NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL BY MAMUHGEENOVELS

NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL

NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL BY MAMUHGEE

Rayuwar Laylah rayuwace Mai cikeda zallan kadaici da maraici,
Tunda tafara wayo taga yanda Momy Bata taba kallontaba bare amsa ko gaisuwarta Amma Kuma Bata taba hantarartaba saita taso cikin juriya da rungumar rayuwar ahakan tareda yarda da cewa tabbas itace sakamakon cin Amana da haincin da akaiwa Momy Wanda ya rusa rayuwarta da kwanciyar hankalinta na gidan aurenta Dan kuwa tun lokacin Momy ta Rasa miji tunda yakoma baida wani amfani agareta da yarta tun daga kan auratayya har Kan sauran haqqoqin.,

Da wannan zuciyarta take kasa Jin ‘dacin Momy sbd takowane sashe tabbas itace mummanar qaddarar data Bata rayuwarsu shiyasa ta sadaukar da kanta da rayuwarta gurin bautawa Momy da anty Sa’adah ko zata iya biyansu ta wani sashen da abinda abbanta da mahaifiyarta da Bata Raye sukai musu,
A rayuwarta cinta da Shanta tareda karatunta momynce ta dauka nauyi abisaga aikin wahalar datake musu tun bayan data girma aka sallami Mai aikin data raineta harta girma ragamar aikin gidan tadawo hannunta tun daga kan girki da tsaftar gidan,

Sam rayuwar Momy a baude take wanzuwar laylah a rayuwarta sbd tuni ta Rasa annashuwa da dariyarta harma da murmushinta,
Rayuwarta Takoma ta wata irin cunkusashiya kasancewarta cikin mutane masu tsananin riqo a zuciya shiyasa duk tsawon shekarun Bata tabajin sassaucin abunda takejiba akan al’amarin.

Babban abunda yake tattareda rayuwar Layla na nutsuwa da kwanciyar hankali shine tsananin kauna da soyayyar da mahaifinta ke Mata Mai tsanani da wadda ‘yar uwarta Anty Sa’adah ke Mata Dan kuwa anty Sa’adah itace gatanta a fili da boye sbd itace ta tsaya Kai da qafa agurin mahaifiyarta ta roqu alfarmar bawa laylan damar karatu bisaga neman alfarmar zata karba ragamar aikin gidan,
Da wannan Laylah tasamu tayi karatu a makarantar gwamnati Mai dama dama harta samu ilimin bokon datake dashi sabanin ita Sa’adah datai karatun private school Mai kyau,

Anty Sa’adah ce gatanta a duk abinda ya danganci haqqin dake rataye akan iyayenta na kula da ita shiyasa koyaushe Abba ya bude idanuwansa akan Sa’adah yake Mata godiya cikin ganin qimarta itada momyn sbd koma yayane da dukiyar momyn Sa’adah ke yiwa Laylah hidima Wanda itama momyn rufin asirine kawai na ‘yar kasuwancin buga buga datake Dan tallatawa rayuwar yarta da abban da yarsa dasuka zamar Mata wani babban jarabawan rayuwa.

Mahaifiyarta ta rasu tabarta a ranarda ta haifeta Dan Haka batasan wani shaquwaba ko sake tayi Wasa tareda wani,
Mahaifintane Kuma kwance ta bude ido tagansa,
Anty Sa’adah Kuma kallon wadda ke tallafe da rayuwarta take Mata duk da a zuciyarta matsayi da girman kaunar datakewa anty Sa’adahn daban ne.

MAMUH

NOOR ALBI
Rabo sai Mai shi…Bata taba saka ran shigowarsa ko zama jigo a rayuwarta ba sbd kallon datake Masa amatsayin Uba,Abokin mahaifinta,Amininsa Kuma Mariqi.!
Soyayyace tashiga tsakaninsu Mai girma da qarfi batareda sun ankare da hakanba bayan dukkaninsu sun haramtawa kansu hakan,Shin ta yaya zata kalla mijin yayarta,Yar uwarta wadda ta riqeta tamkar yanda uwa me riqon ‘da amatsayin nata mijin?
Qaddararsu wannan kokuwa itace rabonsa tun farko?
NOOR ALBI Hasken rayuwata
Littafina dayazo muku da wani salon na dabam Wanda soyayyarsa ta kere sauran labaraina,salonsa ya bambanta da sauran,nishadinsa da shauqinsa na musamman ne
Fata dai ku kasance taredamu kuji zafi zafin damuka dawo muku dashi
NoorAlbi#MAMUH

FOLLOW ME@
Mamuhgee
Wattpad
ArewaBooke@
Mamuhgee

ZAFAFA BIYAR

KUFAN WUTA
Safiyya Huguma

BAQAR INUWA
Billyn Abdul

RAYUWAR MACE
Hafsat Rano

MASARAUTA
Miss Xoxo

NOOR ALBI
Mamuhgee

Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank

Number shaidar biya????????

09032345899

KATIN MTN

09166221261
[7/10, 9:09 PM] +234 704 076 8969: NOOR ALBI
Mamuhgee

3
Tana zaune tsakar gidan tsaye bakin kicin tana wanke hannu a fanfo Dr Abbakar yafito ya fice Tai Masa asauka lfya cikin biyayyarta
Ya amsa Mata cikin kulawa shima ya fice.
Qarasa wanke hannayenta tayi sbd miyar abincin da anty Sa’adah ta zubar a Palo batareda sani ba tagama kashewa shine take wanke hannun,
Kofar palon abban ta nufa Kai tsaye tashiga da sallama
Har lokacin Yana yanda Dr Abbakar yafita yabarsa cikin zurfin tunanin abinda ke addabar zuciyarsa da shawarar dayake nanatawa kansa akan ya yanke Dan inganta rayuwar yarsa ko baya Raye ko Yana raye
Tabbas idan tana qarqashin inuwar Amininsa Kuma Aminin mahaifiyarta zata samu gata da kulawa tareda samun Amintacciyar rayuwar kwanciyar hankali.

Kai tsaye gurinda flask din abincinsa yake ta nufa tafara daukan flask din ta bude wani tiririn zafi da qamshin kunun alkama da gyada ya ringa fitowa daga ciki
Ta dauki dauki cup daya cikin cups din Dake gurin wainda aka Ware musu aka Bata na Abban
Ta tsiyaya kunun Mai Dan yawa aciki kafin ta maida sauran ta rufe ta dauki kofin ta baro gurin bayan ta jefa cokali aciki tana juyawa ahankali ahankali Dan ya huce ta nufi gurin Abban tana kallon yanayinsa da a fili qarara yake nuna yayi nisa a tunani.

Aje kofin tayi tafara tura kujerarsa zuwa bakin windo bayan tasake yaye musu labule sbd iska Dan yanzu tana basa kunun zufa zai taso Masa.

Janyo tata kujerar tayi ta zauna gabansa tareda aje tissue gefensu ta dago fararen idanuwanta ta kallesa cikin kulawa shima ita yake kallo
Ahankali tasaki wani irin murmushin dayasa Abban rufe idanuwansa ahankali sbd murmushinta bakomai yake bayyanawa ba sai zallar tausayinta.

Saida ta tabbatarda ya huce ba zafi kunun ta dauka tafara basa ahankali da spoon ta nufa bakinsa,

Sam bayajin yunwar Shan komai ayanzu sbd damuwar dayake cikinta sosai,
Jin inda lafiyarsa ta dosa ya wargaza duk wani Dan sauran qwarin gwiwarsa da dukkanin jarumtarsa
Tunaninsa ‘daya yanzu yanda zai Fadawa TURAKI buqatarsa Dan kuwa wannan babban abune Mai girma zai roqa agurinsa duk da girman banbanci masu tarin yawa dasuke cike a tsakani.

Sbd kawar da sabuwar damuwar da hanata shiga wani sabon halin yasa hakanan take basa abincin Yana sha tanayi tana goge Masa da tissue
ahaka yakesha har sukai nisa yakusa shanyewa.

Cikin nutsuwa ta Dan kallesa kafin ta bude Baki kamar ko yaushe da taqaitaccen sauti tace”

Koma menene sakamakon asibitinka
Bana cire Rai ga falalan ubangiji akan samun sauki da lafiyarka.
Karka saka sabuwan damuwa
Ko ahakan Ina godiya ga ubangiji daya bani ikon tasowa nayi rayi rayuwa da mahaifina.

Kallonta yake da idanuwansa dasuke jajir har lokacin zuciyarsa na sake zurfafa da tunani.

Tas tagama basa kunun ta dauko maganinsa shima tabasa kafin ta goge Masa ta dauko wani Dan turarensa da baya yanke musu Abdullahi ke siyowa ta ‘dan fesa Masa kadan sbd abdullahi din yamasa wanka kafin zuwan dr Abbakar
Tana gamawa ta fice Dan yau tana Dan da ayyuka
Ga wankin Momy ma ta Tara gwara na anty Sa’adah ta rage Mata jiya tayi abunta da kanta.

Harta fita Jin zafi a garin yasa tadawo ta turo kujerarsa ta fito dashi tsakar gidan Dan Tasha iska musamman dayake yamma tafarayi ba rana.

Wankin kayan Momy tafara a natse sai kayan anty Sa’adah kadan Wanda anty Sa’adah din Bata qarasa ba jiyan tana cikin Yi anty Sa’adah ta fito ta zaune gefen Abban daukeda takardunta na makarantar jami’a datakeyi tana karatu Dan tanada test a satin.

Sama sama take karatun tanayi tana Jan laylan da surutu duk da tasaba Laylah ba wani surutun zataiba musamman ma datake aiki Amma dai Haka sukeyin surutun sama sama tana yiwa Laylan bayanin wasu abubuwan dake cikin handout dinta tunda ita Layla Bata karatu tunda tagama secondary School last year shikenan iya inda nata karatun zai tsay kenan Kuma
Dan Momy tariga tafadawa Sa’adah da Abban hakan,
Bazata iya qarawa daga Nan
Tayi iya abinda taji zata iya
Idan akwai Wanda zai iya daukan karantun nata acikinsu biyun bismillarsu zasu iya dorawa daga Nan,
Shi dai Abba yasan baqar maganace tafada Masa Amma ko ahakan ya gode Mata Dan Koda laylan makarantar datai ta gwamnati ce yaga alamar tasamu ilimin Dan Haka shi ahakanma ya gode matuqa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button