NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL BY MAMUHGEENOVELS

NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL

NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL BY MAMUHGEE

Dama duk tsanani Kam karkiyi sake yadawo Baki Gama sakashi a kwana ba da kisisina da komai
Tunda gaki da ‘yar Mahmoud a hannu kowa yasan irin Aminci da qaunar Dake tsakaninsu Dan Haka kinsan tunda suka dauko yarsa duk Wanda ya sota shine nasu
Tunda gashi yanzu Anne Tadawo tana sake Miki sosai sbd Laylan Dan Haka Turakin ma karkiyi sake
Gwara ki nuna Masa da gaske kike kece uwarta yanzu.

Wani murmushin tayi kawai batareda tace komaiba Dan kuwa kamar anyi komai angama ne.

Bayan dogon shiri da tsare tsare dai jirginsu ya daga zuwa USA inda Laylah take zazzabi da mutuwar jiki suka sameta na yanayin data samu kanta a jirgi doguwar tafiya duk da wannan shine karonta na biyu Hawa jirgi Bayan Wanda suka shiga zuwansu Abuja tareda Anne.

AMB & Alt perm rep AB TURAKI north Buckhead Atlanta Georgia

Cikin wata black Audi A8 aka daukosu daga airport zuwa gidan Wanda Laylah Bata wani damu da yanayin tsananin tsaruwarsa da sabuwar duniyar dasuzoba sbd yanayinta batajin Dadi zazzabi sosai ne ajikinta dukda tana daurewa
Dan Haka suna shigowa gidan aka nufi lafiyayyan dakinta da Ms Na’ima tasa aka gyara Mata shi daga shigowar tasu aka ja luggages dinta zuwa can tace saddika ta kula da ita itama zata huta tana Jin gajiya
Tadaga wayarta da tun a mota tasaka layinta na qasar takira numbern A Abdul dasuke tareda Turaki a office Yana Masa bayanin wasu takardu ya sati kallon Turaki Dake zaune yayi crossing dogayen qafafunsa cikin wasu irin Ash Alexander amosu vanquish ii suit fuskarsa da fararen idanuwansa na kallon screen na Apple iPad Air Dake gabansa na bayanin da A Abdoul ke Masa.

Wani Kiran ne yakuma shigowa yakuma kallon Turaki da tun Kiran farko Bai dagoba bare na biyun
A natse A Abdoul din ya dakata da fadin”

Ms Na’imah ne take Kiran shud I take the call ko naci gaba??

Agogon jaguar executive dake daure a hannunsa yafara kalla yaga lokaci yasan ta isa isowane a yanda Anne ta fada Masa Na’ima din Hanya
Kafin ya dago ya kalli A Abdoul din dake Kiran umarninsa yace ya amsa Kiran.

Juyawa yayi ya fice daga office din tareda daukar wayar cikin Bata nata girman yace”

Barka da isowa.

Kai tsaye ko gaisuwarsa Bata amsaba tace yaturo Mata likita tazo da yarinya ba lafiya.

Tana Gama fadar hakan ta kashe wayarta.

Saida yafara Kiran Dr Noah ya sanar Masa kafin ya kashe Yana mamakin inda tasamu yarinyar zuwa da ita
Ya koma gurin Turaki Yana barin tunanin zancen.

MAMUH

pay 300 @+234 903 234 5899

Mamuhgee’s complete books

Deen Marshal
Ubayd maleek
Min qalb
Kaunarmu
Buri daya
Tarayya
Eznah
Dawood
Zucuyarmu daya
Daiman
Auren raba gardama
Dacewa

Duka completes dinsu suna AREWABOOKS @Mamuhgee
[7/10, 9:29 PM] +234 704 076 8969: Mamuhgee 19
Siyayya sosai Ms Na’ima tayiwa Laylan ta kayan Yan Mata ‘yayan gata,
Komai da aka siyo Mata designers na yayan gayu tun daga kan handbags da shoes da kayan sawar dasu agago,da perfumes da undies ma da aka siyo Mata Kaya guda harma da nightwears.
Harda sabuwar waya Mai tsada sosai ta aka siya Mata tun acan aka saka Mata komai tasaka Mata Numbern Anne wadda takejin buqatar su dawo gida takira ta gaisa dasu musamman anty Sa’adah datakejinta tamkar uwa.

Sai yamma suka dawo gida sbd Saida suka biya spa.
Suna dawowa sallah kawai Laylah tayi ta saka Kiran Anne wadda Kamar tasan Laylah ce Bata qi daga Kiran ba kamar yanda take wasu lokutan na qin daga baquwar numbern Amma ganin international number saita daga.

Cikin sanyi da nutsuwa Kamar koyaushe Laylah tace”

Assalamualaikum Anne Ina wuni.

Da mamaki Mai tattareda farin ciki Anne ta amsa sallamar tana cewa”

Masha Allah Laylah tasamu Kira kenan.

Ahankali Laylan tasaki murmushi Mai qaramin sauti tana cewa”

Dazu ne aka bani wayar,
Ya gida Anne?
Inasu halima duk suna lafiya?

Dariyar manya Annen tayi tana cewa”

Duk lafiya kalau Sa’adah ma da kike Jin nauyin fara tambayarta kafin kowa lafiyarta kalau
Tana daki tareda baqi datai dangin mahaifiyartane sukazo Zan Bata numbrnki saita kiraki,
Yaya kike?
Ya qasar kina Jin Dadi kuwa?
Zaki iya zama kokuwa nasa Turaki ya dawo Dake Nan?

Murmushi kawai ta iya saki ahankali tana cewa”

Lafiyarta kalau.

Kin tabbata Zaki iya zama dasu anan din dai ko?

Kasa cewa komai tayi sbd itakam duk yanda sukai da ita Yi zatai Dan Haka batajin tanada zabin inda zata zauna acikinsu koina zata iya zama ayanzu tunda Bata tareda mahaifinta.

Ga dangin Momy da Annen tace sunzo kilama tafiya zasuyi da ita kamar yanda dama sukace bazata zauna dindindin hannun Sa’adah ba zasu dauketa Takoma gida,
Yanzu da Momy Bata Nan idan Suka dauketa tasan gidan umma Jamila za’a tafi da ita direct Dan Haka ita batada zabi aduk inda za’a kaita
Me gata ne yakeda zabin gurin dazai iya zama.

Sosai Anne ta tambayeta lafiyarta dakuma tambayoyi akan idan batada matsala da komai na gidan
Hardai suka gangaro akan karatu da Laylan zata fara ta Bata qwarin gwiwa da tabbacin zata iya sosai idan tabada himma kafin suka aje wayar tanajin nutsuwa da kwanciyar hankali akan maganar datai da Annen Dan kuwa magana da Anne na Bata nutsuwa shine abinda tasabu dashi a zamansu.

Wanka tayi kafin ta fito komai na dakinta da siyayyar da akayo Mata angama tsarasu ako Ina take dakin yazama na cikakkiyar budurwa
Tana fitowa Cindy data Gama aikin tana ficewa tabar siddika datake qarasa kunna Mata humidifier itama tana gamawa ta fice.

Zama tayi gaban mirror tana kallon fuskarta akaro na farko data zauna tana qurewa kanta kallo tareda Shiga tunanin wannan wace irin rayuwace tasamu kanta aciki kuma wadda take ga Kamar Jin dadin yayiwa marainiyar kamarta yawa.

Mai tashafa da body mist ta miqe ta duba closet dinta da aka gama gyarawa shaqe da Kaya saidai abin sanyin jikin shine yawanci ba kayan mutunci bane Dan mafi yawansu wanduna ne da skirt na Yan gayu da batasan yazatai sabo da sakawa
Dogayen rigunan ciki qalilan ne Suma duk ba masu mayafai bane saidai idan ka saka ka daura qaramin scarf akai.

Batada zabi Bayan saka wando da Riga Takoma bakin gado ta zauna tana daukar sabuwar wayarta da har cikin ranta tayi farin cikin samun wayar sbd waya dasu anty Sa’adah duk da tanajin tanason kira taji abbanta Amma tasan Momy bazata taba iya magana da itaba Dan Haka ta hakura da hakan tunda anty Sa’adah na waya da ita tanajin komai tana fada Mata hakanma yayi zataci gaba da Masa addua ta jira hukuncin ubangiji akan ranar haduwarta da Mahaifinta.

Da daddare ba dalilin rashin fitowarta cin abinci Dan Haka Dole ta fito sanye cikin Riga da wando masu Fadi kalar Ash kanta daure cikin qaramin scarf saidai gashinta ya fito kadan
Tana shigowa dining room din taga ba kowa aciki tasaki boyayyar Ajiyar zuciya tana Shirin juyawa saiga Turakin ya doso dining room din sanye cikin Ash Armani’s da slippers baqaqe da Suka bayyanarda Hasken qafafuwansa
Kyakkyawar fuskarsa a sake saidai bakuma Wai Yana murmushi bane ko dariya
Tana ganin hakan ta dawo tana matsawa daga hanya Yana kawowa ya dago fararen idanuwansa yayi Mata kallo daya ya dauke Yana amsa siririyar gaisuwarta datai Masa itama bayan ta sauke idanuwanta daga kallonsa.

Ms Na’ima Dake gefensa ta miqa Mata hannu ta Kama suka qarasa dining din tana cewa”

You look fresh my girl.

Sunkuyar da Kai kawai Laylan tayi suna zaunawa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button