NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL
NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL BY MAMUHGEE

Anne tafiyar datai kwanaki tareda Turaki da zankada zankadan ‘yan Mata biyu tadawo masu tsananin kyau musamman dayar wadda da alama itace qarama
Kuma Kamar dai ba lafiyayya ba likita gareta kullum sai anzo gurinta
Hakama da alama Anne na tsananin sonta Dan ko yanda take Kiran sunansa a zaka gane,
Saidai babbar naga Kamar su halima sunfi bawa girma da alama itace kila Anne zata……
Kasa qarasawa tayi sbd mummunan tarin daya sarqe Ms Na’ima cikin tsananin firgici da baqin ciki tareda zallar mamaki.
Ruwa ta miqa Mata da sauri tana cewa”
Sannu,kiyi hkr bansan zancen zai damekiba Haka ba.
Ruwan tagama Sha tana kallon siddikar da jajayen idanuwanta da tari dakuma tashin hankali suka sauyasu ta aje ruwan tana cewa’
A Ina suke zaune?
Me kikaji Annen ta fada akansu?
A Sashen dake maqale da Annen Wanda yake kusan hade da nata,
Ita qaramar wadda sunanta Laylah ita naji Kamar Annen nata yabont kamanninta da Matar Aminin Sir Turaki wadda ta rasu
Itadai inaga riqo ta dauko ta sbd Yar Aminin Sir ce Wanda duk yazo kike cewa Yana zuwa dubosa
Dayar ce dai bansan komai akanta ba shiyasa nake zargin itace wadda Anne ake cewa zata aurowa Sir Dan Bayan sun dawo agurin securities na gate din farko naji kamar Suna maganar an dauro aure da sir wallahi Amma ba tabbatarwa nay…..
Wani irin dannewar kirji takeji ta dagawa siddika hannu tana cewa”
Ya Isa kafin ki kasheni
Dama ke bana samun labarin alkhairi daga gareki kullum Kika fara bani rahoto sai ciwon zuciya ya kamani.
Shiru siddika tayi tana sake miqawa uwar dakin tata ruwa Aranta tana cewa”
Kekikace komai da komai na ringa fada Miki.
Miqewa Ms Na’imah din tayi tadawo Palo tana kokarin zama jikinta na rawa sbd duk mugayan labaran da siddika me kawo Mata rahoto a gidan ba kamar wannan,
Wani zafi da ciwo takeji cikin zuciya da jiki,
Ta yarda tabbas dama daga Anne har Turaki zasu qaunaci ‘yar Mahmoud sbd tsananin kaunar Dake tsakaninsu Dan Haka Dan Andauko Yar Mahmoud riqo ba matsalarta bace Dan itama tasan Dole zata nunawa ‘yar kauna da janta ajiki ko Dan wannan sabuwar hanyar kame Turaki da Anne ne takara samun durmiya cikin dukiyar gidan,
Babbar matsalarta da baqin cikinta tareda takaicinta da damuwarta shine ‘dayar da siddikar ke magana wadda tasan tabbas da wata niyar Akan Turaki Anne takawota gidan.
Kallon siddika take kallonta tana jiran tagama fitowa tashin hankalin data Shiga tayi tace”
Me sunan dayar Dan kuwa yanzu Kai tsaye zanje na tambaya Dan bazan taba yarda da wannan rashin kauna da kashe Jin dadin da koyaushe Anne keson yimun ba,
Kafadamun komai da kikaji Kika sani,
kinzama Mara amfani ko kadan da zakice mun bakida tabbaci,
Meye amfaninki a gurina idan bakya da tabbaci akan duk wani Abu da kikaga alamar cutace gareni Zinat zankira nafada Mata bakida wani amfani tazo ta tafi dake…
Cikin rashin abin cewa da fadan Uwar dakin nata data Gama Shiga tension da tabbatarwa siddika ta hada zancenta Dan bawa Ms Na’ima data Gama Hawa sosai sbd itakam ko a mummunan mafarki bazataso barin gidan Amb Turaki ba Dan Haka tace”
Dayar matarsa ce anriga an daura aure Kuma saboda ‘yar riqonsu da suka dauko aka aurota Dan ta kula da ita ace hannun matarsa take Kuma duk Dan sbd basuda magajin gidan ne yanzu itace magajiyar Anne da Turaki……
A haukace Ms Na’ima tace”
Da dafarko ubanwa ya Hana ki fadan komai Kai tsaye kike fadamun Baki tabbatarba?
Siddika Allah ya kwashe Miki da wannan mugun labarin naki
Wallahi bazan yarda ba
Da anbani rikon ne ban karba ba daza’a auro wata kawai sbd riqo
Dan ita datai riqon ta riqe harda tarin dukiyar da za’a bawa yarinyar kenan
To idan hakan ne ai nice nasan taren Mahmoud din da Turaki..
Miqewa tayi ranta na tsananin Kuna zata give daga palon saiga Kiran Haj Zinat wadda siddika takira daga Nan inda take tsaye Dan itace kawai Mai iya dakatar da Ms Na’ima idan ranta ya baci idanuwanta rufewa sukeyi.
A matuqar hasalce ta daga wayar
Haj Zinat tace”
Karkije koina yanzu Yi zamanki gobe da wuri zanzo gidan musan abin Yi
Kinsan siddika munafuka ce karki hau zancenta duka kiyi abunda Zaki qarasa Bata kanki agurin Anne tunda dama ba wani Yinki takeyiba,
Idanma duka gaskiya ne ai a ruwan sanyi Zaki qwace riqon yarinyar Mahmoud din tadawo hannunki mu taru mu ringa nuna Mata gata da kauna
Kinga a sauki ga babbar damar mamaye zuciyar Annen dakuma ogan Mai gaba daya
Idanma tafiyarki tayi USA gurin Turakin sakata gaba Zakiyi kije da ita can danma yagani da idonsa yanda kike tsananin kauna da kulawa akan ‘yar tasu.
Haka Zinat tayita lallaba Ms Na’ima din harta fasa zuwa Sashen Amaryar bawai Dan ta sauko ko taji sassauci ko kadanba a ranta saima wani sabon zafi da tiririn datake ji tayi hanyar bedroom dinta tashige tabar siddika na Mata Saida safe cikin girmamawa.
Saida tashige siddikan ta juya ta nufi dining tafara kwashe kayan Kai tana gyarawa saiga Kiran Haj Zinat
A ladabce ta dauka tana cewa”
Eh tashige Bata tafin ba.
Siddika abinda Kika fada kin tabbatar dashi?
Idan kikai qarin zance Dan ki Kare kanki daga Na’ima Ni karkimun qarya fadan gskia.
Sanin daga Haj Zinat har Ms Na’ima halinsu daya sbd Aminin gske ne yasa takuma fadar abinda tafadawa Ms Na’ima din Dan ko gskiyar tafada musu cewa batasan komai akaiba ba yarda zasuyiba karshema Mara amfani zasu kirata Kuma tsaf zasu iya korarta su sauyata duk da dadewar datai Mai tsayi ataredasu shiyasa duk lokacinda taga gskiyar zance Bata fiddataba abinda tasan shi sukeson rahotonsa take hadawa ta fada shiyasama takawo har tsawon lokacin ataredasu sirrinsu Babu Wanda bada Bata saniba Dan itace Yar aiken sirrinsu.
Washe gari qarfe goma Sha daya Haj Zinat ta iso gidan Nan suka Gama Yan sirrance su suka fito zuwa Sashen Annen Dan gaidata.
Zaune Annen take a babban palonta tana waya da Turaki Wanda yatafi Zurich wani aikin Yana waya da Annen cikin nutsuwa da kamewarsa duk da Mahaifiyarsa sosai take mutunta Dan nata so da Dama sbd mutum ne Mai haibar cika ido har nata ita Annen nasa.
Cikin girmamawa suka qaraso Suka zauna masu Aikin Sashen Annen suna gaida Ms Na’ima din a matuqar girmame tana amsawa batareda ta kallesu.
Saida Annen tagama wayar ta ajiye gefe ta kallesu fuska a sake tace”
Zinat kina gidan kenan?
Eh Anne yanzune shigowata nace kafin nashige gurinta Bari nazo nafara gaidake,
Barka da Rana Anne?
Barka Zinat ya iyali?
Alhmdlh Anne.
Cikin girmamawa Ms Na’ima tana kallon Annen a ladafce tace”
Anne barka da Rana?
Jiya cikin dare na iso shiyasa ban shigoba sbd lokacin nasan kin shige bakya fitowa.
Murmushi Annen tayi irin nasu na manya tace”
Bakomai ai
Ga gajiyan tafiya dama kin debo
Allah a muku albarka duka to.
Firar rashin makama Ms Na’ima ke Dan yiwa Annen cikin girmamawa
Annen na tankawa ahankali tana duba sakon wayarta na Admission din Sa’adah daya fara samuwa kafin na Laylah da sai anhada da Mai sake koya mata wasu abubuwan.
Ms Na’ima na cikin magana Laylah tashigo palon sanye cikin Riga da skirt na Grand super red data fitar da yanayin shafaffen cikinta da tudun kirjinta sai hips dinta dasuka Dan fito
Dayake dinkunansu kaf a anan Abujar ake musu komai daidai jikinsu ake musu fuskarta fayau sai Hasken fatarta Dake qaruwa kanta red turban hula ce da Bata rufe duka ba sai qamshin turaren Valentino Donna takeyi Mai sanyin dadi…