NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL BY MAMUHGEENOVELS

NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL

NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL BY MAMUHGEE

Bakowa a palon bayan tv Dake aiki ba murya ko kadan ga sanyin AC da yayi yawa da qamshinsa daya Gama kame palon duk da humidifier Dake aiki tana sakar da nata qamshin Amma nasa ya fita daban.
Kayan tea tagani ajiye Kan table na kujerar dayafi zama alamar yariga yasha tea Dan Haka ta ajiye abincin Kan table tana kokarin juyawa sai Kuma ta juyo ta kalli kofar master bedroom dinsa ta qarasa tayi knocking ahankali Dan sanar dashi takawo abincin.

Shiru ba’a budeba
Takuma bugawa ahankali saitaji shiru
Dan Haka sai ciwonsa na wancan Karon ya Fado Mata arai ta janye daga jikin kofar ta daga wayarta Dake hannunta ta saka Kiran A Abdoul Yana dauka ta sanar Masa takawo abincin tayita buga kofar Abban Amma ba motsinsa.

A Abdoul Baya gari Amma cikin daren zai dawo Dan Haka yace”

Nakira wayarsa akashe suke tun yamma karki tafi kishiga ki duba ko lafiya.

Kashe wayarsa yayi sbd Yana airport sunfara shiga jirgi dama dan Haka ya kashe wayar gabaki dayanta Yana sakawa aljihu harda Kuma qarin rashin baiwa Laylahn zabi bayan na shiga duba Turakin da kanta tunda Ms Na’ima Bata Nan.

Kallon kofar tayi tareda komawa jikin kofar takuma bugawa kadan taji still ba motsi Dan Haka cikin fargaba ta Murda kofar tashiga tana kallon koina ganin dakin da haske kadan sai sanyi da qamshin ke tashi.

Wani yawu ta hadiye sbd qamshinsa da yanayin duhun dakin da tsit din da taji duniya ta dauka ya tuno Mata da tarayyarsu a LA ta rufe idanuwanta ahankali tana kokarin dakatawa daga inda take tsayen batareda ta qara gaba ba sai gashi ya fito toilet dinsa daureda towel da rashin Hasken sosai yasa batasan wace kalar bace illa farar lafiyayyar fatarsa datake bayyane Yana zuba qamshin shower gel dinsa masu tsada ya zuba Mata idanuwansa alokacinda da ta hadiye wani mugun yawun faduwar gaba daya ratsa maqoshinta.

Ganinta ya tabbatar Masa da A Abdoul ne yayi sanadin zuwanta Saman sbd sanin halinda yake ciki Dan Haka Yana shaqar qamshinta yaji wani irin yanayi Mai qarfi gske Yana taso Masa Dan dama ruwan dayaketa watsawa kansa na kokarin kwantar da kansane dan Haka qamshinta na saka shigarsa yanayinsa na sake sauyawa ya tako da fararen qafafuwansa ya tsaya gabanta tayi saurin yin baya zata juya ta fita ya riqo hannunta wannan karon juyo da ita yayi Kai tsaye tareda rungumeta Yana kokarin fara samun nutsuwar gudanaar da komai.

Sanyin ruwan jikinsa na wanka yasata sakin Ajiyar zuciya Mai qarfi ta tsoro kafin ta dago hannuwanta ba zato ta Dora tafin hannuwanta Kan tsakiyar bayansa da Babu komai akai zata janye jikinta
Jin tafin hannuwanta Kan fatarsa da Babu Kaya akai yasashi dagata cak ya dora akan closet din fa tsadaddun suits dinsa suke jere Yana matseta jikinsa tareda hade fuskarsu ya fara kissing dinta a haukace suna watso kayan kasa.

Yanda yake kissing nata ba Wasa ko kadan aciki hakama ba damar Bari yasata qanqamesa ba shiri tana fida numfashi daqyar
Tanaji yaga duka kayan jikinta yayi wurgi dasu tareda daukanta gabaki dayanta ya nufa gadonsa suka zube akai Yana dago fuskarta da idanuwanta ke qanqame yayi Mata wani mawuyacin kallo Yana maida kansa cikin wuyanta hannuwansa na zazzafan yawo ajikinta.

Duk yanda taso kwatar kanta yau ta Hanasu aikata abinda take ganin barnace agurinsu hakan Bai samuba sbd Babu wani dama daya Bata na qwatan kanta saima zafi da al’amarin ya dauka tafara kuka tana turesa saidai yariga yayi loosing control.

MAMUH#

KUYI FOLLOWING DINA A AREWABOOKS DOMIN SAMUN COMPLETE LITTAFAINA.
[7/10, 9:32 PM] +234 704 076 8969: Mamuhgee 22
Da kanta tashiga cikinsu Cindy sukai Abincin Daren gidan suna gamawa Takoma daki yin wanka ta tadda anty Sa’adah ta tashi
Cikin tsananin farin ciki ta qaraso gabanta tana cewa”

Anty Sa’adah sannu da tashi,
Kin gaji sosai ahanya.

Rungumeta Sa’adah tayi tana cewa”

Wannan Jin nauyin Yana Nan.

Dariya tayi tana qara rungume Anty Sa’adahn tace”

Nayi kewarki ganinki in person Sosai anty Sa’adah.

Sakinta Sa’adah tayi tana kallonta dakyau fuskarta daukeda murmushi da mamaki sosai a fili tace”

Masha Allah Laylah.

Murmushi Laylan tayi tana miqewa tsaye tace”

Zansa Miki qamshin abinci Bari nayo wanka Anty Sa’adah.

Toilet ta nufa tashige tayo wanka ta fito sanyeda bathrobe blue ta nufi gaban mirror ta goge jikinta sharp sharp ta shafa Mai da spray sai body mist ta nufi closet ta dauko Kaya ta saka Anty Sa’adah nata binta da kallo cikin burgewa da shaawa sbd duk yanda ta waye take ganin ta Gama zamowa wata shegiyar Ganin Laylah yasa ta shafawa kanta sbd laylah gabaki daya Babu abinda Bai Gama sauyawa nataba kwata kwata Bayan kunya da Jin nauyi Babu abinda ya rage na tsohuwar Laylah data sani,

Fatarta tagama gogewa Takoma asalin ta mahaifiyarta fara Sol
Hakama jikinta duk ya sauya,
Kayan Dake jikinta ta kalla lokacinda Laylan tagama sallar magriba ta zare Abayar sallarta
Rigane da wando na skinny jeans blue da black chiffon blouse da Bata kamata ba sai hula qarama akanta ta zuro slippers Suka fito cin abinci.

Ms Na’ima na dawowa ta tadda baqinda batai farin cikin zuwansu ba badan kowa ba sai Dan Sa’adah wadda batama San tanayiba
gabaki daya annurinta ya dauke Dan ma sbd Anne ta iya danne wani abin ta tarba Annen harma ta Dan daure taci abinci tareda su.

Sarai Anne ta fahimci rashin murnar zuwansu agun Na’imar Amma Bata damuba saima tausayinta data Dan ji wani bangaren Amma Kuma sanar da ita asalin kishiyar tata ayanzu ba alkhairi bane Dan zata cutatar da Laylan tunda suna guri daya.

Ganin yanayin Ms Na’ima baiwa Laylah Dadi ba sbd tasan Dan zuwan Anty Sa’adah ne duk da ta lura anty Sa’adahn ko ajikinta kamarma ba gidan mijinta tazo ba,

Sunyi fira a dakin Anne Amma dasuka koma dakinta firar Yan uwantaka suka bude Nan take sake Jin yanda su Momy suke Dan momyn takoma Nigeria ta Dade sosai Amma Takoma gurin Abban sbd ya farfado Amma baya iya komai Yana daga Nan kwance yanajin komai.

Farin ciki da godiyar Allah tahau Yi tareda bayyanarda zaquwarta tason zuwa gurin ganinsa tace”

Anty Sa’adah yaushe Zaki tambaya Momy sai muje muga Abban Dan Allah kafin ku koma.

Murmushi Sa’adah tayi tana cewa”

Ki fadawa Anne Zaki bimu kila ta yarda sbd daga Nan mu dama zamuje ganinsa.

Cikin zaquwa tace Zan fadawa Anne da mum Na’ima Inshallah zasu barni.

Da wani irin mamaki Sa’adah ta kalleta Jin takira Ms Na’ima da mum cikin zuciyarta dake cikeda mamaki da tausayi Tace”

Dake da ita Kuna cikin wani yanayi
Ita tana rainon Kishiya kema kina kiran Kishiya da sunan uwa.

Sai dare sosai suka Gama firar yaushe rabo da juna kafin Laylah takuma yowar wani wankan ta saka pyjamas dagama shafe shafenta tazo ta kwanta gefen Anty Sa’adah tareda shigewa bargo.

Washe gari da pyjamas dinta ta nufa dakin Ms Na’ima ta rarrasota ga fito sukai breakfast taredasu Annen da Anty Sa’adah da mamakin duniya na Ms Na’ima din yagama kasheta Dan kuwa qarara tsanartace bayyane da Ms Na’ima tun Bata tsarguba harta fara tsarguwa sbd tsoronta Ranarda Ms Na’iman zata gane waye Laylah agurinta komaima zai iya faruwa.

Bayan sunyi wanka Suka fito tareda anty Sa’adah da zata fita da ita yawo
Tana sanyeda long pencil skirt Ash da farar blouse sai kimono shrug data sanyi akai.

Yau Bata dauka Sofia ba daga ita sai Anty Sa’adah suka wuni suna yawo takaita gurare daban daban sai dare suka dawo Lokacin Anne ma ta fita Ms Na’ima ma daman bazata zaunaba tunda suna gidan hakama da gayya ta Hana masu aikin gidan suyiwa kowa abinci Laylah kawai akaiwa pancakes da akasan shi tafi ci yawanci da daddare batacin abinci Mai nauyi shiyasa jikinta yake yanda yake batai qiba ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button