau da hakan ta faru.

Kawar da tunanin abin yayi a kansa gabaki daya tareda sake daukan maganinsa ya qara akan Wanda yasha Amma bayajin daidai Dan Haka Kai tsaye wayarsa ya dauka ya Nemo Numbern DR Allen Sbd wani irin erotism Dake taso Masa Dan dama Dr ya basa umarnin kaucewa body contact da mace Kota Yaya sai yagama Shan sabon maganinsa sbd kaucewa matsalar irresistible desire dazata iya zuwar Masa ta sex da Bai taba having ba.
Ba shiri Dr Allen ya turawa A Abdul sunan maganin dazaije ya siyowa Turakin yakai Masa before things get out of their control.

MAMUH

Follow me at Arewabook @mamuhgee Dan samun complete books Dina dama sauran pages na Noor Albi Dake fara sauka acan.

????????
Eznah
Tarayya
Deen Marshal
Ubayd maleek
Min qalb
Buri daya
Kaunarmu
Noor Albi
Dacewa
Dawood
Zucuyarmu daya
Auren raba gardama
Taura biyu
[7/10, 9:29 PM] +234 704 076 8969: Mamuhgee 21
Jiki amatuqar mace ta tattaro kanta ta fito toilet bayan ta zare kayanta dake jiqe acan ta dauro towel
Tana fitowa a darare ta samo Riga da wando masu kauri na bacci cikin kayanta ta Sanya ta Haye gado Bayan takira Cindy takawo Mata maganin zazzabi dataji yana saukar Mata da koinama ajikinta,
Shigewa Tai cikin bargo tareda to rintse idanuwanta dasukai jajir zuciyarta da jikinta ba Dadi.

Daqyar ta hadiye maganin zazzabin da Cindy takawo Mata sbd radadin da maqoshinta keyi
Tana Gama Shan Takoma takuma shigewa bargo tareda zura hannu ta kashe sidelamp tana rufe idanuwanta da Dan qarfi cikin azaba.

Washe gari da zazzabi Mai qarfi ta tashi Dan Haka ko breakfast Bata iya fitowa shima Kai tsaye yau din Bai tsaya breakfast a gida ba ya fice office Dan Haka breakfast din Haka taqaraci zamansa Kan dining Dole aka daukar Mata Wanda zataci aka Kai Mata daki saidai zazzabinta Mai qarfi ne Dan Haka Bata samu cin komaiba sbd tsananin zafi da ciwon da maqoshinta keyi gashi ya Dan kumbura.

Wuni tayi batareda ta iya cin komaiba sai ruwa datake Sha daqyar
Ahaka dare yazauna cin abinci Wanda Dole Cindy ce tayi serving dinsa Kai tsaye yaci abincinsa batareda ya tambaya Laylan dabai ganiba Yana gamawa ya fice ya Haye sama.

Da dadadden yunwa da azabar ciwo suka taso Mata sosai Haka ta ringa kuka tana juyi cikin mummunan yanayi
Daga qarshe wayarta ta iya dagawa daqyar ta saka Kiran Cindy
Tana dagawa taji kukan Laylan sai hankalinta yayi mummanan tashi ta taso ta nufo dakin Laylan a rude.

Ganinta cikin halinda take yasa Cindy Jin tsoro sbd kukane da Laylan Tasha farar fuskarta tayi jajir hakama fararen idanuwanta sun kumbura gabaki daya dai fuskarta ta sauya gata akwancen takasa tashi sbd sosai maqoshinta ke Mata azabar ciwo ga kumbura da yayi.

Kasa tabata Cindy tayi ta juya da sauri ta nufi main hall ta dauka wayar landline Dake hall din tayi dialling Numbers din dazasu Kai kiranta direct dakin Turaki.

Saida tasake Kira kafin ya daga cikin nutsuwa Kai tsaye furta kalmar “yes”

Cikin sauri da nutsuwa ta sanar dashi halinda Laylan take ciki tunda Ms Na’ima Bata Nan shine kawai zasu iya sanarwa Kai tsaye Dole.

Aje wayar yayi bayan yaji abinda tace tareda miqewa tsaye ya nufi closet ya sauya pyjamas Dake jikinsa zuwa milk jallabiya ya zuro slippers ya fito.

Yana saukowa hanyar dakin nata ya nufa direct Yana Dan sake saka Kiran Dr Noah Bata Shiga kafin ya kashe ya saka Kiran A Abdoul yace yaje yazo da Dr Noah.

Kai tsaye dakin ya bude yashiga sbd sanin Cindy na ciki tareda ita.

Amai tagamo a galabaice Cindy ta taimaka Mata Ta Watson ruwan zafi ta fito daure da brown towel a sulale daqyar tana bin bango sbd rashin qarfin jikin Cindy tabar dakin taje kawo Mata wani tea din Mai zafi,
Kai tsaye bakin gado Takoma tana kokoarin zaunawa aka turo kofar dakin Bata dagoba sbd sanin Cindy ce saigashi qamshunsa ya fallasar Mata da waye a matuqar wahalce ta dago daidai Yana sanyo Kai dakin idanuwansa akanta bai tsammanin samunta ahakanba,

Idanuwansa dasuka sauka Kan fararen cinyoyinta Dake bayyane ya daukesu da Yana dakatawa daga kofar.

Da Dan sauran qarfinta tayi saurin miqewa tsaye har towel din na Dan subucewa daga sama da sauri Takoma cikin toilet tana dafe bango batama Gama ankarewa sbd tsananin rudewa da firgitar datai sai wani Aman Mai karfi yakuma kufce mata tafara kelayawa da qarfin gaske Dan babu komai acikin nata.

Cindy ce data kawo tea din tayi saurin ajewa tana qarasawa cikin toilet din ta nufeta lokacin tuni jikinta yasaki agurin ta zube jikin Cindy gaba daya Bata wani motsi.

Ihu Cindy tasaki tana Kiran sunanta da qarfin gaske cikin rudewa ganin Kamar Laylan Bata numfashi….

Kai tsaye shigowa yayi toilet din ya dauketa gabaki dayanta Yana cewa Cindy ta dauko Mata Kaya ta Sanya Mata.

A gado ya kwantarda ita ya juya ya bar dakin Cindy da duka jikinta ke rawa ta dauko wata doguwar Rigar bacci bataredama tasan abinda takeba ta Sanya Mata tafito ta fada Masa.

Dan shiru yayi Kamar Bai jiba Yana nazarin lafiyarsa idan yakuma hada jikinsa da natan Dan bayan fitowarsa Saida yaje yasha magani ya dawo.

Kallon A Abdoul daya iso Yana jiransa yayi Dan Dr Noah baya gari Dole asibiti za’a kaita.

Dakin yashiga ya daukota da kansa yakaita mota batareda ya lura da kayan da Cindyn tasanya mata Saida Suka Isa asibitin bayan an dauketa anyi ciki da ita A Abdoul ne ya kalli Cindy cikin Dan fada yace”

What was that??

Sauke Kai tayi saboda itama Saida Suka iso asibitin ta lura da abinda tasanyawa Laylan
Cikin damuwa da ban hankuri ta saci kallon inda Turaki ke zaune kamar baisan da tsayuwarsu agurinba murya na rawa tace”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button