NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL BY MAMUHGEENOVELS

NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL

NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL BY MAMUHGEE

Gyada Mata Kai tayi cikin kulawa da Yar qaramar magana tace”

Daga can kisamo Min babbar tsarabar saurayi ko miji Dan Naga anan bakida alamar yin ko daya….

Murmushin rashin abin fada take kokarin saki idanuwanta suka sauka Kan Wanda ke fitowa kwarjininsa ya cika idonta da bakinta takasa fadar abinda zata fada ta dauke kanta tana maidawa Kan Ms Na’ima tace”

Good morning,
Barka da fitowa.

Kallonta yayi kafin ya kalli Ms Na’ima Data dawo gurinsa tareda riqo hannunsa cikin nata tana cewa”

Good morning Turaki.

Amsawa yayi Yana daga wayarsa da hannun daya ya Dora a kunne Yana amsa Kiran daya shigo wayarsa
Ya zare hannunsa a hankali tareda kallon Laylahn data dauke Kai tana kokarin shigewa mota Kai tsaye yace”

A Abdoul zai kira Wanda zai daukeki dakun isa….Harya gotasu ahankali ya furta”” ki kula…
Ita kadai ta iya Jin kalmar saidai Bata bi bayansa da kallonba harya shige mota suka fice da A Abdoul sbd mum Na’iman Dake gurin.

Juyawa tayi ta fada mota itama Dan tsayuwar ta isheta jiri jiri take kamar ji sbd zazzabin tun Daren jiyan datake tareda shi.
Suna Isa gidansu Sofia ta shirya ita kawai take jira Daman
suka dunguma zuwa airport dinsa sauran yan tafiyar suke can
Suna Isa ba jimawa Suka daga.

Koda suka Isa Florida zazzabine sosai a jikinta Haka ta lallaba Suka Isa gidan step sister din Sofia
Suna Isa ta kwanta Dan gabobin jikinta gabaki daya ciwo suke.

Bacci tayi Mai nauyi sai yamma sosai ta tashi lokacin zazzabin ya fada mata tayi wanka da ruwan dumi tayi sallah kafin ta shirya ta fito sanyeda half gown da doguwar socks har cinya da cardigan,

Tea Aunt siya ta hada Mata ta Bata tareda maganin zazzabin dayake Nurse ce
Saida tayi mintuna da Shan tea din suka nufi Dan dining din gidan mai kujeru hudu sukaci abinci sbd mijinta baya qasar yaje gida nijar ba yanzu zai dawoba..

Wanda zai dauketa yakirata kusan so uku tana bacci Bata dagaba Dole takirasa Dan kada yakira Abban ya fada Masa ta sanar dashi yabari sai gobe yazo ya dauketa sbd batajin Dadi yau din.
Anan ta kwana gidan, washe garin ma anan ta wuni sai yamma takirasa yazo ya dauketa tareda Sofia suka tafi zuwa apartment din da aka Kama Mata,

2bedroom ne sai Palo dasu toilet
Komai na gidan yagama tsaruwa yanda zataji dadin zaman garin fiyema da yanda tayi tunani dan kuwa dagani gidan ba qaramin kudi aka biyaba aka Kama matashi da dukkanin kayan cikin da aka zuba Mata sabbi.

Bayan tafiyar wanda yakawosu kayanta Sofia ta jera Mata a closet ita tana kwance tana waya da Anty Sa’adah har Lokacin dai ba wani qarfi ajikinta..

Sofia tayi musu order na wasu abubuwan abinci ba jimawa aka kawo musu ta gasa musu bread sukaci da kwai da hot milk sallar ishai kawai Laylan tayi ta kwanta bacci yayi gaba da ita.

Saida Suka kwana biyu a floridan tana fama da zazzabin datazo dashi kafin tasamu warwarewa bayan magungunan data samu gurin Aunt siya tasha Suka fara fita zuwa abinda yakawosu Wanda kullum da qarfe 10 suke shiga su fito 12 daganan saisu koma gidanta kokuma gidan Aunt siya danma bata cika zamaba gida tana asibiti koyaushe,
Hakan yasa Suka fara yawon shoppings da guraren bude ido a garin tunda basuda wani abin Yi dasun fito class din program nasu.

Kwanansu goma a garin suka Saba da garin sosai musamman dayake cikin abokan tafiyarsu akawi Yar garin Kuma suna Shiri sosai da Laylan gashi tanada mota Nan suka ringa yawo kala kala.

Yau pleasure beach sukaje Suka shiga water Ride daqyar ta iya shiga sbd tsoronta da ruwa Amma su Sofia suka tilasta Dan Haka tana shiga Bata jimaba a ta fito kanta na juyawa ta nema guri ta zausa Saida Suka Gama Suka fito suka nufa Cinema acan Suka qarasa wunin Suka kamo hanyar dawowa gida.

Gidan Aunt siya Suka nufa suna shiga ko tsakiyar palonta Bata Gama kaiwaba ta tsaya cak jirin datake ji tun fitowarta water Ride tana daurewa ya dibeta tayi gefe ta zube idanuwanta na rufewa.

Kiran sunanta Sofia tayi tareda yowa kanta da sauri tana qwala Kiran Aunt siya Dake Shirin fita zuwa asibiti…

Da mamakin Kiran Aunt siya ta fito tana ganin Laylah akwance da sauri ta taho tana cewa”

Meya sameta?

I dnt know….she just fainted….

Ruwa Aunt siya ta nufa fridge ta dauko da sauri tadawo tana kokarin bude robar ruwan idanuwanta ya sauka Kan jinin Dake biyo gefen Laylan ta qarqashinta Yana gangarowa ta saki robar hannunta da sauri tareda fadar”

is she pregnant Sofia????? Da mamaki Mai tsanani girma Kan fuskarta qarasa tambayar Sofia hakan.

Sai alokacin Sofia ta lurada jinin ta kalli Laylan da sauri wadda idanuwanta ke rufe da alama ta some
Tace”

She can’t be pregnant Aunt,batada ko saurayi fa bare,
Wani abun ne daban just do something Aunt siya….

Da sauri taje ta daga wayarta takira motar asibiti tareda dawowa ta Kama hannun Laylan tana Jin pulse dinta tasake kallon fuskan Laylan ta bude tafukan hannunta ta duba cikeda mamaki ta miqe tana sintirin jiran motar asibitin sbd ta tabbata Inshallah Laylah is having a miscarriage…

Koda motar asibitin tazo hankali tashe suka kwasheta zuwa asibiti
Lokacin Sofia takira wayar mum Na’ima yafi so nawa baya shiga sbd ranar ta wuce Nigeria….

Shiga tashin hankali Sofia tayi sbd batasan waye zata kiraba Kuma ta sanar bayan mum Na’iman sai Abban Laylan Wanda take Jin shakkar kiransa sbd tsoron idan cikin ne da gaske karyazo yaji tajawa Laylan fitina a gida Dan Haka ta daure Bata kirasaba tafara kaida kawon jiran ganin laylan tafara samuwa tukuna.

Aunt siya tayi mamaki miscarriage a jikin Laylah saidai sbd yanda yazo Mata da matsala yasa Bata tsaya wannan ba aka duqafa ganin bata galabaita sosaiba sbd cikin duka suka baifi sati ukuba suke saka gani Dan Haka Dole Sofia takira Abban ganin jikin yazowa da Laylah da wuya.

A Abdoul takira ta sanar Masa suna asibiti Laylah batada lafiya.

Shiru yayi bayan yagama Jin abinda tafara ta dago ya saci kallon Turaki dake zaune cikin navy blue Ralph Lauren Kaftan suit fuskarsa sai sheqi yakeyi da alama Yana cikin nutsuwa.

Dan gyara necktie din wuyansa yayi tareda aje iPad Dake hannunsa
Turakin ya kallesa ganin magana yakeson fada ya dauke ido akansa alamar yanajinsa.

Ms Laylah na asibiti batada lafiya
Da alama kamar sosai ne sbd qawarta data Kira akwai sautin kuka s tareda ita…..

Dakatawa yayi iya Nan sbd Ganin cak Turakin ya tsaya daga signing dayake a takardu batareda ya dagoba ya kallesa.

Shiru ya ratsa office din kafin ya dago ya kalli A Abdoul Dake jiran umarnin abinyi.

Kallon da yayi Masa yasashi gyada Kai Yana cewa”

Zanyi booking tickets yanzu.

Juyawa yayi ya fice da sauri Yana fidda wayarsa take yayi musu booking tickets din zuwa Florida
Yakoma ya tattara sauran ayyukan Dake desk na office din Turakin yayi clearing schedules dinsa na ranar gabaki daya dama na gobe ya dawo ya sanarwa Turakin jirginsu Nan da 3 hours zai tashi.

Sai cikin dare ta farka idanuwanta jajir sun Mata nauyi hakama jikinta ba qarfi ko kadan
Ta waiwaya gefenta ahankali taga Sofia zaune tana riqeda hannunta daya idanuwa sun Dan sauya alamar harda kuka tayi
Ta lumshe ido hawayen dake ciki Suka gangaro gefen fuskarta tanaji ahankali Sofia tace”

Laylah you had a miscarriage…

Wani irin kukan da bataso zuwansa bane ya taho Mata cikin qaramin sauti da rashin kuzarin jiki na tsoro da damuwar da batasan ta halinda take ciki ko kunyar kanta datasu Sofia din.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button