NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL
NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL BY MAMUHGEE

A asibiti Saida suka Bata layi kafin suka samu ganin likita Dan Dan sunyi lattin zuwa,
Dunata likita yayi tareda rubuta Mata magani akan Tasha idan kwana biyu Bata warware ba zasu Mata wasu test saisu gani idan wata matsalarce babba.
Cikin ikon Allah kwana biyu tanashan maganin saigashi ta warware sosai Takoma walwalarta sai Alokacin ta lura da Sosai Laylan ta firgice kamar wadda tafara samun damuwar qwaqwalwa sai Kuma hankalinta ya tashi Dan Haka saita qi cigaba da zuwa makaranta tafara kokarin ganin ta dawo da Laylan daidai.
Asibiti ta ringa kaita gurin Abban kullum suna dubosa ko hakan zaisa tadawo daidai Amma sai hakan yake qara dagula Mata komai sbd duk ta kalla Mahaifinta ahalinda yake ciki komai sake rikice Mata yake musamman da Dr Abbakar ya tabbatar musu da Abban Yana Nan ahakan sai abunda Allah yayi kodai ya tashi kokuma daga hakan shikenan Allah ne kawai yasan abunda ya yanke akansa.
Ranar da akai musu wannan bayanin duk da anty Sa’adah tashiga wani halin itama Amma ganin halinda Laylan tashiga duk da Bata cewa kala sai hakan yayi mummunan daga Mata hankali da kuwa a bayyane tafara fahimtar depression ne yake neman juya kwakwalwar Laylah din
Haka tashiga mayuyacin halin neman mafitar tallafawa rayuwar Laylah din Dan kuwa alqawarine ta dauka zata cikawa Abba burin bawa Laylah kyakkyawar rayuwa Inshallah.
Ta bangaren Momy ganin yanda kowa yake cikin mummanan Hali na rayuwa yasa ta Amincewa umma Jamila Akan buqatar ayi auren Sa’adah ko ita zata samu ta fita daga wannan qaddarar rayuwar tasu taje gidanta tasamu rayuwar kwanciyar hankali da nutsuwarda su suka rasa ahaka suka share kusan wata biyu.
Zaune suke a palon gidan Momy na zaune shiru ta zubawa Sa’adah da duk ta lalace sbd rashin kwanciyar hankali ido tanaji tsananin tausayinta Dan kuwa a yanzune ta tabbatarda son da Sa’adah kewa Laylan Mai qarfi ne Dan kuwa wani irin so taga tanai Mata tamkar Wanda uwa kewa danta,
Ta tattara karatu ta daina zuwa tsawon watan biyu ta tattara rayuwarta gurin kokarin dawo da Laylan daidai wadda yanzu bayan idanuwa datake zubawa kowa ko magana Bata iyayi Dan kamar qwaqwalwarta ta tabu gashi basuda wani kudi ko arzikin nema Mata magani sai momyn ta zubawa sarautar Allah idanuwa Dan kaf Yan uwanta tasan bazasu bada taimakonda za’a nemawa laylan lafiya ba sai itama yanayin laylan yafara tabata sbd Sa’adah da al’amarin ya taba sosai Dan hatta ayyukan gidan sun dawo Kan Sa’adah da kula da laylah wadda ba jinyar kwanciya takeba jinyar qwaqwalwa take.
Cikin ‘dan zafi umma Jamila ta kalli Momy kafin ta maida kallonta Kan Sa’adah dake zaune gabansu tace”
Yanzu Zainab kina kallo Sa’adah zata lalata rayuwarta da kanta gurin kulada Mai ciwon qwaqwalwa bayan tanada rayuwa Mai kyau datake jiranta Amma ta kafe akan bazatai auren ba matuqar baza’a barta ta tafi da wannan Mai Kama da Marmaid din ba,
Ta Yaya kike tunanin za’a Kai budurwar Amarya dakinta ace anhadata tafiya da wata budurwar?
Waye mijin zai kalla a tsakaninsu?
Waye Zaifi Shiga ransa tunda kinsan ko a kyau da sigarsu ba daya ba
Waccar din kinaga daukan idone da ita duk da batada lafiya ga maza yanzu baka Basu Amana,
Gskia nidai ban amince ba
Babu inda za’a tafi da wannan yarinyar musamman yanzu datake kamar Mai ciwon qwaqwalwa..
Numfashi Momy ta sauke tana rintse idanuwanta cikin yanayi na gajiya da komai da komai na rayuwa ta bude Baki ahankali tace”
Sa’adah banida wani sanyin idaniya a yanzu bayan ke Dan Haka fatana da burina ganin kinyi aure kin samu ingantacciyar rayuwa,
Naga qaunar da kikewa Laylah nayi Miki alqawarin har abada bazan rabaku ba saidai aure Dole zai rabaku
Idan inganta rayuwarta kikeson Yi Dan ki rabata da zama Dani bayan tafiyarki namiki alqawarin barin ta tafi tayi tata rayuwar gidan nata auren Dan kuwa Abbanku ranarda ciwon Nan zai kwantar dashi Aurenta yaso badawa Dan dauketa daga gareni sbd kuna ganin nice ukubarta….
Shiru tayi wani Daci da qunci na sake mamaye zuciyarta sbd ita kadai tasan radadin datake ciki na duk abubuwan dake faruwa.
Da mamaki umma Jamila take kallonta da cewa”
Aure Kuma?
Hala dai Abdullahi zai bawa aurenta?
Amma kuwa za’a tauyesa da yawa yaron Nan
Yana fama da jinyar uban Kuma yanzu sai a basa wata kayan lalurar.
Girgiza Kai Momy tayi jiki amace da damuwa tace”
Ko a hali na ciwo Mahaifinta ya bayyanarda cewa nida ‘yata mune daga baya,
Dan kuwa inda ya bayarda aurenta guri ne daba gurin wasan kowaba Dan kuwa ko yayane sarakuna suka samu wannan matsayin sai anmusu barka bare anan….
Mamakine yakama umma Jamila ta kalli Sa’adah wadda duk ta yamutse gwanin tausayi tace”
Tashi kije idan nagama da momynki Zan dawo kanki Dan kuwa aure Babu fashi Kuma Babu inda Zaki tafi da ita.
Miqewa Sa’adah tayi ta juya ta nufi hanyar dakinta da tuni ta maida Laylah dakin nata tashige
Momyn tabita da idanuwanta dasukai laushi cikin sabon tausayin ‘yarta da hakanan takejin sabon son yarta akowane safiya Yana qara qarfi aranta
Gashi duk ta rame tasawa ranta damuwa da Jin Kamar tanada hannu acikin kowane Hali Laylah tashiga.
Kallon tsaf umma Jamila tayiwa Momy Kai tsaye tana Shirin magana Momy ta datasan tambayar dazatai Mata ta katseta da cewa”
ABU TURAB TURAKI ……..
Da wani irin mamakin kasa gasgatawa ta kalli momyn ba tsayawa komai ta Dora tata tambayar da cewa”
AB TURAKI dai wannan Dana sani?
Aminin Mahmoud din?
Wannan dai Mai yiwa masu kudinma wuyar gani?…..
Kasa magana Momy tayi ta gyadawa umma Jamilan Kai tana maida bayanta jikin kujera ta jingina.
MAMUH
????????????Kuyi following Dina Dan samun posting akan lokaci dama sauran novels Dina complete ????????
Mamuhgee @Arewabooks
????????????????????
KUFAN WUTA
Safiyya Huguma
BAQAR INUWA
Billyn Abdul
RAYUWAR MACE
Hafsat Rano
MASARAUTA
Miss Xoxo
NOOR ALBI
Mamuhgee
Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank
Number shaidar biya????????
09032345899
KATIN MTN
09166221261
[7/10, 9:18 PM] +234 704 076 8969: Mamuhgee 9
ArewaBooks@Mamuhgee
Wani irin tunani Umma Jamila tashiga zuciyarta na juya zancen Dan kuwa Sam ba zancene dazakayi gangancin yardaba lokaci daya duk da tasan Momy ta wuce ace tana qarya ko Wasa da magana irin wannan
To Amma Kuma tsakani da Allah duk Mai lafiyayyan hankali bazai yarda da Jin maganar auren Mutum Kamar AB TURAKI ba lokaci daya ya yarda musamman da yarinya ‘yar cikinsa ‘yar Amininsa dasuka taso tare….
Roqan Alfarma Mahmoud yayi Amma tabbas wannan magana bama Mai karbuwa bace ga kunnuwan mutane jama’a bare shi Turakin,
Bayan hakan ko ‘yayan manyan attajirai bazasu iya kishi da matarsa ba wadda duk Wanda ke bibiyar labaransu a duniya yasan mace ce datake zuba wata irin Rayuwar hutawa da Jin Dadi sbd babbar damar da Allah yabasu ta arziki da suna hakama ga kyawu duk da shekarunta sun Dan fara ja Amma sbd Bata taba haihuwaba yasa Bata daina zuba rayuwar data Saba da itaba,
To irin wannan ko masu aikin gidan tako Ina sunfi Laylah din bare Matar gidan har aje Kan Mai gidan kankat Wanda ita kanta Matar tasa saita share lokaci Bata gansaba bare wani Mahmoud da wata ‘yar sa Mai Kama da aljanar ruwa.
Girgiza kanta tayi tana kokarin yakice zancen karta cinnawa kanta hauka da tunanin maganar tana zaman zamanta
Kallon Momy tayi tana cewa”