NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL
NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL BY MAMUHGEE

Ganin dai Kawun baida niyar dawowa gida bare suzo ayi magana dashi yasa Suka yanke shawaran haduwa dashi a asibiti Dan Haka yau da daddare Yana zaune bayan yadawo daga masallacin asibitin sallar ishai yaci tuwon semo da miyar kubewa da gandar da aka kawo Masa tareda fruits
Gamawarsa kenan Yana kokarin amsa Kiran Mai dakinsa daya shigo wayarsa saiga Alhaji Qarami tareda Alhaji Atiku da umma Jamila sai Haj Karima data iso a jiya sunshigo sanye cikin shigar Alfarma,
Miqewa yayi cikin sakewar fuska Yana cewa”
Marabanku da zuwa,
Alhaji Qarami bismillah ku qaraso daga ciki,
Alhaji Atiku barka da zuwa
Sannunku sannunku
Yanzu da Daren Nan kuke shigowa.
Haj barkanku da zuwa Bismillah ku shigo,
Hannu ya miqa musu sukai msabaha Yana sake gaidasu cikin mutuntawa duk dai ya girmesu saidai kasancewarsu manyan mutane yasa shine yafara gaidasu din Suma cikin mutuntawa fuska asake suke gaidasa tareda maida kallonsu Kan Abba cikin alhini suke tambayar jikinsa,..
Allah yakawo sauki da afuwa yasa kaffarane.
Amin Amin ya Allah,
Alhaji Atiku Naga hidima anatayi damu
Allah ya Sanya alkhairi yabada Lada
Ana kokari sosai wlh
Ngd Sosai Haj Jamila.
Bakomai Kawu saidu ai duk yiwa Kaine musamman kaida kabaro iyali kazo nesa gashima bamu samu lokaci anyi maganar datai dalilin zuwan naka.
Gyara Basu gurin zama Kawun yayi Yana zama shima kafin ya nutsu Yana kallon Alhaji Atikun yace”
Eh wlh to nazo na tararda jikin na Mahmoud ba sauki ba sauyi shine hankalina duk ya koma kansa Amma ai tunda maganar aurece ba wata damuwa duk lokacinda magabatan yaron suka tsaida ranar zuwa sai a sanar Dani naje saimu taru a tattauna din….
Kallon Alhaji Qarami sukayi sbd shi Basu fada Masa ainihin gskiyar zancenba Dan bazai taba yarda da hakan ba
Haj Karima ta karbe zancen da cewa”
Aure Kam ai magana na hannunka Dan kaine Wanda zai tunkari Wanda aka bawa auren da maganar auren kasancewar Kaine tamkar uba agareta tunda Kaine tamkar uba ga mahaifin nata Dan Haka komai a hannunka yake.
Murmushi Kawu yayi Yana jinjina Kai yace”
Hakane,
Inshallah Allah wannan aiba wani matsala bane,
Auren ne manemin Bai tashiba kokuwa?sai anemesu muyi mgn dasu….
Alhaji Qarami ne ya gyara zama Kai tsaye cikin nutsuwa yace”
Alhaji Mahmoud ne kafin Allah ya sako Masa wannan jarabawa a kwanakin baya yabar wasiyar bada auren Sa’adah ga Aminsa AB TURAKI Wanda kasani,
To ita yarinyar yanzu akwai masu neman aurenta da har mun amince anbasu saigashi Kuma Haj Karima takirani akan a dakatar da waincan din sbd yarinya mahaifinta yariga yabada ita ga Amininsa shinefa Muka dakatar da waincan sbd Afaraji ga Turakin idan ya amsa shikenan sai adaura aure abawa waincan hakuri
Idanma akasin hakan aka samu kaga dai anfita haqqin wasiya sai abawa waincan dama sukuma fitowa sai ayi dasu wannan shine taqamaimai dalilin kiranka Alan kazo Dan kuwa Babu Wanda yafi cancanta yabada aurenta Kamar Kai
Hakama Kaine kafi cancantar neman AB TURAKI da maganar sbd ba huruminmu bane mu dangin uwa.
Shiru Kawu saidu yayi Yana jinjina Kai cikin Dan mamakin zancen Yana juya zallar tazara dakuma banbancin rayuwar Dake tsakanin AB TURAKI da Sa’adah din
Saidai tunda Allah Bai haramtaba ba illa bane face qarfafa tare dakuma bawa yarinyar rayuwa Mai kyau a gaba duk da Laylah ce tafi cancanta da hakan ko Dan maraicinta dakuma shaquwar Turakin da mahaifiyarta zaifi Mata riqo na gaske sbd uwarta.
Numfashi ya sauke ahankali Yana sake jinjina Kai ya dago yace”
Babu illa Inshallah zanyi magana dashi saikuyi hanyar da zata hadani dashi din sbd Baya daukan waya sai dace.
Wannan ba matsala bane Inshallah zamu saka lokaci saimuje gabaki daya can Abuja har gidansa sai ayi maganar sbd Inshallah Ana saka ran shigowarsa gobe.
Kawu dai zancen yazo Masa wani iri Amma tunda maganar aurece zaije din bakomai bane dama shine Kamar waliyin su Sa’adah din yanzu tunda mahaifinsu ga yanda Allah yayi dashi.
Da zasu tafi kudi sosai suka bawa Kawun Amma yaqi karba yace bazai karba ba hidimar abinci kawaima da akeyi dashi ya isa.
Haj Karima da umma Jamila sai Alhaji Atiku dasukasan gskiyar lamarin zukatansu cike suke da farin ciki da qaguwa har suka Isa gidajensu
Kawu kuwa dayake mutum ne Mai maimaicin zancen bayan tafiyarsa zaunawa yayi yanata sake juya lamarin har Abdullahi yazo Nan yasake bayyanarda zancen ya Dora da cewa”
Ina shakkar son abun duniya irin na zuriar Zainab idan basune sukeson ingizani Kai zancen wasiyar da babu ba mutuncina da Turaki yake gani ya zube
Dan kuwa Ina mamakin Ta yanda Mahmoud zai bawa Amininsa daya Isa haihuwar yarsa so dubu aurenta batareda laakari da komaiba
Hakama tayaya yake tunanin Turakin zai karba auren Shi Dana mazauniba,hakama baya haihuwa…….
Shiru Abdullahi yayi Yana sauraron Kawun yanason magana Yana Hana kansa
Jin dai Kawun nata nanacin zancen yasashi bude Baki a natse yace”
Dan bada Aure kam Abba yabada aure ga Turaki Kuma yace wasiyace acikamasa ita Amma dai Kam ba Sa’adah ba……
Kawun Bai gama gane qarshen zancen Abdullahin ba yace”
To Allah yasa Turakin yasan da zancen Dan zaifi sauki da mutunci akan nine zanfara tunkararsa da zancen,
Tabbas nasan Akwai alqawarin hada zuria a tsakaninsu saidai ta ‘yaya waya sani Ashe ba yayansu zasu hadaba Matar Turakin ce zata fito ta tsatson Aminin nasa,
Wannan da Laylah ce amaimakon Sa’adah da sainace Rabon aurensa da itane yasa ya tsaya tsayin dakan auren uwarta da ubanta harma shine ya biya sadakin.
Shiru Abdullahi yayi Yana sauraron Kawun kawai sbd fahimtar ba sauraronsa zaiyiba bare ya fahimci zancensa sbd ya tsinke da zance.
Kwana biyu da zancen suka kwasa zuwa Abuja
Suka fara sauka gidan Haj Karima sukaci abinci suka huta tareda salloli sai dare sukai Shirin zuwa gidan Turaki,
Da Alhaji Atiku da alhajin qarami sai Haj Karima umma Jamila dai bata biyosuba sai Kawun.
Da farko ko babban gate din farko da qaton gidan ba’a Bari sun qarasa ba bare shiga ciki su Isa gate na biyu Wanda dagashi sai harabar gidan.
Daqyar Suka samu ganin A Abdoul wanda tashin farko ya sanar dasu cewar Turaki yariga yashige Yana sashen Mahaifiyarsa wadda idan Yana can bamai Kuma ganinsa Dan Yana jimawa sosai daga can Yana fitowa yake shigewa.
Neman appointment din ganinsa gobe sukai ya sanar dasu cewar goben akwai tafiya Mai mahimmanci a gabansa Wanda zaiyi tareda Mahaifiyarsa.
Sunajin hakan Alhaji Qarami yace”
Idan harda Haj Anne zaiyi tafiya Inshallah ba tantama gurin duba Mahmoud zasu tafi sbd Babu zuwan dayake batareda itaba itama ta dauka Mahmoud tamkar ‘da.
Duk da hakan Dan karsuyi tsammanin daba shiba
Kawu ya kalli A Abdoul cikin nutsuwa yace”
Kayi hkr ka kirasa a waya kokuma kakira Haj Anne a waya kace Kawu saidu ne na Mahmoud.
Shiru Abdoul yayi Yana ganin girman Kawun sbd Kiran kansa da yayi a Dan uwan Alhaji Mahmoud Wanda yariga yasan irin Aminci Mai girma dake tsakanin Alhaji Mahmoud da Turakin duk da daga baya yasan labarinsu shida Turakin
Ta wani bangaren Kuma Yana jinjina tsari da kaidar Turaki Dan Haka ya kalli Kawun cikin Yar mutuntawa yace”
Kayi hkr Kawu gskia bazaku samu ganinsaba daga yau din har goben,
Amma idan har Yan uwan Alhaji Mahmoud ne ku taimako daya dazan bada shine ku koma gida ku jirasa sbd zuwansa duba Alhaji Mahmoud kamar kaidace da baya takewa.