NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL BY MAMUHGEENOVELS

NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL

NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL BY MAMUHGEE

Washe gari suna dawowa daga karatunsu Suka sake bajewa sukaci ciye ciyen Aunt siya
Anan dai suka wuni suna Abu daya sai dare tayi wanka ta kwanta Bayan tagama waya da Anty Sa’adah dake sanar da ita wani labarin na yawan kiran da A Abdoul ke Mata yanzu.

washe gari dayake batada Kaya a gidan yanzu Dole tayi shirin komawa gida Dan Haka daga school Bata dawo gidanba gidanta ta wuce suka rabu da Sofia akan zataje gida ta hado Yan kayanta kadan tadawo anan zatai Mata weekend.

Tana dawowa gidan dayake Rosalie tasan Bata Nan kwana biyu Bata zo ba da kanta ta gyara gidan koina yayi fes yadauki qamshi da sanyin Air-con
Dayake har bedroom dinsa ta gyara dukda bayanan takuma Yi mamakin Jin dakin bude tunda tasan duk zamanta gidan kafin yafara zuwa dakin rufe yake,so yanzu dinma batai tunanin samun dakin a abudeba
Haka ta gyara dakin da komai na cikinsa yake white sai wasu abubuwan dasuke golden ta fito Takoma dakinta ta tube tayo wanka,
Tana fitowa ta Sanya wata qaramar singlet Mai Dan tsayi zuwa cinyoyinta ta daure kanta tafito qamshin body mist na tashi ajikinta kadan kadan ta nufi kitchen ta debo mango juice a fridge tanasha Dan batajin yunwa sbd Kafin tayi aikin saidataci noodles data dafa.

Ahankali qamshin da Bata kuskuren shaqarsa yashiga hancinta ta aje cup din hannunta zata waiwayo da sauri sai taji an rungumota ta bayanta Tareda zuro hannayensa ahankali zuwa cikinta dake shafe.

Take dukkaninsu suka saki Ajiyar zuciya, tata a bayyane tasa a sirrance,

Sun Dan Yi mintuna a hakan kafin ya saketa Yana juyowa da ita Suka fuskanci juna mayun idanuwansa akanta Yanawa rigar jikinta wani irin kallo daya sanyata bude Baki a hankali tana neman rikicewa tace”

Sannu da zuwa….

Cup din data aje ya kalla kafin ya bude Baki ahankali yace”

Na sameki lafiya??
Ja jikinki?

Cup din juice daya dauka take kalla tana amsawa a natse,
Ganin ya nufi bakinsa da cup din tayi saurin riqewa batareda Tama San tamayi hakan ba da sauti Mai sanyi tace”

Zan zuba maka a cup Mai kyau…

Akaro na farko daya sakar Mata wani irin qayataccen murmushin daya kusan rabata da bugun zuciyarta na seconds ta ware dukkanin idanuwanta Kan bakinsa Dake murmushi tana kallo ya daga Tumblr din ya shanye juice din duka ya aje tareda janyota jikinsa yayi kissing lips dinta Kai tsaye kafin ya sake kallonta yace”

Me Mike kallo?

Dauke Kai tayi da sauri tana kokarin Hana murmushinta bayyana saidai yariga yaga saukan murmushin a fuskarta hakan ya kashesa Bai tsaya komaiba yakuma janyo fuskarta ya hade bakinsa da nata wannan karon wani irin deep French kiss Suka fara Dan kuwa Yana jefe Mata bakinsa ta Kama batareda tasan tana hakan ba.

MAMUH

[7/10, 9:35 PM] +234 704 076 8969: Mamuhgee 30
Daukarta yayi cak ya bakinsu na hade ya nufi Palo da ita ya zaunar Kan dining suna cigaba da wani irin kiss
Hannayent na sakale da wuyansa
Nasa hannuwan Kuma suna Kan singlet dinta daya fincike batareda Bata lokaciba yabarta da white lace padded push up bra data Kuma daukan hankalinsa tareda yamutsa kansa gabaki daya,
Ya shafo wuyanta tareda saukar Mata da wasu kisses ajere dasuka sata dauke numfashi tana bude idanuwanta daqyar ta kallesa…

Qwayar idanuwanta suka sake haukatar da hakurin dayake kokarin bawa kansa ya barta
Ya Kuma kamo fuskarta Yana cusa kansa cikin wuyanta ya shaqa qamshinta dayafi komai barazana ga hakurinsa koda yaushe…
Wata irin yamutsa yake mata Yana kokarin zare bra dinta kawai sukaji Ana kokarin bude kofar palon da sauri ta dago jajayen idanuwanta ta kalla kofar tana Shirin zame jikinta yaqi sakinta saima daukanta da yayi bayan yagama wurgi da bra dinta palon suka nufi dakinsa Yana rufo kofar da qafafunsa Sofia na shigowa palon Kuma idanuwanta akan bra din laylan yafara sauka Dan taji lokacinda kofar dakinsa ta rufe
Da sauri ta qarasa gurin bra din ta kalla tana kallon koina a palon fuskarta daukeda murmushi dakuma fargaba ta qarasa gurinda akai jifa da singlet din ta Layla takuma sake murmushin farin ciki tareda miqewa da sauri Takoma ta fice tareda rufe kofar Dan dama abinda yasa ta iya shigowama tasan pins na bude kofar ne.

Acikin bedroom din Sir Turaki kuwa komai yadauka zafi Dan kuwa wani irin hot romance yake Bata daya kusa zauta qaramar qwaqwalwarta musamman kisses dinsa dake sauka koina jikinta…

Tun tana iya daurewa Dole ta fara janyewa tana hawaye harda rokonsa wannan karon akan yabarta Dan haryanzu saitajin kamar lokacin farko daya fara zuwa gareta Dan Haka ko ayau din ba qaramar gurzuwa tayi a hannunsa shiyasa da kansa yayi Mata wanka yakaita har daki ta saka wasu kayan baccin yakuma daukota ya dawo da ita ya kwantar a dakinsa
Tana kwantawa kuwa sai bacci.

Washe gari ko data farka baya gadon Yana zaune Kan sofa Yana amsa waya a natse Kamar ba wayar yakeyiba
Tashinta zaune yasashi maida fararen idanuwansa Dake wani sheqi akanta gabaki daya harma da hankalinsa duk ya koma kanta Amma dai Bai daina wayarba.

Yaye lallausan duvet cover Dake jikinta tayi tareda zuro qafafuwanta qasa ta miqe tsaye gashin kanta dake daure ya Dan yamutse ta kalli irin kallon dayakewa rigar baccin jikinta da batada tsayi ko kadan duk da Mai kauri ce Amma fararen siraran cinyoyinta dake bayyane sunfi komai Jan hankalinsa Yana kallo ta shige toilet batareda tayi magana ba ganin Yana amsa waya musamman da kamar ta lura da mum Na’ima ce Amma Bata tabbarba.

Brush sabo ta fasa a toilet din tayo brush dayake sunyi sallah da asuba tana fitowa ahankali ta furta”

Good morning Abba” da sauti Mara fita.

Hannu ya miqa Mata alamar ta Kama tazo
Ba musu Kamar wata baby ta qarasa gabansa batareda ta Kama hannunba
Ya zaunar da ita Kan cinyarsa tareda kallon kirjinta daya hadu da nasa kirjin ya lumshe ido a natse Yana cigaba da wayar…

Jin wayar na neman gagararsa yasashi sakinta ta miqe ta fita.

Kai tsaye kitchen ta nufa tafara kokarin hada breakfast.

French toast tayi sai fries da green tea sai cereals da Madara datafi so.

Tana gamawa bedroom dinta ta nufa tayo wanka ta fito ta duba kayanta suka Babu masu irin girman Nan dazaisa yau dai tayi shigar matan aure a gida,
Kayanta duka qananun kayane
Gashi ko kananun kayan mum Na’ima ta sabar Mata da Sanya irin kayan da yawanci celebrities ke sawa sbd koyaushe cikin gayun tsadaddun designers Kaya take.

Doguwar chiffon half gown tasaka kalar red Mai fadin wuya ta wuce cinyarta ta sauka zuwa gwiwanta kadan sai qaramin red silky scarf data daura akanta ta fito tana waya da Sofia Dake sanar da ita tazo jiyan Amma dai….

Bata qarasaba tahau dariya tana cewa”

Sai bayan weekends dai zamu hadu Mrs Abba Turaki.

Kashe wayarta tayi ta qarasa palon tana kokarin tattara kayansu Dake yashe palon na jiyan sai yanzu ta lura dashi tana kokarin kaiwa daki ta fito daka bedroom dinsa sanye cikin black
Calvin Klein set dasuka fidda haskensa Sosai ya da Kuma nutsuwarsa da kamewarsa.

Kayan hannunta ya kalla tareda qasarowa fuskarsa na bayyanarda sanyayyan murmushin dabai fito duka ba yace”

Can I have my breakfast now??

Waiwayowa tayi tabi bayansa daya nufa dining da kallo fuskarta daukeda murmushi kafin ta aje kayan hannunta da sauri tabi bayansa tana kallon qafafuwansa dakeda haske sosai cikin black Gucci slippers.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button