NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL
NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL BY MAMUHGEE

Dayake baccin zazzabi ne sai yamma sosai ta tashi da Rashin qwarin jiki Amma dai zazzabin ya saketa Dan Haka tana farkawa dmta tashi zaune cikin sanyi tareda zuro qafafuwanta qasa ta sauko ta miqe tana nufar toilet ta shige.
Wani wankan da alwala tayo ta fito jikinta na sakewa da samun qwari Dan Haka Kai tsaye sallah tafara Yi kafin ta saka wata doguwar rigar Mai hannuwa Dan ta dazun qaramin hannune da ita Takoma ta zauna Kan couch tana jingina tareda rufe idanuwanta tanajin kewar mutanen data Saba dasu a rayuwarta Wanda ayanzu Anne tana ciki sbd ko ahalin data shiga na yanayin lafiyarta ta shaidar da girman kaunar Anne gareta Dan Haka take sake Jin girman Anty Sa’adah a zuciyarta sbd duk itace ta Bata wannan kyakkyawar rayuwar tunda gidan Aurenta ne ita Anty Sa’adah din.
Tana zaune agurin cikin tunani har tsawon lokaci saiga siddika tashigo dauke da manyan varieties na turarukan Zubawa a humidifier Dake dakin ta jeresu tsaf a inda ake jerawa ta fice Bayan ta sanar da ita anjima zata fito cin abincin dare tareda su Ms Na’ima Dan Haka saita shirya,.
Wasu turarukan tafita takuma shigowa dasu kala daban daban masu tsananin tsada ta jere agaban makeken madubin dakin tana sake sanar da ita koina na gidan basa Wasa da qamshi sbd Mai gidan da zasu zauna guri daya dashi anan gidan.
Sai alokacin ta Dan dago fararen idanuwansa daga zaunen ta kalli siddika da farar baturiyar Dake tayata shigowa da kayan dasuketa shigowa dasu wainda online shopping ne akai Mata masu delivery suka kawo.
Anty Sa’adah na can mijinta na Nan daban
Dama Haka zasuyi rayuwar auren? Kokuwa Dan antyn tana karatu ne
Dan Kam zaman kishi da irin Ms Na’ima Dole a taimakesu anty Sa’adah tayi karatu Mai zurfi sbd samun damar nutsuwa dako wane irin al’amari zaman zai kawo duk da tana jinjinawa Ms Na’ima wani bangaren da batada Kishi ko fitina har tana iya daukar riqon qanwar kishiyarta da zuciya daya Dan Bata taba nuna mata wata fuskar ba bayan ta kulawa da kauna saidai duk girmanta da mutuncinta data gani har abada bazata Kai Mata ‘yar uwarta agurinta ba.
Da daddare bayan tagama sallar ishai tana kokarin kwantawa duk da yunwar datake ji saiga knocking kofar dakin ahankali cikin nutsuwa dake nunin ba’a son damunta da bugawar.
Batace komaiba Saida aka Kuma bugawa ta sauko gadon ta nufi kofar ta bude a natse tareda kallon farar baturiyar dasuketa aikin hidimarta dazu da Siddika.
Kallonta tayi da fararen idanuwanta kafin ta Dan sauke idanuwanta tana sauraren abinda take fada Wanda bayan come da waiting in dining room Babu abinda ta fahimta acikin kalmomin Dan turancin yamata tsauri musamman dayake turancin na asalin baturiya ne Dan Haka tunda Bata da wani abun cewa a natse ta saki kofar tabi bayanta cikin nutsuwa.
Doguwar rigace ajikinta Mara nauyi Mai Fadi sosai wadda fadin nata da rashin nauyin material din rigar yasara kwantawa ajikinta sai hular kanta ta bacci mara girma sosai da Bata rufe gaban gashintaba dayake kwance cikin zallan gyaran dayakesha a Abuja Dan kuwa anty Sa’adah da qarfi da yaji Takoma Kamar Mai saloon dinta.
Suka nufi hanyar dining room din Dake palon kurya na hanyar hayewa sama asalin palonsa da master bedroom din Mai gidan.
Daga bakin kofar shiga Cindy ta Dan dakata tareda bata hanya tana nuna Mata tashiga,
Kallonta Laylah tayi kafin takalli kofar data iya jiyo qamshi na musamman na tarbonsu tun daga Nan din,
Jin tayi zuciya na neman shiga rawa sbd ita daza’a barta dakin dayafi Mata
Sam Bata Saba da irin wannan rayuwar ba.
Sake nuna Mata kofa Cindy tayi Wanda yasata daga qafafunta ahankali ta shiga tana kokarin sauke kanta Dan kuwa tana saka Kai akan farar kamilalliyar fuskarsa Data cika palon da kwarjini idanuwanta suka fara sauka.
Zaune yake Kan dining din Kan kujerar Dake saiti da kofar shigowa wadda itace asalin kujerarsa dayake zama cin abinci,
Sanye yake cikin wata black jallabiya da farar hular sallah gabaki daya qamshinsa na Bois Elite ya cike dakin cin abincin
Ms Na’ima na zaune Kan daya daga cikin kujerun dining din itama sanyeda doguwar Riga mara dogon hannu fuskarta ba kwalliyar komai sai lipstick data Dan lura so da dama kamar Yana burge Turakin tunda dadewa sbd duk ranar datasha lipstick Yana Dan yawan kallonta saita dauka hakan da duk suna guri daya lipstick baya rabuwa da bakinta sai idan bacci zatai kokuma tashinta da safe kenan batai wankaba.
Qamshin body mist dinta na Perry Ellis ne yasa Ms Na’ima waiwayowa kofa ta kalleta fuskarta daukeda yanayin damuwa da kulawa tace”
Heyyy Laylah qaraso zo ki zauna
Yaya jikinki?
Kinji sauki da kikasha magani kuwa? Kodai asake Kiran Dr yadawo?
Dagowa yayi ya zuba Mata idanuwansa akaro na farko daya fara ganinta gabansa Dan kuwa tun tana jaririyarta rabon daya Kuma ganinta,
Dogon hancinta zuwa idanuwanta da yanayin jikinta gabaki dayanta yake kalla Wanda tsaf tanajin kallon na yawo akanta Dan Haka sai takasa daga qafafuwanta ta qaraso taja ta tsaya da inda take tsaye zuciyarta na Dan bugawa da rashin sakewa dakuma tsoro harma da shakkar kallo Dan duk abubuwane wainnan gabaki daya da Bata Saba da subaba.
Tasowa Ms Na’ima tayi ta qaraso inda take tareda Kama hannunta ta qaraso da ita tana kallon Turaki Wanda ya maida hankalinsa Kan abincin da aka gama zuba Masa ya saka spoon yafara ci cikin nutsuwa da kamewa tace”
Laylah ki gaida dadynki kafin ki zauna muci abinci ko.
Turaki dama Suprice naso baka shiyasa ban fada maka tareda Laylah zanzo ba
Karatu nakeson tayi anan Dan inason tasamu ilimin dayafi na makarantannin Nigeria sbd gaba idan zata riqe matsayi masu girma a companies dinka”” taqasa fada fuskarta daukeda farin ciki da murmushi Mai yalwa.
Dan dagowa yayi yayi mata kallon seconds biyar na mamakinta Yana tabbatarwa da kansa tabbas batasan matsayin Laylah ba agurinta Amma dai koma tasani ko batasaninba baya tunanin hakan nada amfani Dan kuwa ayanzune ya sake tabbarwa da wannan auren Kamar wani riqone agaresa Dan kuwa Babu ta yanda zai iya kallon ‘yar cikin Mahmoud da Zainab amatsayin Mata,
Alaqar aure da ita Kamar abune daya Riga ya haramtawa kansa
Zamanta a matsayin Yar riqo garesa kamar yanda Na’ima tadauka
Da kansa zai aurar da ita Inshallah idan lokacin hakan yayi.
Cikin wata irin sanyin murya da nutsuwar dake bayyanarda rashin sakewarta agurin ta furta”
Ina wuni.
Gyada Kai yayi Kai tsaye Yana cewa”
Seat.
Zaunawa tayi a darare tanajin duk girmansa ya cika gurin Dan Haka sama sama taci abincin Wanda dama Bata iya cinsaba Dan macaroni salad ne sai baked potato da fresh fruits masu sanyi kadan.
Ita tafara gamawa Amma takasa barin gurin Saida yagama ya miqe yabar dining din Yana yimusu Saida safe cikin sautin girma da kulawa.
Yana fita Ms Na’ima tasake zuba Mata abincin Wanda tasata ci Dole ahakan kuwa cikinta ya cika ba laifi kafin suka baro dinning din zuwa Palo Ms Na’ima na janta da zantukan yanayin qasar da rayuwar gidan
Dayake zuwa yanxu tasaba da yanayin Laylan sai rashin tankawarta sosai baya damunta tunda tasan hakan Laylahn take.
Saida bacci yazowa Laylah sosai kafin Ms Na’ima tabarta ta nufi bedroom dinta tayi Shirin bacci ta kwanta
Take bacci ya dauketa sbd koshi da gajiya.