NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL BY MAMUHGEENOVELS

NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL

NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL BY MAMUHGEE

Wuta Ms Na’ima ta dauke tana hadiye wani mugun yawu tareda Dan rikicewa da abinda take fada idanuwanta gabaki daya Babu wani basarwa ta zubasu akan Laylah wadda Bata lura dasu ba hanyar kicin ta nufa gurin aikin abincin ranar data barwa halima ta duba Mata.

Haj Zinat kanta sakin Baki tayi tana kallon Laylan mamaki na neman kashesu,
Duk kyau da wayewa tareda budewar ido irin nasu na tsoffin Yan duniyar dasuka Gama bude ido a yawan Jin Dadi da daula Saida Suka tabbatar ba kushe yarinyar kyakkyawace.

Zuciyar Ms Na’ima bugawa take neman Yi ba shiri ta bude Baki Yana rawa zatai magana cikin yanayinta duk ya sauya zuwa firgici Haj Zinat tayi saurin Kai hannu zata dafeta sai Anne ta rigata da Kiran sunan Laylan Kai tsaye.

Da sauri suka waiwayo suka kalla Annen atare lokaci daya suna sake maida kallonsu Kan Laylah
Take wata boyayyar Ajiyar zuciya tazo musu Ms Na’ima na sake maimaita sunan Laylan a fili
Haj Zinat kuwa sakin fuska tayi sosai tareda sakin wani faffadan murmushi tana cewa”

Masha Allah yarinya kyakkyawa
Anne baquwa kikai n….
Bata qarasaba Ms Laylah ta saki zancen dayasa Anne kallonsu da idanuwanta cikin boye mamakinta Jin Ms Na’ima na cewa”

Itace Laylah Yar Mahmoud da aka dauko Mana sbd ba yara gidan….

Tsit Haj Zinat tayi cikin tsananin takaicin Aminiyar tata da koyaushe Bata iya danne zance ko boyewa shiyasa komai nata yake gashinan idan badan itabama da yanzu ba sauran labarin Na’ima a gidan Turakin wlh.

Boyayyan tsoki taja cikin ranta na takaicin Na’ima Amma a fili washe Baki tayi tana sake Kiran Laylah cikin bayyanarda kauna afili tace”

Masha Allah
Sannu da kokari Anne wlh Kam anyi dabara gida da yara yanada Dadi
Gashi dama Na’ima nata tunanin samun Dan dazata riqe ai shikenan an huta.

Murmushi Anne tayi sai kawai tace”

Eh ai yanzu gashinan mun samu qarin yarinya cikin gidan
Saikuyi addua daga kan yarinyar Allah yabude Mana haihuwa a gidan yara suyita zuwa masu albarka.

Amin suka amsa bakunansu daukeda murmushi kafin cikin kulawa Anne ta kalli Laylah data qaraso gurin tace”

Laylah ki gaida manyanki,
Matar Turaki ce da kawarta.

Cikin ladabi ta bude Baki da muryarta Mai sanyi ta gaidasu.

Ms Na’ima tayi saurin cewa”

Anne Laylah nada nutsuwa gskia
Amma dai gurina zata zauna ko?

Murmushi Annen tayi tana cewa”

Zaki iya rikon nata ne?

Anne akwai Wanda yakamata yayi riqon wanda yake matsayin ‘da tamkar ‘Dan da Turaki ya Haifa Kamar ni?
Inshallah Zan kula da ita nabata gata tamkar nida Turakin ne muka haifeta.

Cikin wani yanayi na ganin wautar Na’ima Anne tasaki murmushi tana basar da zancen da kallon kofar da Sa’adah ta fito tana sanye da doguwar rigar lace din daya kwanta baida nauyi ko kadan sbd kudinsa pink kala
Dayake tafi Laylah son kyale kyale harda siririyar sarqa a wuyanta Mai kyau gashi girmanta akan Laylah Ana Dan ganewa sbd jiki datafi Laylah.

Kallon Sa’adah Ms Na’ima tayi dakyau ta tabbatarda itace kishiyar tata wadda ta kutso rayuwarta da abinda tafi so da kauna a rayuwarta wato kudi da Turaki,
Itace wadda takawo kanta acikin masifar da batasan kalar hadari da girmanta.
Dauke Kai tayi tai kamar bata ga Sa’adah din ba Dan kuwa wannan Koda Bata Isa haihuwarta ba ta Isa yin qanwar qarshe sosai da ita,
Dan wannan ma tasan auren Anne ne tayisa Amma Turaki ko ita datake macen data Gama zama mace tako Ina ga kyau ga jiki Mai Kyau da ilimi da wayewa da komai Bata Gama zama shi yazama itaba bare wannan da da ita da wannan Yar Laylah bawani banbanci.

Haj Zinat ma Yi tayi kamar bataga Sa’adah din ba wadda ganinta yasa sukaji duk zafinsu ya rage sbd Dan wannan ba abun daga hankali bane Dan kuwa ba lallai ma Turakin ya dauketa mace ba saidai ‘ya ko Yar riko.

Anne dataga basarwar dasukaiwa Sa’adah data gaishesu cikin mutuntawa tana satar kallon Ms Na’ima da akace Matar Turaki duk sai jikinta yake neman mutuwa Dan kuwa a kallo daya tasan Ms Na’ima ba qaramar mace bace ga kyau ba laifi ga gayu da komaima.

Laylah dama ta wuce kicin tuni Dan Haka itama tana gaishesu kicin din ta nufa
Ko bayanta Babu Wanda yasamu damar bi da kallo sai Anne data kalli Ms Na’ima tace”

Dukkaninsu tamkar ‘yaya suke gareni
Zasu zauna damu har abada Inshallah ‘yar riqona da aure kawai zai rabani da ita Amma dayar kamar yanda Naga alamu sun nuna kinsamu labarin Matar mijinki ce
Turaki Bai fada Miki bane sbd shima Kai tsaye auren yaxo
Kuma ninace yabari Zan sanar Dake saigashi Kikai zamanki Lagos sai yanxu da Kika dawo
Dan Haka Kamar yanda Kika gani yarinyace qarama akanki sosai
Ina fatar bazaki wani damuba Zaki zauna lafiya da ita kamar yanda na tabbatarda zata Baki girmanki sosai.

Zinat tasake fadawa tasake yiwa qawar tata nasihar zama da kishiya musamman Miji irin nata da baya kaunar fitina ko kadan.

Murmushi Haj Zinat ta nuna bakomai ai tunda ma yarinyace Kuma ma ai kamar ba guri daya suke zauneba.

Da wannan suka tashi suka baro Sashen Annen harda Kiran Laylah Haj Zinat tayi sukai sallama cikin kulawa
Anne dai Bata sake bi takansu ba.

Bayan futarsu Ms Na’ima wasu hawayen baqin ciki da takaici ne suka silalo Mata dan tagama tabbata dai Kishiya akai Mata
Turakin da Bata taba dandana kayantaba shine za’a kawo Mata Kishiya Dan Yana samun lafiya arasa waye zai fara samun rabon dashi.
Wlh bazata taba yarda da wannan dakon wahalar datai ba
Ba Sa’adah ba ko uwar Sa’adah ce bazata Bari ko inda inuwar Turaki take ta kusanta ba bare harya ringa tunawa da ita da wani aurenta.

MAMUH

pay 300 @+234 903 234 5899

Mamuhgee’s complete books

Deen Marshal
Ubayd maleek
Min qalb
Kaunarmu
Buri daya
Tarayya
Eznah
Dawood
Zucuyarmu daya
Daiman
Auren raba gardama
Dacewa

Duka completes dinsu suna AREWABOOKS @Mamuhgee
[7/10, 9:25 PM] +234 704 076 8969: Mamuhgee 18
Duk yanda takeda sani ba laifi akan kayan gidajen masu kudi yanzu sbd rayuwarsu ta Abuja Nan Saida ta Raina kanta dan komai na gidan wata rayuwace daban,
Toilet din komai nasa tsarinsa daban yake Dan Haka Saida Siddika ta hada Mata komai na ruwan wanka masu dumi sosai tayi wanka ta fito sanyesa white bathrobe wadda Zata shiga toilet din aka kawo matasu sabbabi ajere kusan guda biyar kala daban daban saidai dukansu ba wasu masu tsayi bane Dole ta Sanya ta fito har lokacin siddika na dakin tana qarasa jera Mata kayanta a closet Wanda Basu wani da yawa Dan Ms Na’ima Bata barta tazo da wasu kayan ba sai anzo Nan.

Koina dakin yadauka qamshin Untrasonic Humidifier dake aiki sai sanyin AC da siddika ta rage Mata sanin akwai zazzabi tareda ita.

Kan couch ta zauna ta jira siddika tagama jera kayan ta fice kafin ta miqe jiki amace ya dauki wata doguwar English gown da siddikar tabar Mata Kan gado tasaka sai qaramar hula Mara nauyi
Cikin qarfin hali tayi sallolinta da aka nunar da ita gabas tana gamawa zazzabin yaci qarfinta sosai ta kwanta agurin kenan saiga saqon zuwan dr Dole ahaka saddika ta kamata suka fito zuwa main hall na gidan ma’ana babban palon farko.

Kallonta Dr Noah yayi anatse kafin yafara mgna da ita saidai ganin maganar bazata yiyuba sbd Bata Gane abinda yake fada sai kawai ya taba duba temperature dinta da sauran abinda yakamata ya Bata magunan dasuka kamata ya tafiyarsa.

Bedroom dinta aka maidata tareda Kai Mata black tea Mai zafi Tasha sosai kafin Tasha magani take bacci ya dauketa siddika ta rufeta da abun rufa Mai tsakanin taushi aka rufo Mata dakin ta nufi nasu dakin na maids tana sauke ajiyar zuciya a gajiye Dan tunda suka iso Bata zaunaba sai yanzu zataje ta huta tayi nata sallolin.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button