NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL
NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL BY MAMUHGEE
Kamar yanda yasan Abban akan abinda yake so dagewa Abban yayi cikin azabar ciwon daya taso Masa gadan gadan yace”
Amatsyina na ubanta nine nake rokonka cikin qasqantar da Kai Turaki ka dauketa ka tafi da ita,
Idan bazaka auretaba nabaka ita halak malak Dan Allah ka inganta rayuwarta,
Batada kowa bayan Ni Ina rokonka daka zame gatanta tana cikin maraicin uwa da uba,
Shi kadaine rokona dakuma burina da gata kacal daya dazan Mata tsawon rayuwat……….
Bai qarasaba take bakinsa ya juye sbd ciwon yagama tasowa gabaki daya take ya sake fadowa daga kujerarsa ya zube qasa Yana fitarda wani irin zufa da kumfa idanuwansa na juyawa…
Daidai shigowar Laylah daukeda ruwan dumi data debo da qaramin towel zata Dan gasa Masa qafafunsa..
Mummanar faduwa gabanta yayi ta dire kayan hannunta tayo kansa cikin mummunan yanayi tana Kira sunansa cikin iya sautinta Mara qarfi sosai Dan wahalar rayuwar tagama cinye qarfinta shiyasa komai nata a sanyi take yinsa Wanda bayan sanyin jiki hardana wahala data Gama cunyeta.
Kamosa tayi tana Kiran sunansa dukkanin jikinta na rawa sosai Kamar yanda na Abban keyi
Tana kokuwar dagasa saiga abdullahi yashigo
Shima da gudu yaqaraso cikin tsananin tashin hankalin ganinsu ahakan hankali tashe da babban sauti yace”
Meya samesa?lafiya?
Kasa magana tayi sbd halinda tariga tashiga da ganin Abban hakan sai kawai ta sauke kanta tana rintse idanuwanta bayarwa hawaye sun fito ba dan tuni qamewar zuciya yagama busar da hawayenta tuntuni Dan kuka gareta wahalar banzace shiyasa Bata kuka Dan ko taso tayi kukanma Baya zuwa….
Jiki na rawa Abdullahi ya fitarda wayarsa ya lalaubo numbern Dr Abbakar ya Danna Masa
Yana dauka cikin rudu yake fada Masa halinda Abban yake ciki take Dr Abbakar din ya kashe wayar Yana cewa ga motar asibiti Nan zuwa yanzu.
Kafin motar asibitin tazo tuni Abban yayi nisa
Abdullahi daya Gama firgicewa cikin tashin hankalin sai jijjigasa yake Yana Kiran sunansa Dan karya qarasa yin nisan Amma tuni Abban yayi nisa
Ganin hakan ta dafa bangon Dake palon sbd Jin kunnuwanta Kamar suna rufewa Dan dummmm takeji sai can taji kalma daya
Kanta ta dafe da hannu daya yayinda dayan take dafe jikin bango dashi idanuwanta sun kada sunyi jajir Babu abinda takeji Kamar tsananin radadi a zuciya da cikin kwanyar kanta Wanda ake Kira da asalin Depression
Su Momy Basu San abinda yake faruwaba Saida motar asibiti tazo kofar gidan aka shigo aka daukesa cikin gaggawa aka fito dashi sai alokacin Sa’adah ta fito da Dan sauri daidai Ana fitowa da Abban Wanda babu alamar numfashi atate dashi
Gabanta yayi mummunan faduwa hankali tashe ta kalli kofar palonsa datasan Laylah na ciki ta nufi palon cikin tsananin firgici tana Kiran sunan Laylan da zuwa lokacin kunnuwanta basa jin komai sai idanuwanta dake gani Suma ba sosai ba
Da gudu Sa’adah ta qarasa gurinta tana Kiran sunanta da qarfi tareda tallafota jikinta sbd sulalewa da laylan ke neman Yi qasa.
Laylah
Laylah
Meya samu Abban?
Meyake faruwa?
Kina Jina kuwa?
Karki rufe idanuwanki Laylah kalleni,
Kina bani tsoro
Dan Allah bude idanuwanta sosai ki kalleni,
Meyasa samu Abban?
Kina lafiya kuwa??
Laylah.. Laylah.. Laylah.
Sunan Momy Sa’adah din ta kwala da qarfi cikin tsananin firgici tana cewa”
Momy kizo Dan Allah Laylah ma mutuwa zatai tabarni
Na shiga uku,
Momy….Momy Dan Allah kizo…
Momy dake zaune jagwab a Palo tana tsiyayar hawaye bayan tafiyar da akai da Abban tanajin Sa’adah Amma takasa motsawa Bare ta tashi saima wani irin sabon mawuyacin halinda take sake Shiga akan komai dayake faruwa tanajin radadinta na shekaru Yana ninkuwa sbd har cikin ranta ba rayuwar dataso su gudanarba da Mahmoud da ‘yarta,
Meyasa komai ya lalace musu Haka,
Ina amfanin hakan,
Ta Rasa yanda zatai ta gogewa zuciyarta komai shiyasa tata zuciyar take cikin qunci fiyeda Mahmoud din Dan kuwa takasa cirewa,
Takasa daina Jin zafin na sabuntar Mata koyaushe,
Tabbas da Bata ganin Laylah da zata iya dannewa,
Amma koyaushe ta wayi gari taga laylan ko taji motsinta saita tuno Kunci da baqin ciki tareda mawuyacin halin data shiga duk akan wannan al’amarin da Mahmoud yabarta acikin quncin da sanin aurensa yayi Ashe yabarta tana bibiyar Yan uwanta gurin tallafa Mata da ‘yarta.
Hawaye takeyi sosai tana buga kanta akan kujera zuciyarta cikin qunci Mai girma yayinda Sa’adah keta ihun Kiran momyn cikin tsananin firgici da nata hawayen Dan kuwa wannan ne Karo na farko da Laylah tashiga irin wannan halin Dan har wani kakkarwa jikin laylan keyi.
Ganin ba wani taimako daga kowa yasa Sa’adah zame Laylan daga jikinta da sauri jikinta na rawa ta debo ruwan zafin da laylan tashigo dasu tun farko tazo tazubawa laylan da yawa a fuskarta tana Kiran sunanta cikin fatar tadawo hayyacinta….
Kamar bazata dawo hayyacin nataba sai gashi ta bude idanuwanta ta zubawa fuskar anty Sa’adah din dake kanta cikin firgici tana jiran farkawarta….
Batareda ta motsaba ta maida idanuwanta Kan hancin anty Sa’adah din Dake digar da jini alamar habo
Duk da halin datake ciki sai data Kai hannu Kan hancin Sa’adah din da qaramin sauti tace’
Jini hancinki anty Sa’adah.
Da sauri Sa’adahn ta saketa tana tare hancin cikin mamaki da Dan sauran firgicin data Shiga na halinda Laylan da abban suke ta miqe tana juyawa da sauri ta fice zuwa waje hannunta toshe da hancin ta nufa bakin fanfo ta kunna tana gogewa da hannunta tana wanke hannun a fanfo.
A sulale Laylah ta fito ta nufi dakinta ta shige ta zube qasa Kan dadduma tareda cusa kanta cikin qafafunta kanta na tsananin sarawa kamar zai juye
Gashi Babu Wanda zata tambaya Ya Abbanta sai lokacinda Abdullahi yadawo,
Shin Abbanta Yana Raye kuwa
Kokuwa shima ya rasu ya barta a duniyar da Babu komai acikinta sai son zuciya da zabi.
Ta bangaren Sa’adah tana Gama wankewa ciki tayo ta nufi dakin Momy data bar palon Takoma dakinta ta zauna bakin gado tareda dafe kanta dake tsananin Mata ciwo itama
Ta qaraso gurin momyn ta zauna gefenta tareda riqo dayan hannun momyn da idanuwanta sukai jajir itama idanuwanta suka ciko da hawayen tausayin momyn cikin tsananin kulawa da sanyin jiki tace”
Inshallah wata Rana Zaki komai ya wanke daga zuciyarki
Kici gaba da daurewa ahakan yafi kibar zuciyarki ta ri jayeki
karki Bari shedan yafi qarfinki,
Wata Rana zakiji zuciyarki ta saki gabaki daya
Amma Dan Allah Momy ki sassauta muku ku dukan sbd zuwa yanzu Babu Wanda baya cikin mawuyacin hali acikinku,
Abba lafiyarsa da rayuwarsa gabaki daya acikin jarabawa suke
Ta yanda ma ko yaso neman yafiyarki bazai iyaba Dan Allah Momy ki saki komai kibar rayuwarki tasamu salama da nutsuwarda kowace irin zuciya ke samu.
Na Miki alqawarin idan ganin Laylah ne damuwar daga ranar da nayi aure zanbar gidan Nan Zan tafi da ita bazata sake dawowa ba har sai ranarda zuciyarki ta samu aminci da ita wannan shine alqawarina agareki umma sbd bakisan iya qaddarar da Allah ya rubuto a tsakaninki da itaba Dan kuwa dagani har ita bakisan waye Zai zana gatankiba alokacinda tsufa ko ciwo ya riskeki,
Inaji ajikina Laylah zata zame Miki farin ciki abin alfahari Inshallah
Amma saikin bar zuciyarki ta amsa qaddarar da Allah yariga ya rubuto a tsakaninku wadda ta Dade da wucewa ki yadda cewa Laylah ‘ya ce daga wata uwar.