NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL BY MAMUHGEENOVELS

NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL

NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL BY MAMUHGEE

Washe gari da safe data Gama tabbatarda sake kiranta za’ai gurin Cin abincin safe Dan Haka saita lafe taqi nuna ta farka duk yawon kiranta da Cindy taringa Yi Dole aka barta sbd lokacin Turaki ya sauko harya zauna cin abinci
Yana gamawa ya fice.

Sai qarfe goma Sha daya ta nuna ta farka ta tashi tayo wanka tuni akai Mata nata abincin aka Kai dining ta fito Dole sanye da farar chiffon lace blouse da blue palazzo kanta daureda qaramar veil fari fuskarta ba komai bayan glowing na savor beauty moisturizer Babu abinda takeyi
Kai tsaye dining room din Cindy ta nufa da ita agaba tana binta.

Ba laifi abincin da akai ta iya cinsa sbd pancakes ne da Black tea sai soyayyan kwai da potato chips.

Tana gamawa daki Takoma tayi zamanta cikin kadaici da kewa.

Da yamma Dr Noah yasake dawowa yaduba yanayin jikinta ya tabbatarda tasamu lafiya saiya tafiyarsa.
Haka ta wuni ba wani abin Yi ko abokin Hira har dare takuma dojewa fita cin abincin Amma da Rana dayake akwai Dan sani da sabo tsakaninta da Ms Na’ima taje sunci abincin Rana tare a dining din.

Washe gari Bayan fitar Turaki A Abdoul yasakawa Ms Na’ima wasu irin maqudan kudi na siyayyar Laylah da har anshigar da maganar sakata makaranta,
Dadin duniyane yafara cika Kan Ms Na’ima ganin tafara morewa riqon Laylah tun baaje koinaba Dan kudin da aka batan idan siyayyar haukar me zataiwa Laylah bazasu cinyesu Dan Haka Laylah Nagama breakfast Ms Na’ima na jiranta cikin Shirin doguwar Ashape gown ta chiffon Mai tsadar gaske suka fita cikin daya daga cikin manyan motocin gidan.

MAMUH

Follow me at Arewabook @mamuhgee Dan samun complete books Dina dama sauran pages na Noor Albi Dake fara sauka acan.

????????
Eznah
Tarayya
Deen Marshal
Ubayd maleek
Min qalb
Buri daya
Kaunarmu
Noor Albi
Dacewa
Dawood
Zucuyarmu daya
Auren raba gardama
Taura biyu
[7/10, 9:25 PM] +234 704 076 8969: Mamuhgee 17
Duk yanda Ms Na’ima taso Kar tayi kishin Sa’adah kasawa takeyi saidai kamar yanda Haj Zinat ta fada Mata dannewa kawai takeyi Bata wani nunawa saidai ko inda Sa’adah take Bata kalla sbd duk iya qanqantawa tagama daukan Sa’adahn a qasqance ganin harda ilimin boko Mai qarfi sosai Bata dashi Dan Haka sai sukafi maida hankali akan Laylah wadda cikin kwanaki kadan Ms Na’ima din tagama fahimtar irin kaunar da Anne ke yiwa Laylah ga laylan nada wuyar sakin jiki da mutane Dan Haka tuni ba itaba ba Haj Zinat ba suka maida hankali sosai Kan nunawa Laylah kulawa Sosai,
Musamman Ms Na’ima ke janta ajikinta tana Mata siyayyar kayan Yan gayun ‘yan Mata ‘yayan manyan duk da Anne Babu abinda Bata siya musu na duk Wani abun buqata Amma dayake Ms Na’ima wayayyar Yar gayun gaske ce sai siyayyar datakewa laylan yana sake wanke Laylan
Anne said kawai takawo ido tasake sakawa Na’ima Dan tagama gane manufarta ta son abata Laylan Dan samun damar data fi wadda take da ita yanzu Alan dukiyar Turaki,
Murmushi kawai takeyi na ganin wautar Na’ima so da dama idan taga yanda suka taqarqare akan Dole qaunar Laylah sukeyi ba
Kuma ganin rashin sanin zaisa bazata taba cutatar da Laylahn ba ayanzu Dan Haka saita bar komai ahakan yanzu saima tabada fuskan da Ms Na’ima din ke daukan Laylah tana fita da ita.

Laylah Bata sakewa da Ms Na’ima Sam ko kadan sbd sanin matsayinta na kishiyar Sa’adah batason jawowa Sa’adah matsala sai Anty Sa’adah din ta nuna Mata bakomai ai hakan shizaisa azauna lfy kowa da kowa,
Da Haka Ms Na’ima taja Laylah sosai jikinta har Dan Dole Laylah tafara sakewa da ita Dan har cikin ranta so take ta cusa qaunarta Mai qarfi a zuciyar Layla ta yanda zata dauketa tamkar uwa tako Ina yanda Turaki zai sake musu komai yanda yakamata tunda ta rungumi ‘yar Kamar ita ta Haifa.

Sa’adah tafara zuwa makaranta tuni a one hundred level takuma farawa tana karantar Biology
Kuma ba laifi tafara sabo da makarantar da ‘yan friends din data fara tsirarru ga uwa uba surutu da manyan designers Kaya data duka
Ga hankalinta tuni yagama kwanciya Dan Laylah tasamu lafiyarta cikakkiya itama karatun zata fara Amma Ms Na’ima ta dage akan ita baza’a sakata anan Abuja ba da ita zata tafi USA acan zata sakata karatun kafin su tashi dawowa Laylan tagama Inshallah idanma harta tashi dawowan Laylah Bata kammala karatun ba zata jirata ta kammala kokuma tabarta acan tadawo tunda Turaki na can ga maids a gidan Kuma.

Da wanna ba musu Anne ta Amincewa tafiya da Laylan wadda da farko ta daga hankalinta Amma Sa’adah ta lallasheta tareda sanar da ita Anne tace acan kusa suke da gurinsa Abba zaa ringa kaita tana dubo Abba da Momy tarea Bata qwarin gwiwar karatun shine zai tallafi rayuwarsu data iyayensu Inshallah Dan Haka badan tasoba Haka ta amince musamman da Anne ta zaunar da ita ta rarrasheta Akan Turaki nacan Dan Haka kartaji tunda yasan matsayinta akansa na dolenta.
Hakama dai maganar ganin abbanta shine yafi komai Bata nutsuwa da tafiyar wadda takasa gane dalilin dayasa Ms Na’ima ke sonta Haka Bayan ita din qanwar kishiyarta ce Amma idan ta tuna wasu daga nasihun Anne sai tana yadda da akwai sauyin da Allah ke kawo maka na rayuwa da basai ka tsaya wani tunaninba Bayan gode Masa.

Da wannan aka hau Shirin tafiyarsu USA, Ms Na’ima farin cikin tafiyar takeji sosai musamman ta kalli Haj Zinat tana zare siririyar sarqar white gold din Dake wuyanta dasuka dawo daga Gama harhada bayanan komai na manyan stores data barwa babban ‘dan Haj Zinat ragamar cigaba da kulawa da komai tace”

Zinat kisake yiwa siddika sabuwar huduba sbd tana min hauka acan ko kudin ticket din dawowa bazan siya Mata ba Zan korota
Dan kuwa banason duk wani abun damuwa ko ciwon Rai acan
Hutawa najeyi da mijina.

Murmushi Haj Zinat tayi tana aje wayarta data Gama amsawa tace”

Idan hankalinki Bai kwantaba da haukarta ki barta Mana a samo wata kije da ita.

No zuwa da itan zaifi sbd Laylah da ita tasani zatafi Jin dadi idan akaje da Mai Mata hidimar data sani tun anan sbd Kinga turancin ba wani jinsa takeba Dan Haka masu aikin can zasuyi Mata wuyar muamala shiyasa sbd ita kawai zanje da siddikar.
Dan Haka idan tamun abinda zai sakamun ciwon zuciya ratayeta zanyi kowama ya huta” taqarasa fada da Dan takaicin halayen siddikar duk da sune suka sakata ta gwane a munurfin da gulmar Dan kawai dauko musu kowane irin zance.

Dan gyara zama Haj Zinat tayi cikin Isa tana cewa”

Laylahn ma sai anyiwa Siddikar fadan kiyaye abinda takeso da Wanda bataso Dan zata iya kwafsawa tunda munafurci kawai tafi gwanewa akai.

Wani lafiyayyan murmushi Ms Na’ima tayi tana daukar face wipes taqara da Neutrogena makeup remover akai tafara goge fuskarta tana cewa”

Duk halinta zatai tabari ne Dan kuwa amfanin dagewa da tafiya da Laylah shine Zan fake da karatun nata naqi dawowa Dole yanzu zamu zauna Kamar kowanne ma’aurata gani gashi a gida daya qari ga ‘yar riqo duk ihun Anne da damuwarta Akan rashin haihuwa dai yanzu Zan huta tunda burinta yacika ta aura Masa gagari
Dan kuwa ko ganinsa ita Annen bazataiba bare juyayyar Matar da aka aura masan saidai taqaraci karatun bokonta tagama tayi gaba tasamu bokon koshi taqaru dashi taje tasamu wani mijin Turaki Kam bana yara bane
Ita kanta dataji komai ta Isa Bata Gama saninsaba bare wadda ya Isa haihuwa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button