NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL BY MAMUHGEENOVELS

NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL

NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL BY MAMUHGEE

Bayan sun Gama cin abincin Kai tsaye kallon Laylah yayi bayan ya miqe yace ta samesa Palo idan tagama.

Kasa hadiye ruwan dake bakinta Tai sbd wata irin fargaba data sameta ta dago ahankali ta kalli Ms Na’ima Dake Mata murmushi tace”

Take it easy Girl ba komai bane zaiji abubuwan dakike buqata ne da Kuma raayinki Akan abinda kikeson karanta.

Kallon Ms Na’ima din tayi tareda bude Baki cikin sanyi da nutsuwa tace”

Me zance?

Wata dariyar Jin Dadi Ms Na’ima tayi ta Jin dadin Laylah tafara zama tafin hannunta akan sai abinda tace.

Ta Kama hannunta suka miqe zuwa gurin Turakin tana cewa”

Daddynki ne kibar Masa zabi da kansa ya zaba miki kawai dai ki dage kiyi karatu sbd akwai yiyuwar rayuwa Mai kyau agaba idan kikai karatu zamuji Dadi Sosai agaba.

Gyada Kai kawai tayi batareda tana fahimtar komai da Ms Na’ima din ke fada ba Dan duk Bata nutsuwarta.

Zaune yake gabaki daya yagama sauya iskar palon da qamshin jikinsa Wanda Babu Wanda zaiyi haduwa biyu zuwa uku dashi batareda ya Gama sanin wannan qamshin nasane na musamman.

Saida suka kawo tsakiyar palon kafin ya dago daga wayar daya keyi ya zuba musu idanuwansa take Laylah ta Dan rage takunta ta danyi bayan Ms Na’ima itama kanta Ms Na’ima din idanuwan Turaki kasheta sukeyi Dan Haka ita qafafuwanta sauri suka qara Kamar ansaka musu batir ta qaraso gefensa ta zauna tanajin a duniya batajin akwai ranar dazata iya barin Turakin ya iya kallon wata macen da sunan so ko makamancin hakanba Dan kila Aron hauka zatai ta halaka koma wace da danginta gabaki daya.

Dauke kallonsa yayi daga kan Laylan wadda duk tabi ta rikice Tama Rasa gurin zama saitayo gurin Ms Na’ima din tana kokarin zama a qasa.

Muryarsa dake sake rudar da ita sbd kamewa da Rabin Wasa ko kadan acikinta ya furta”

Gobe za’a fara fita Dake zuwa harkar makaranta Dan Haka ki ringa kula Nan ba Nigeria bane karkiyi qawayen banza ok??

Bata Gama gane meyace ba kawai dai ta gyada kanta cikin biyayya tareda furta “nagoge” ahankali.

Daga Haka Ms Na’ima ce ta ringa tsarowa Laylan zance da nasiha akan ta dage tayi karatu.
Ita dai Kai kawai take gyadawa Bata iya bude Baki.

Sai kusan goman dare tadawo bedroom dinta ta sauke numfashi tareda Ajiyar zuciya tana zare kayan jikinta ta nufi toilet tayo alwala ta fito ta Sanya kayan bacci Kamar yanda Ms Na’ima ta Gama Bata tsari da yanda zata ringa gudanar da komai.

Face cleanser ta Gama goge fuskarta kafin ta kwanta Wanda shikuma a spa din dasukaje aka karbo Mata shi akace ta ringa shafawa kullum kafin kwanciya shima duk aikin Ms Na’ima ne.

Washe gari qarfe goma A Abdoul yazo ya dauketa a motar Turakin yakaita Emory inda dama tun zuwanta washe gari aka fara process na shigar da ita Dan Haka Koda A Abdoul yakaita har process da payment nata na extra classes anyi komai tareda da daukar Mata wata Sofia Yar asalin nijar da zata ringa koyar da ita wasu abubuwan da Hausa kafin tagama iya turancin da wasu abubuwan.

Dan Haka washe gari tun safe tafara zuwa makaranta
Da farko hankalinta ya tashi sbd kasa Shiga cikin mutane tayi Saida Sofia ta ringa Bata qwarin gwiwa tana nuna Mata zata iya kafin ta Dan daure ta iya Shiga mutane Amma Kam Koda suka tashi akazo daukarta tagama ficewa hayyacinta sbd rashin sabo.

Ko data jera kwanaki tana zuwa makarantar Saida Dole Anne ta hadata da Dr Meenah suka koma communicating ta waya sbd ta ringa magana da Laylan Kota fara sakewa cikin sauran dalibai.

Ahankali ahankali tafara sakewa da makarantar sbd Sofia Dake tayata komai tun daga kan muamala da mutane har karatun da magana da kalolin abincinsu da yanayin muamalantar komai.

Taci wuya matuqa kafin tasake ta Saba da komai shikam karatu duk da tsakanin dagewar datakeyi da maida hankali sbd kullum shine burin Anty Sa’adah dinta akan ta maida hankali hakama Anne Da uwa uba Ms Na’ima da itama take sake cusa Mata cewan Turaki nason tayo kokari ta samu ilimi sosai sai hakan ya shigeta take maida himma duk da sai ahankali da bazai yiyu ace tasamu budewar Kai lokaci daya ba saidai ba laifi turancinta na samun cigaba sosai tunda Babu inda a qasar zakai rayuwa bada yaren turancin ba shiyasa shikam tuni ya Dan fara shigarta sama sama Dan ko Sofia Bata cika Mata Hausa ba da turancin take Mata magana hakama a gida datai Sabo da Cindy Sosai Dole Haka suke turancin Dan Haka kawai tafi Jin nutsuwa da Cindy akan siddika duk da siddikar ma tana jinta ba laifi sbd da ita kawai take zaunawa tayi hausarta yanda tasaba sai kuwa idan tana waya dasu Anne Dan anty Sa’adah ma ba laifi yanzu tuzama Yar gayun Abuja maganarta daya biyu turancine na ukun.

Sun samu hutun farko results dinta ba laifi tunda dai Bata Fadi duka ba Dan Haka a Dan hutun saita dage itada Sofia suna Dan tanason tayi karatun yanzu da gaske.
Ta bangaren zamanta da Ms Na’ima wadda da qarfi da yaji Ms Na’ima tasata tazama ‘yarta Dan Haka Dole mum Na’ima take kiranta Kamar yanda Ms Na’ima din tace ta ringa kiranta,
Batada matsalar komai a gidan saima gata datake samu sosai Dan kuwa kudi sosai mum Na’ima din ke karba hannun Turaki na kullum qaryar siyayyar Laylan na kayan shafa ko kwalliyar kokuma shoes da handbags Dan Haka ba laifi duk ta karba takan yiwa Laylahn siyayya acikin kudin ta riqe sauran.
Sofia ma tanajin dadin qawancen da Laylah sbd sosai take samun designers Kaya a hannun Laylah Dan Laylahn nada kyauta tunda yanzu Allah yakawo sauyi rayuwarta.

Ta bangaren Turakin ne iyakacinta dashi dining room idan za’a ci abinci sai Kuma a kaidarsa duk bayan kwana biyu yakan zauna cikinsu Bayan cin abinci yayi fira da Ms Na’ima Wanda itadai daga yagama tambayarta karatu take sulalewa tabarsu Dan ba laifi ta rage tsoronsa da fargabar haduwa dashi Dan yanzu tagama daukarsa matsayi daya da abbanta tunda Anne tayi Mata bayanin irin kusanci da qaunar Dake tsakaninsu tareda kusancinsa da mahaifiyarta sai wani irin girmansa qaunasa irin ta shiqiqinka Mai girma tashigeta tana Masa kallon uba,Mariqi Kuma mijin yayarta ‘yar uwarta datakewa kallon uwa ta wani bangaren.
Bismillahi fa yanzu zamu Shiga labarin.

MAMUH

Follow me at Arewabook @mamuhgee Dan samun complete books Dina dama sauran pages na Noor Albi Dake fara sauka acan.

????????
Eznah
Tarayya
Deen Marshal
Ubayd maleek
Min qalb
Buri daya
Kaunarmu
Noor Albi
Dacewa
Dawood
Zucuyarmu daya
Auren raba gardama
Taura biyu
[7/10, 9:29 PM] +234 704 076 8969: Mamuhgee 20

Sungama session dan haka hutun dasukai Mai Dan kwanaki ne taso zuwa Nigeria Amma Mss Na’imah tace sai Ankara Gama wani session dinn
Anne ma ce Mata tayi ta zauna har gaban Dan Haka Dole ta hakura Amma taso tsananin ganin Anty Sa’adah wadda yanzu iyakacinsu vidcall Wanda kusan kullum awuni sai sunyisa yafi so biyu sbd yanzu Kam saidai raunin wani ilimin Kuma Amma wayewa da zama babbar yarinya Laylah tajima dakaiwa saidai nutsuwarta da sanyinta na Nan sai suka qarawa yanayin nata burgewa sbd sai yanayi kamar ajine da yayi Mata yawa,
Ta bangaren addini ma na laifi suna attending Islamic class a wata private school duk weekends itada Sofia Wanda ma sai daga baya da kansu suka gano gurin taiwa mum Na’ima mgnar aka sanyasu suka fara zuwa dakansu Dan ba laifi yanzu tana Jan mota sosai Dan musamman Turaki ya siya Mata motarta fara Sol kirar infinity QX50 wadda taqarasa sauya rayuwarta gabaki daya
Ga qananun kayan tuni tayi sabo da sanyasu tunda babu wasu kayan idan basuba,
Hakama ta bangaren ‘yan matanci Sofia ta Bata sosai dason kwalliya saidai dayake Bata Saba ba sai son jambaki kawai yashigeta Dan Haka duk wasu kamfanin lipsticks masu tsada ba kalar da batada Dan koyaushe kwalliyarta Bata wuce lipstick da mascara sai eyeliner duk da Bata cika sanyataba Dan idanuwanta sunfi Mata kyau ahakan gashi tayi haske sosai idan ta Sanya liner cikin idon sai tayi Kamar zata gurin wata biki ko taro shiyasa Bata cika sakawarba saidai lipstick da idan ya zauna bakinta yake qara Mata kyau da burgewa sosai.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button