NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL BY MAMUHGEENOVELS

NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL

NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL BY MAMUHGEE

Pancakes din sukaci suka kwanta Banda Anne da Dole akai Mata abinci kala biyu a Daren.

Washe gari ma yawo sosai sukai tareda Sofia Saida sukai kwana hudu suna fita kafin aka fara Shirin tafiyarsu dubo Abba harda ita murna gurinta da farin ciki Kamar me.

Ms Na’ima ba wani dogon zance tace aje da Laylan sbd a matse takeda su Annen su koma Dan Haka taje su tafi.

A Abdoul ne yayi musu komai na tafiyar a waya duk da baya gari suna Vegas tareda Turaki
Kai tsaye tareda Ms Na’ima aka siya tickets na tafiyar abisaga umarnin Turaki Amma taqi zuwa Dan Bata buqatan hada Hanya da duk inda Sa’adah take Dan zuciyarta ingiza take Dan Haka ta sharewarta taqi zuwa suka tafiyarsu.

Koda suka Isa LA jikin Laylah sanyi yayi sbd farin cikin yau zataga abbanta datai shekaru Bata ganiba…

A gidan Turakin Dake LA suka sauka duk da ba babbane sosai ba gidan zamansane shi kadai idan aiki ya kawosa Dan duka idan aka cire bedroom dinsa sauran dakuna biyu a agidan da makeken sitting room Dan gidan tsarin hutawane kawai.

Dayake Yana gari Dole a daki daya da ita da Anty Sa’adah suka sauka Anne Kuma a daki daya.

Baccin gajiya sukai kafin dasuka tashi sukai wanka sukaci abincinda cook yazo ya dafa musu sukai Shirin zuwa asibitin.

A Abdoul ne yazo da wata farar Audi8 ya daukesu zuwa asibiti Dan Turaki na gurin wani conference.

Sanye take da Riga da skirt na atampar Holland datai masifar Yi Mata kyau Wanda tuni ta manta rabonta dasu Dan Bata taba samun sakonsu ba tunda Babu Mai zuwa daga gida hakama itama batada Mai zuwan yanzun ma na Anty Sa’adah ce Kamar tasani taxo Mata dasu Dan idan zasu ganin Abba ta Sanya sbd koyaushe sukai video call taga qananun kayane jikin Laylan.

Batazo Mata da mayafi ba Dan Haka siririn qaramin gyaran Abayar rigar Anty Sa’adah ne a jikinta sai handbag dinta ta Lv da takarmin Versace Dake qafarta wedges.

Sa’adah ma lace ne ajikinta Riga da skirt daya fidda shape dinta dakyau saidai transparent gyalenta ya rufeta
Sai qamshin khumrahs din Amaryar kb masu dadin gaske Dake tashi jikinta.

A Abdoul ne yakaisu har kofar dakin Abban yakoma gefe ya bawa Anne Hanya tafara shiga kafin Sa’adah tabi bayanta sai Laylan daga baya wadda zuciyarta keta harbawa da qaguwar son ganin Abbanta.

Momy dake zaune tana amsa waya shigowarta kenan daga gidan da Turakin ya Kama Mata tana zama Sosai tashiga mamaki da farin cikin ganin Sa’adah Dan batama lura da Laylah dake bayanta ba sai daga baya…

Wani irin bugu zuciyarsu tayi dasukaga juna daga momyn har Laylan tayi saurin sauke kallonta daga Momy a matuqar ladapce da bayyanarda girman momyn agunta tace”

Momy Ina wuni?
Ya gida?

Akaron farko da momyn ta bude Baki ta Amsa gaisuwarta batareda takuma kallonta ba saita maida hankalinta Kan Anne suna gaisawa fuskarta daukeda murmushi Wanda duk na ganin Sa’adah ne data Gama sauyawa tana alfaharin ganin yarta akoyaushe yanzu sbd rayuwarta ta ingantu.

Laylah Kam qarasawa tayi gaban gadon Abbanta da idanuwansa suke bude Yana kallon sama takai hannunta dake rawa ta Dora Kan NASA tareda sake wani irin murmushin tsananin farin ciki hawaye nabin fuskarta
Ahankali ta furta”

Abbah.

Tana gani hawaye Suka biyo gefen idanuwansa da alama yajita yakuma ganta din
Da wani sabon farin cikin ta qanqame hannunsa tana fashewa da kuka Mara sauti tana share hawayensa Dake gangara tace”

Abbah nayi kewarka sosai
Allah yabaka lafiya katashi..

Anty Sa’adah ma qarasowa tayi cikin nutsuwa da kulawa idanuwanta na cika da hawayen tausayi da kewa tace”

Abba ya jikinka?
Allah zai baka lafiya Inshallah,
Zaka tashi kaga burinka na Auren Laylah da Turaki yacika kasamun Albarka ko akwance sbd na tabbatarda cikar burinka……

Tsit kowa yayi sbd subutar zancen da Sa’adah tayi gaban Laylah wadda itama dauke wutar tayi duk da zancen Bata wani fahimcesa illah ma saita Dan dago ta kalli Sa’adah da idanuwanta dake kaca kaca da hawayen farin cikin ganin Abbanta tace”

Anty Sa’adah Abbyana kukan farin cikin ganinmu..

Hawayen Abban ne suka ninka gudu alamar zancen Sa’adah ya shiga zuciyarsa sosai Kuma dukkaninsu sun gano hakan shiyasama Anne ta matso tayi Masa sannu tareda adduoi dakuma sake basa tabbacin Aure tsakanin Turaki da Laylah anyi shekaru yanzu kam saidai fatar alkhairi aciki.

Maganar Anne tasanya Laylah dagowa wannan karon tana kallonsu da kyau Dan yanzu zancen ya wuce subutar bakin Sa’adah da rudu tunda Anne tana fada.
Kan Momy ta maida kallonta zuciyarta na tsananin bugawa da tsoro da fargaba dama komai,

Dauke Kai akanta Momy tayi Kai tsaye ta juya zata bar dakin Laylah tayi saurin Shan gabanta tareda zubewa qasa idanuwanta na sauyawa ja murya na rawa tace”

Momy wallahi har abada bazan taba cutatar da Anty Sa’adah ba sbd ta wani bangaren kallon tamkar uwa nake Mata,
Har abada bazan taba kallon mijin anty Sa’adah da wani manufa ba daban bare hada wata muamala dashi ,
Momy wallahi ba……

Hannu momyn ta daga Mata tana sake dauke kallonta daga gefen Laylan tace”

Karki haramtawa kanki abinda yake halas gareki Dan Aure Kam Dake aka daura tun farko bada Sa’adah ba,
Ki gode Allah daya karbe uwa daga gareki saiya Baki uban daya fifitaki akan Yar uwarki.

Tana Gama fadar Haka ta raba ta fice daga dakin
Anty Sa’adah da jikinta yayi Sanyi da yanda momyn ta qarasa zancen saita bi bayan momyn.

Kasa dagowa Laylah tayi saima wani irin nauyi da hawayen kunyar kanta dasuka rufeta data Gama sauraran abinda Anne ke fada cewan itace asalin matarsa bawai Sa’adah ba
Takuma jaddada Mata akan tabar zancen ahakan ba buqatan Ms Na’ima tasani sbd gujewa fitina tukuna.

Jin tayi duk ta muzanta agaban anty Sa’adah da Momy sbd ta tabbata Kamar yanda Momy ke fada cewan zata zamewa Sa’adah matsala
Gashinan ta zama sanadin hanata aurenda aka gama Sanya Mata rai,
Bayan Haka ta Yaya Rana tsaka zata iya kallon mijin yayarta a matsayin nata mijin?
Tayaya zata kalli Abokin mahaifinta amatsayin mijinta,
Tayaya mariqinta Wanda takewa kallon uba mahaifi amatsayin miji¿
A bangare daya Kuma mijin uwar riqonta data dauketa ‘ya lokaci daya ace itadin kishiyarta ce,
Wannan wani al’amari Mai girmane gareta daga ita har mum Na’ima din Dan itace Mai tabbacin zafin kishin mum din tata dakuma yanda take fada bazata iya hada kowa da Turakin ba.

Ziyarar Abban gabaki daya rage armashi tayi sbd Laylah gabaki daya ansanyata cikin wani Hali Mai wuya da tsaka sbd Jin tayi tagama muzanta a gabansu Momy harma da mum Na’ima da Bata tareda ita
Dan Haka Koda suka dawo masaukinsu kasa sakewa tayi tana Gama komai ko abinci bataciba ta kwanta.

Washe gari bayan sallar asuba qin tashi tayi da wuri sbd kunyar anty Sa’adah takeji matuqar gaske data Momy data biyosu gidan ta kwana
Dan Haka Bata fitoba Saida Momy da Anty Sa’adah sukai wanka Suka fita Dan Anty Sa’adah taga inda momyn take zama Anne ma ranar akwai likitan dazata gani na ciwon qafafu dayake ba motaci a gidan da yawa sai guda daya ta Turakin sai A Abdoul ya fita dasu da ita Dan Anne wuni zatai a wani gurin daga asibiti anty Sa’adah ma gurin Momy zata wuni dayake ranar ba’a ziyara asibitin,
Dan Haka Bata fitoba saidataji gidan tsit alamar sun fice ta tashi tafada toilet jikinta duk amace sbd damuwa da yunwa ta sakarwa kanta ruwa tayo wanka.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button