NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL BY MAMUHGEENOVELS

NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL

NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL BY MAMUHGEE

Ko mintuna uku baaiba saiga Cindyn da dan saurinta tana ganin halinda Laylan ke ciki ta tsaya kanta tana kamata cikin tsananin kulawa da tausayi tana tambayarta lafiyarta kuwa?
Bata iya ko daga hannunta Dan Haka sai kukanta ya tsananta tana sake rintse idanuwanta dasukai jajir.

Ganin hakan ya daga hankalin Cindy sosai taje da sauri ta hado ruwa da towel tana gogewa Laylan jiki sbd batasan wa zata kiraba acikin tsakar Daren Dan kuwa ko hauka bazata sakata zuwa saman sir Turaki ba kiransa ga Ms Na’ima Bata nan Dan Haka taringa goge Mata jikinta Batareda Tama lurada rigar jikin Laylan ba…

Tana kokarin baro dakin taje ta sanar da siddika tazo ta tayata kada ‘yar Mutane ta mutu a hannunta ita kadai bayan ta fito dakinsu saitaji doorbell na tashi ahankali ta kalli hanyar zuwa kofar gabanta na faduwa da karfi
Ta juya ta kalli makeken agogon dake palon taga lokaci sai kawai ta juya zata nufi hanyar komawa daki wayarta Dake hannunta tayi haske tana vibrating da sauri ta daga ta duba ganin sunan A Abdoul yasata dauka da wuri har jikinta na rawa.

Kai tsaye yace ta bude Masa kofar shigowa ya kashe wayar.

Da sauri takuma juyawa ta dawo ta nufi kofar ta tana zuwa ta bude ganinsa tareda Dr Noah da wata nurse yasata matsawa tabasu hanya Suka shigo
Ya kalleta kafin ya kalli siddika data fito itama tana kallon kowa cikin tsoron menene yake faruwa yace”

Ki shiga dasu gurin Ms Laylah.

Juyawa tayi suka bita
Ya maida kallonsa kan Cindy Yana magana da ita Dan tunaninsa yagama basa abinda yafaru Dan Haka ya sanar da ita zata kulada Laylahn sosai batareda ya sanar da ita abinda yake damun Laylan ba.

Sosai Dr Noah ya duba manyan raunikan da Laylah tasamu yayi Mata treating dinsu tareda taimakon nurse dinsa kafin yayi Mata allura yabar nurse din zata kwana anan harsai da safen idan Laylah tasamu kanta.

Allurar da Dr Noah yayi Mata yasa ciwon datake ji suna Dan raguwa sai jikinta yaqarasa sakewa ta lumshe idanuwa bacci ahankali ya dauketa a wahale.

Guestroom aka Kai nurse din suka barta tunda tasamu bacci tareda kashe wuta da rage Mata AC.

Bata farkaba sai qarfe Takwas na safe ta bude jajayen idanuwanta tareda motsawa kadan tana kallon dakin dake qamshi alamar har Cindy tashigo tayi gyaransa.
Ahankali ta dafa ta tashi zaune tareda zuro qafafuwanta qasa ta miqe tsaye tafara takawa ahankali ta shige toilet tana shiga ta shige ruwan zafi sai alokacin ta Dan saki numfashi tana rintse ido tareda Hana kokarin Hana kanta tuna komai Dan kuwa tsautsayi ne kawai zata iyace ya gifta Wanda har abada bazasu tunawa,
Bazata Bari zuciyarta ko gangar jikinta ta tuna komaiba game da wannan Kota halin Yaya…..

Hawayen datake riqewane suka balle Mata takasa riqe kukanta tasake kukan tana qanqame jikinta Dake amsa radadin duk wani cakuda da kisses dinsa dake yawo jikinta.

Ta Jima a toilet saidatayi kukanda Babu Mai rarrashi ko Wanda zata iya fadawa wannan qaddararren tsautsayin kafin ta fito idanuwanta da fuskarta a matuqar kumbure ga wani ja datai na kukan.
Towel ne ajikinta ta fito kanta na tsayayyar ruwa
Lafiyayyar fararta sai sheqi takeyi kanta a qasa yake jikinta amace ta nufi bakin gadonta zata zauna ta huta sbd gajiya da rashin qarfin jiki…..

Qamshin daya doki hancintane lokacinda takai tsakiyar dakin yasata dagowa ahankali jikinta na sake mutuwa ta kalli inda take jiyo qamshin idanuwanta na sake fidda tsananin mutuwar jikin datake ciki….

Tsaye yake sanye cikin farar jallabiyar data bayyanarda wani Hasken daya qara Wanda ke bayyanarda bayajin dadin shima Amma ba’a wani ganewa, sauraron nurse da zata tafi yagama Yi kafin ya dago oily eyes dinsa da har lokacin Basu Gama dawowa daidaiba yayi Mata kallo daya ya dauke idanuwansa Yana juyawa ya fice Dan ganin yanayinta na rashin kaya sbd towel din jikinta qarantarsa Tayi yawa gashi rashin qarfin jikinta yasa takasa dauresa dakyar riqe kawai take dashi saman saman kirjinta Yana Dan bayyana.

Jiki mace ta iya saka Riga Mara tsayi Takoma tasanya jallabiya tayi sallah a zaune kafin ta lallaba ta koma gado tana kokarin kwantawa aka shigo Mata da breakfast batada apatite Amma Sbd magani da zatasha Dole Tasha tea da kidney sauce Mai kwai aciki Tasha maganin Takoma ta kwanta wani baccin yakuma daukanta.

Sai yamma ta farka lokacin zazzabinta ya Dan rage Amma dai tana Jin pains kadan kadan ajikinta Dan Haka takuma komawa tasakarwa kanta ruwan zafi.
Wayarta a kashe ta wuni Kuma Bata kunnaba Saida takwana biyu zuwa Lokacin taji sauki ba laifi tana iya fitowa daga bedroom dinta Amma iyakacinta kitchen kokuma qaramin palo wadda bazata hadu da Wanda batason haduwar dashiba.

Kwana biyu tasake samun sauki sosai suka koma school Dan Haka ta fara fita school ta rage zama gida Sosai sbd mum Na’ima Bata dawoba har lokacin,
Abin daya faru tsakaninta da Abban ta dannewa zuciyarta ta Hana kanta tunawa sbd ta dauka hakan babbar qaddara wadda tariga ta faru tunata kamar tunawa kanta kuskuren dayariga ya faru ne Dan Haka ta danne ta talastawa kanta Yi kamar Bata tana sanin wani abin makamancin hakan ya faruba ta saka kanta zama busy Sosai a karatu
Danma kada ta bar duk wani tunanin dazai tunatar da al’amarin saita sake sosai tana yin rayuwarta Kamar koyaushe acikinsu Cindy.

Sai Bayan sati biyu Mum Na’ima ta dawo gidan lokacin Bata Nan tana dawowa school taganta wani irin Abu taji Yana bugawa a zuciyarta na tsananin kunyar Mum Na’ima din Mai tsananin qarfi da baqin cikin kanta Dan kuwa sai tanajin kamar ta zama babbar butulu saidai tayi alqawarin qin saka zancen wannan al’amarin cikin kanta Dan Haka ta qaraso da murmushi a Kan fuskarta da murnar ganin mum din ta rungumeta kamar yanda ta ware Mata hannu tana cewa”

I’m back princess.

Murmushi tayi Mai sauti tana cewa”

We miss you mum.

Dariya Mai sauti Ms Na’ima tayi ta farin ciki Dan kuwa da farin ciki ta dawo sbd abinda sukaje Yi sunyi komai cikin Jin Dadi yanda sukeso na kasuwancinsu tace”

Nayi kewarki sosai My baby keda Abbanki gashi nadawo shima bayanan tun last week Yana Nigeria yatafi.

Dan murmushi tayi tana cewa”

Mum lemme go and freshen up, I’m morethan tired.

Bedroom dinta ta Isa ta tube tafada toilet tayo wanka ta fito ta shirya cikin qaramar Riga mara nauyi da skirt tayi sallah ta fito ta nufi kitchen ta hado Krispies tafito tanaci ta zauna tareda mum din daketa Mata labarin boutiques da sabbin shagunanta da za’ai launching.

Da daddare tare sukaci abinci a dining Kamar yanda aka Saba tunda mum din tadawo Kuma qarin samun nutsuwarta a dining din daga ita sai mum din Dan Haka har fira sukai sai 10 ta shige tayi wanka ta kwanta.

Da anty Sa’adah sukai waya wadda take fama da Dan rashin lafiya kwanakin Amma dai tasan bazai wuce stress na karantun datake Shirin kammalawaba,
Tunda wannan abun yafaru da ita Bata iya waya da Anne sbd wani irin nauyi Mai girman gaske takeji duk da tasan har abada Babu Wanda zaisan hakan ya faru Amma ta kasa Hana kanta Jin tsananin nauyin Annen,
Annen da kanta take kiranta Amma hakanan sai Bata wani Gane Kan Laylan sbd yanda take magana cikin rashin sakewa bayan suna murnar lafiyarta data Dade da samuwa saidai Bata damuba sbd tasan bazai wuce yanayin jiganiyar karatuba itama.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button