NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL BY MAMUHGEENOVELS

NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL

NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL BY MAMUHGEE

Anty Sa’adah fa???

Da ido Annen ta nuna Mata bedroom dinta tana cewa”

Tana jiranki a dakinki hutawa takeyi.

Sakin Anne tayi ta nufi dakin ta tadda anty Sa’adah kwance kan gadonta tana bacci tayi wanka da alama Dan rigar jikinta bamai nauyi bace.

Kasa tada ita tayi ta aje handbag dinta tareda wayarta tana fadawa toilet da sauri tayo alwala tazo tayi sallah har lokacin anty Sa’adah Bata farka ba Dan Haka ta fito Takoma gurin Anne tana sake bayyanarda farin cikin zuwansu dayake Ms Na’ima Bata Nan tafita Koda suka iso.

MAMUH

[7/10, 9:29 PM] +234 704 076 8969: Mamuhgee 24
Jikinta amatuqar mace yake Yana rawa ta janyo rigarsa Dake gefenta ta rufawa jikinta ta sauko gadon tareda nufar kofa ta fice dakin ta nufi Wanda take ciki tashige.
Tana Shiga daki toilet ta nufa da sauri itama ta sakarwa kanta ruwa tana Jero Ajiyar zuciya ba kakkautawa sbd ba qaramin yamutsa kwanyarta da birkita tayiba da abinda yafaru mintinan dasuka wuce a bedroom dinsa.

Saidataji tana neman shidewa ta fito ruwan tadauro towel ta fito ko kanta daya jiqe da ruwan data sakarwa kanta Bata busarba ta saka wasu kayan baccin ta kwanata tareda duqunqunewa cikin bargo.

Asubar fari ta tashi sbd dama Bata samu damar bacci ba ko kadan
Dukkanin abinda yafaru ya tsaya Mata cikin Kai koina ta juya hannuwansa takeji suna yawo jikinta,
Bakinta kuwa harda safen datai brush tanajin sauran qamshin Lebon mint mouth wash aciki.

Wayarta tahau dubawa Bata ganiba Dan Haka tayi amfani da iPad dinta tayiwa kanta booking ticket na komawa Atlanta
Ta tashi tayo wanka ta shirya cikin dogon pencil skirt da Riga ta Dora kimono har qasa akai ta fito janyeda akwatinta cikin sa’a kuwa batagansa ba bare motsinsa ta fito ta tari taxi sai airport.

Kodata Isa Atlanta Sofia takira tazo ta dauketa takawota gida lokacin mum Na’ima na babban palon gidan tareda Haj Zinat suna fira hankali kwance suna jiran agama hada dining suje cin abincin Rana.

Tare suka kalleta dukkaninsu cikin kulawa da farin ciki Haj Zinat tace”

Masha Allah Laylah tadawo
Ashe da rabon zamu hadu kafin natafi.

Janyo hannunta ms Na’ima tayi tana cewa”

Happy to see back baby,.so ku gaisa da Zinat tanata son ganinki kafin ta tafi kuwa..

Wani irin nauyin mum din takeji Mai tsanani da kunyar kanta Dan sai tanajin Kamar wani zaisan abunda yafaru tsakaninta da Turakin acan
Ta qaraso a darare gabansu tana Dan sakin murmushin Dole da sanyin murya tace”

Sannu da suwa Momy Zinat,
Ya hanya?
Yaya su Anty farida?

Lafiya kalau Laylah
Ya karatu?
Da rayuwan Atlanta?
Kinata kokari ko?
Allah ya taimaka kinji?

Amin Momy Zinat nagode.

Kallon Ms Na’ima tayi a sanyaye tace”

Mum ya gida?
Bakizoba nadawo sbd school Sofia nata kirana.

Da kulawa tace”

Barin nayi har Zinat ta tashi tafiya saimuje LA din tareda ita itama ta duba Abban naki dama daga can ta wuce.

Murmushin yake kawai tayi tareda nufar hanyar dazata kaita bedroom dinta tana cewa”

Ok Bari na shiga ciki da ciwon Kai na dawo sbd mura.

Tana shigewa dakinta Cindy dake gyara Mata dakin tun shigowarta ta Isa dakin tafara gyara Mata kafin tashigo ta kalli Laylan tana cewa”

Welcome Ms Laylah.

Kai kawai ta gyada tareda aje kayan hannunta tayi hanyar toilet tashige.
Kodata fito Cindy tagama komai ta fice Dan Haka sallah kawai tayi ta Haye gado ta kwanta ko abinci Bata fito taciba taredasu mum Na’iman Dan wani irin mutuwar jiki yake tareda ita.

Sai dare ta daure ta fito sbd mum Na’iman datake ta tambayar lafiyarta kalau kuwa
Dole ta sake tafito sukaci abincin dare tare harma ta zauna Palo tana Amfani da iPad dinta kusan karfe goma kafin ta tashi tashige.

Washe gari tanada zuwa school Dan Haka tana tashi wanka tayi sama sama Tai breakfast sbd tayi latti ta wuce makaranta.

Kwana biyu Bata zama Sosai sbd makaranta kafin tasamu kanta har tana hutawa gida sosai
Daga bayama dasuka samu break koyaushe tana kicin taredasu Cindy matuqar tana gida Dan mum Na’iman kam tayi busy Sosai Bata zama sunata hidimar business dinsu dasuke na kayan da Haj Zinat zata tafi dasu.

Ranar data cika kwana Tara da dawowa ranar Turaki ya dawo gidan tana fitowa daga dakinta da safe ya nufa dining room sanyeda fararen Riga da wando kanta sanyeda hular sanyi fara itama ta shiga Kai tsaye
Sai ganinsa tayi zaune Kan kujerarsa sanyeda milk Balenciaga polo shirt da milk Wandon Alexander yayi wani irin fresh haske gabaki daya yacika dakin da qamshinsa fuskarsa na Kan abincin dayake ci Bai dagoba.

Rudewa take nemanyi sbd faduwar da gabanta yayi na rashin tsammanin ganinsa ta saci kallon Ms Na’ima Dake zaune tana cin abincin tana Masa Dan surutu ta daidaita kanta da murya Mai Dan sanyi tace”

Ina kwana Abba.

Dagowa yayi a zuba Mata fararen idanuwansa dasuka qarasa rudar da ita Amma ta Dan Dake tana kallon Ms Na’ima tace”

Good morning mum.

Morning Laylah
Qaraso Mana,
Abbanki ma gashi yadawo
Zo muyi family breakfast.

A sulale ta qaraso tana zaunawa batareda takuma dagowaba.

Gurin yayi tsit suna cin abinci sai Ms Na’ima Dake zuba zancenta na kisisinar son bin Haj Zinat dazatai Dubai su qarasa siyayyar kayan manyan shagunansu Dake Nigeria din Dan Haka kudi takeso sosai yabata dakuma qarin kamar yanason daukar tsarin zamanta a gida a Yan kwanakin ta lura saidai tunda yariga ya Saba Mata da baya takurata sai hakan yazo Mata wani iri bakuma tanajin zata iya zama guri daya.

Suna gamawa ita tafara tashi ta bar gurin Dan tanajin takurar zaman dama
Daki Takoma ta kunna wayarta da Cindy tabata tana fitowa tace A Abdoul ne yace tabata.
Cajin wayar tasaka tareda Shiga ciki tana duba abubuwa.

Wunin ranar ms Na’ima Bata zaunaba sbd gobe da qarfe shidan asuba jirginsu zai tashi Dan tana lurada Turaki zai hanata tafiyar saita nuna Masa jikin qanwar mahaifiyarta uwar riqonta ya tashi dama ba lafiyayya bace Dole yabarta tayi tafiyar da sharadin sati biyu cif zatai tadawo.

Bayan tafiyar mum Na’ima sai itama Bata wani cika zama ba Dan Haka Yan aikin gidan ne sukadai koyaushe.

Kwanan mum biyar da tafiya tadawo school a gajiye taci abinci kawai tayi wanka ta kwanta da wuri Dan Haka ko dining bataje cin abinciba sbd ko Turakin Ms Na’ima na tafiya ya daina zuwa cin abinci dining itama daina fitowa tayi a daki ko kitchen takecin abincin ta shige.

Kwana biyu saita lurada kamar bayanan ta daina ganin A Abdoul a gida Dan Haka itama hutu take kwana biyun na fashin zuwa makaranta.

Sanyeda Riga da skirt marasa nauyi ta fito daga kicin bayan sungama barnarsu a kitchen itadasu siddika saiga Sofia Nan Suka dunguma zuwa dakinta suna Hayaniya
Sai dare Sofia ta fito zata tafi tasaka driver yakaita tadawo ciki Kai tsaye wanka tashiga.

Tana fitowa ta tadda siddika dakinta tana jiran fitowarta.

Kallo daya Tai Mata tana nufar gaban mirror tace”

Akwai wani abin ne?

A Abdoul yau duka Bai shigoba ga abincin sir Turaki is ready
Munkira A Abdoul din yace afada Miki kikai Masa sama.

Shiru tayi tsawon mintuna tareda tuno abin daya faru dasu a LA tanason Jin fargabar zuwan Amma ganin Nan gidane hakan bazai taba faruwaba
Bare tasan abindaya faru a LA wani tsautsayine da dukkaninsu yakamata su manta Dan kilama shi bazai iya tuna abinda ya farun ba.
Ta cire tunanin komai tace to
Siddika na fita ta shirya cikin kayan baccinta Riga da wando ta saka doguwar kimono Mai zip har qasa ta fito kanta rufe da hular kayan baccinta taje ta dauka abincin ta nufi saman tana cire tunanin komai aranta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button