NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL BY MAMUHGEENOVELS

NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL

NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL BY MAMUHGEE

Tabbas Basu fada Mana cewan Sa’adah Matar Turaki shiyasa shegu tsinannu suka bar Na’iman ta tafi da Laylah wato takai Masa matarsa har gidansa……

Tun farko wane Dan burauban shegen ne Yafada Mana Sa’adahn ce Matar Turaki????” Tafada tana dago da jajayen Idanuwanta ta Dora Kan Siddika da jikinta yafara rawa tana neman zancen fidda Kai tana kokarin magana Zinat ta sauke Mata wasu kyawawan Marika guda biyu tana fizgota tace”

Dama bakida sani akai Kika kawo Mana wannan zancen kokuwa da gayya kikace Mana Sa’adahn ce?

Cikin azabar Marin datasha tafara rarraba Ido tana hawayen tsoro sbd komai zasu iya Mata tunda tafi kowa saninsu ba Imani ne dasuba musamman Haj Zinat din tunda har Ms Na’iman itake fada Mata yanda za’ayi komai.

Dukan fita hayyaci Zinat ta ringa yiwa siddikan tana cewa”

Kece Kika lalatamun komai da shirina na shekaru Dana Jima Ina fafutaka akansa,
Matsiyaci wlh zanyi lokacinki idan nagama da Laylan da Na’iman tukuna..

Tattarawa tayi tabar gidan sbd zata iya kashe siddikan idan Bata bar inda take ganintaba,

Sabon tashin hankali tashiga na musamman sbd na farkon duk Mai saukine a daukansu cikin shege ne jikin Laylan ba Turaki Dan Haka komai zaizo da sauki,
Amma Jin Laylah Matar Turaki ce yasata Shiga matsananciyar tashin hankali sbd Dan halak ne wato zata Haifa masa,

Magajinsa fa kenan??

Magajin dukiyar dasuka Dade suna shirka akanta Dan su mallaketa koba dukaba su mallaka Rabin,

Magajin dukiyar da akanta taketa durawa qawarta dasuka taso tare tun yarinta maganin data juyar Mata da qwaqwalwa ita ke controlling dinta….

Amma ace Rana tsaka wata qanqanuwar yarinya ta samesu daga sama Bayan tagama lalata mata komai na wargaza gashi sanadin hakan Turaki zai iya gano halinda Na’iman take ciki Wanda Yana ganowa tasan labarinta yaqare daga Nan Kuma…

Wlh bazata yardaba,
Komai zata iyayi dan ta tsira,

Yanzu babban burinta ta fito da Na’ima daga gidan,
Sbd sai Na’iman Bata gidan zata samu damar kawar da Laylah da cikinta daga duniya Kai tsaye sai laifin ya rataya Kan Na’iman wadda ita Kuma takardun shedar haukanta zaisa hukunci bazai hau kantaba
Dan Haka duk tsanani saita fidda Na’ima daga gidan
Kuma zata fiddatane daga gidan ta hanyar da Laylah zata daga hankalinta itama ta fito daga gidan.

Washe gari da gangan tana sane taqi zuwa gidan sai dare tazo
Lokacin Na’ima ta farka Amma Bata iya komai sai Ido datake Binsu dashi Haka ta sake sakarwa Na’iman wata allurar data sake maidata halinda ta fito idanuwanta suka rufe Takoma baccin wahala.

Fitowa dakin tayi siddika na biye da ita Saida suka zo palon ta kalli siddikan cikin bayyanarda Mahimmancin aikin da zata sakata ta kalleta tace”

Aiki Mai mahimmanci Zan sakaki
Idan Kika Bata mun aiki wannan karon Wlh yanda na maida Na’ima fin hakan Zan maida rayuwarki,kina Jina????

Gyada Kai tayi tana cewa”

Zan kiyaye Wannan karon.

Ciro qaramar kwalba daga jakar hannunta tayi tareda qaramar lighter ta miqa mata..

Karba siddikan tayi tana bude idonta akan kwalban da warin fetir ke tashi acikinta
Ta hadiye wani mugun yawu tana kallon kwalban da lighter din cikin rawar murya tace”

Wannan fetur…..

Katseta tayi da cewa”

Nafiki sani tunda nice nabaki,

Anjima da daddare ki zuba a akan gadon Na’ima Kuma ki zuba Mata kadan a jiki saiki janyota ki fito da ita daga bakin kofar dakin ki kunnawa dakin wuta,

Karki Kira jama’a sai wutar taci sosai Kuma ki tabbatarda ta shaqa hayaqin wutar saiki fita ki Nemo jama’a,

Kafin akirani idan antambayeki garin Yaya kice itace ta kunnawa dakin wuta da kanta tana cewa kunnawa gidan wuta zatai kowa ya mutu har Laylah.

Tsananin tsoro da mamakin girman rashin Imanin Zinat din da zata cutatarda Ms Na’ima sbd son abun duniya..

Cikin sake bayyanarda zata iya Mata abinda tace zatai Mata idan ta Bata Mata aiki tace”

Idan Kika aikata kuskure daya komai ya lalace wlh ke Zan cinnawa wuta kifara Isa lahiran kafin muzo.

Wucewa tayi tabar siddikan tsaye tana binta da kallon mummunan tsoro da tashin hankali…

Kasa zuwa kitchen tayi da fetir din ta nufi dakin Ms Na’iman dashi ta boye bayan Kan gadonta tana kallon fuskarta…

Akaro na farko da Tausayin Ms Na’iman ya ratsata sbd batada Mai qaunarta bare yabata shawara,

Tayi watsi da qanwar mahaifiyarta data riqeta sbd samun duniya a hannu gashi yanzu tazo tana neman Rasa komai…

Duk da Ms Na’ima Bata kyautata Mata saima izza da bossing dinta datake koyaushe Amma Bai kamata a cutatar da ita hakaba abun yayi yawa bayan arzikin dasuke ci suna Tarawa daga Haj Zinat din har ita duk qarsqashin Ms Na’iman suke samunsa…

Itadai gaskia bazata yarda tayi biyu babuba wlh ta koma rayuwar wahalar data fito,
Dan gwara Mata wulaqanci da masifa harma da bala’in Ms Na’ima akan barin gidan AB TURAKI Dan Haka Dole zatasan yanda zatai bada saninsuba ta bayyanarwa da Anne ko Turakin lalurar da Ms Na’ima take dauke da ita ko za’a rabata da Zinat a cetota tasamu taci gaba da cin arzikinta lfy kafin Zinat din ta wargaza musu Suma komai.

Ba yanda ta iya da daddare Haka ta cinnawa dakin wuta
Aikuwa wuta Mai qarfi ta tashi wadda batama tsammata ba
Tsoro ya kamata ta fito da gudu tunda wuri ta nema jama’a sbd wutar kamar jiratake a kunna koina yafara dauka.

Hankali tashe securities da kowa gidan ya fito,
Anne na dakin Laylah a Daren sbd wani zazzabin datake fama dashi na damuwar Dole data sakawa kanta,
Gashi taqi yadda ko ganin juna suyi da Abban nata sai zaman boyo take a daki duk ta Hana kanta sukunin zuciya shima ta hanasa sbd rashin ganinta yafi komai daga hankalinsa ita kanta rashin ganin nasa ne yaketa nukurkusanta.

Jin hayaniya na tashi a gidan yasa Anne miqewa daga zaunen datake tana bawa Laylah tea abaki tana Sha jiki amace.

Fitowa Palo Anne tayi tana cewa”

Halima lafiya gidan Nan kuwa nakejin hayaniya?

Wutace ta tashi Anne a bangaren Ms Na’ima sosai Kuma wlh..

Subhanallh innalillahi, yanzu?
Ina Na’iman?
Bata ciki dai ko???

Fita tayi da sauri tana faman nanata tambayar Allah yasa Na’iman Bata ciki.

Siddika ce kawai a waje takasa komawa jiki jikinta sai rawa yake hankalinta ya tashi Bata dauka wutar zata juye ta zama hakanba..

Koda Turaki ya fito gurin cikin sauri ya qaraso Yana tambayar Ina Na’ima?

Cikin tsananin kuka da firgici siddika tace tana ciki… Aikuwa Bai tsaya Gama ji ba ya nufa kofar ya shige…

Anne da sauran maaikatan gidan da securities suka fara ihun Kiran sunansa….

Anne da sauri ta bisa zata kamo halima ta riqeta ta hanata shiga….

Ihun Kiran sunan Turakin da ake yasa Laylah fitowa Bata ko ganin gabanta sosai jikinta har rawa yake ta kallesu cikin yanayinda muryarta Bata ko fita sosai ta bude Baki zatai magana sai gashi yafito daukeda Na’iman data Gama shaqar hayaqin harta fita hayyacinta da sauri ya nufa mota da ita Yana cewa A Abdoul daya iso ya bude mota da Sauri.

Shigewa motar yayi Suka nufa asibiti
Suna fita motar kashe wuta na isowa aka fara kashe wutar.

Anne jininta ya Riga ya hau Dan Haka Dole Saida aka kamata aka maidata ciki
Laylah ma daqyar ta maida kanta ciki suka kwantar da Anne bayan anbata maganin Hawan jininta ta kwanta itama ta nufi daki ta zauna sbd bacci kam ya Riga ya qauracewa idanuwanta,
Zazzabin datake ji ma take taji yasake,
Gabaki daya hankalinta ya tashi Kuma sbd koma menene tasan wanna wutar tanada alaqa da abinda yake faruwa..
Gida takeson zuwa kowa yasamu damar samun nutsuwa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button