NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL BY MAMUHGEENOVELS

NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL

NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL BY MAMUHGEE

Tana kunnawa Kiran Anne yafara shigowa ta gyara zama suna wayar harda tambayar jikin mum Na’ima tayi Anne tace taji sauki sosai ba laifi.

Suna gamawa Abbahh na Kira ta kalli wayar zuciyarta na samun nutsuwar ganin kiransa ta daga wayar tareda komawa ta kwanta jikin gadon tana amsa sunanta na asali daya kirata dashi.

Bacci Takoma bayan Gama wayarta da Abban Bata farkaba sai guraren 11 lokacin Ruky tagama Mata komai na abubuwan datasan tana breakfast dasu
Anty Sa’adah kuwa sai kulawa takeyi da komai data shafi Laylahn sbd har cikin ranta Jin so da kaunar cikin take itama harma takejin inama Allah zai nuna Mata ranarda zata raini nata cikin harma ta Haifa idan tanada rabo.

Momy kuwa da wuri ta shirya ta fice daga gidan sbd ganin kamar yarta takoma itace naiwar Laylah yanzu tunda suna zaune gidan mijinta,
Hakan ke son saka ‘daci cikin ranta Dan Haka ta shirya ta fita Bata dawo gidanba sai magriba sbd qarin Bata kaunar Yan uwanta ko daya yazo gidan a yanzu,
Duk sukazo sukaga Laylah da ciki zasu tada hayaniya da Rigima ne kawai shiyasa duk qarin fitarta sbd idan batanan karsu zo.

Washe gari ma Haka ta wuni gurin harkokinta a cikin gari sai dare tadawo.

Itadai Laylah koyaushe tana tareda abbanta da anty Sa’adah dasuke debe Mata kewa da Bata tsananin kulawa da kauna,

Wata tsananin shaquwa da sabuwar kauna suke nuna Laylan da cikinta Wanda wasu lokutan sai taji jikinta na yin sanyi har hawaye takeyi idan taga yanda anty Sa’adah ke Mata ta.

Ta bangaren abbanta koyaushe sake tunatar da ita yakeyi karta taba riqe abinda Momy ke Mata a ranta sbd koma menene itace ta zauna dasu alokacinda suke basuda kowa Kuma tunda Bata taba cutatar da itaba shi ko ahakan Yana godiya.

Da wannan take sake girmama momyn duk da duk wani girma da kaunar momyn datake sbd itace ta Haifa Anty Sa’adah,wadda takewa kallon uwa awani bangaren.

Ms Na’ima taji sauki sosai tadawo hayyacinta hakan yasa Zinat ta sakata taqi Kara ko kwana asibitin sbd Kar a zurfafa bincike akanta agano batada hankali cikakke
Dan Haka Kai tsaye Ms Na’iman ta tattara ta tafiyarta gidan Haj zinat batareda ta sanarda Turakin ba Saida Dr faruk yakirasa ya sanar dashi cewan ta tafiyanta.

Cikin nutsuwa Turakin yace”

Ba damuwa tunda tasamu lafiya,
Kawai dai ayi gaggawar bincika syringe din da aka samu gurin bincika sanadin gobarar sbd ba daya bane Wanda aka samu kusan gudan biyar ne,
Inason sani menene takeyi da alluran koma wane irine.

Inshallah Allah sir Turaki Muna Kan bincikawa cikin qanqanin lokaci zamu Gama dubawa,

Sai maganar results din Ms Sa’adah shima ya fito tana tareda Leukemia Sir and tayi nisa…..

Shiru Turaki yayi cikin wani yanayi Mai girma daya taba zuciyarsa..

Mahmoud da momyn Sa’adah din yafara Jin sun tsaya Masa arai kafin A Abdoul dinsa daya Riga yasan maganar Dake tsakaninsu Bayan yasan A Abdoul dinsa Bai taba soyayya da kowace mace ba sai akan Sa’adahn…

Gangaro da tunaninsa yayi akan tasa Matar da batada kowane makusanci bayan Sa’adahn take yaji zuciyarsa ta karye da labarin.

Cikin nutsuwa ya bude Baki yace”

Menene nisanta??

Ajiyar zuciya Dr faruk ya sauke cikin sanyin jiki shima yace”

Tayi nisa sosai sbd inaga ta Jima tana samun symptoms dinta Amma Bata saniba inaga kokuma tasani Bata tana zuwa ganin likita ba.

Dr faruk ka shirya Mata ganin likitan cancer dayakeda qwarewa da sani sosai akowace qasar yake cikin gaggawa zai duba ta.

Inshallah Allah Turaki zanfara aikin hakan ayau dinnan.

Yana Gama waya da Dr faruk kasa sanar da kowa yayi sbd Babu Wanda abun bazai tababa acikin mutanen Nan Dan Haka yasa A Abdoul yayi masu booking tickets na tafiya.

Na’ima yafara Kira dan jinta itama Amma taqi daga wayar yana kashewa massage dinta yashigo wayarsa cewar zata zauna gurin Zinat kafin agyara Mata sashenta Dan Haka yabarta tasamu nutsuwa anan din kafin kwana biyu.

Yana gama karanta massage din ya kashe wayarsa ya aje gefe Yana sake shiga nazarin rayuwar Sa’adah da Allah yabawa kyakkawar zuciya Ashe tanada tata qaddarar agabanta itama.

Haj Zinat data turawa Turaki massage din ta ajiye wayar Na’iman a gafe tareda kallon siddika Data dauko Mata wayar daga daki Na’ima na wanka tace”

Tafiya zamuyi gobe tunda safen Kuma goben zamu dawo karki kuskura Koda Wasa wani yasan munyi tafiya munbar garin Abuja a goben.

Kallonta siddika tayi cikin tsoron fadar abinda ke bakinta tace”

Akwai yiyuwar Anne zata iya zuwa Nan din dubata idan tazo mezance Mata?

Wani mugun kallo Haj Zinat tayi kafin tace”

Kice munje asibiti kokuma kice munje siyan kayan sawar Na’iman tunda kusan komai ya kone.

Gyada Kai siddika tayi tareda juyawa tabar gurin Takoma daki.

Waya Haj Zinat ta dauka ta lalubo wata number tasaka Kira
Ana dauka tace”

Komai ya zama ready kufara wucewa yau zamu sameku goben acan.

Kashe wayar tayi tareda miqewa daukeda wayarta data Na’ima ta nufi dakinda Na’iman take tana shiga ta aje Mata tata wayar ta fito.

Bata fadawa Na’iman komaiba Saida tasa aka siya musu tickets din tafiya da daddare sun fara cin abincin Na’iman na zaune tarasa meyake Mata Dadi acikin Rai,
Bata cikin nutsuwa zuciya data ruhi
Qunci da damuwa takeji sosai wanda ta rasa inda zata saka ranta taji sanyi,

Zinat ta kalleta cikin son sake cakuda Mata qwaqwalwa ta gyara zama ta kalleta dakyau cikin yanayi na bayyanarda damuwa tace”

Na’ima ki nutsu kiji sauran gaskiyar da aka rufemu baibai akanta sbd yaudara da son zuciya irin na Anne Dan wlh itace taci mafi girman Amana a lamarin..

Ba cikin shege neba a jikin Laylah,
Ciki dai Dan halak ne,
Dan cin Amana, Dan zamba cikin aminci,
Laylah itace asalin matar Ba Sa’adah ba…….

Abincin Dake bakin Ms Na’ima ne ya dawo Mata da qarfi tana sakin wani tari Mai qarfin gaske ta dauki cup da sauri zata Sha ruwa Haj Zinat ta jefa Mata wata qaramar qwaya aciki batareda ta Ankara ba takai ruwan bakinta Tasha tanajin zuciyarta na balbalowa da wuta….

Wurgi tayi da cup na glass yafashe ta kalli zinat da idanuwanta dake neman sauyawa tace”

Wlh bazai yiyuba,

Laylan ce Matar Turakin?

Kishiya ta ake nufin na Raina?

Ba gaskia bane sbd yamata ciki ne zasu boye mutuncinsa suce ita matarsace Amma qaryane,
Bazai yiyuba tana matarsa shekaru masu tsayi bansaniba……

Riqota Zinat tayi Dan qarasa yamutsa kanta da qwayar data Bata tace”

Gskiyar kenan Na’ima,
Laylah matar Turaki ce Kuma uwar yayansa tunda gatanan da cikinsa a jikinta,

Abin haushi da baqin ciki ke yanzu ba lallai ki haihuba tunda qwayoyin ciwonki sunada qarfi zasu iya lalata qwayoyin haihuwarki Dan Haka bazaki taba yardaba da wannan Cin Amanar da yaudarar da akai Mana….

Jikin Na’iman har wani irin rawa yakeyi idonta yayi jajir tafara bubbuga kanta tana maimaita kalmar”

Bazan yardaba,
Cin Amanata sukayi,
Yaudarata sukayi,
Saina kashe Laylah da cikinta sunbar duniya…
Sai sun bar duniya..

Miqewa tayi tana tareda ture duka kayan abincin Dake Kan dining din tana bin hanya ko gani Sosai batayi sbd masifar Dake ci acikin jikinta.

Wani murmushin cika aiki Zinat tasaki tana kamota ta riqe da qarfi tana cewa”

Ki nutsu Zinat zamu ladabtar da Laylah Amma ba yanzuba sbd Bata gari tana gidansu Turakin ya aikata Dan Haka gobe tunda safe zamu tafi da hannuwanmu zamu dasa Mata tarihi kaman yanda ta dasa Mana.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button