NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL BY MAMUHGEENOVELS

NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL

NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL BY MAMUHGEE

Yana kashe wayar yayi switching nata off gabaki daya ya ajiye gefe Yana Kama tafukan hannayenta dakeda Dan sanyi ya matsa Ahankali tareda dagowa ya kalli fuskarta da tamkar fuskar Zainab ce aka zaro aka Dora Mata saidai kuruciya da haske tareda kyan fata ta hutu da Laylan tafi mahaifiyarta ya lumshe ido ahankali tareda kwantarda kansa cikin wuyanta ya sauke qaramin numfashi yana sake rufe ido cikin nutsuy Yana tuno lokacinda ya Ciro sadakin mahaifiyarta daya biyawa Aminsa ranarda aka daura auren Mahmoud da Zainab.

Hannu yakai ahankali ya rungumeta tsam tsam jikinsa wani irin sabon dumin shigarta jininsa nabinsa koina,
Dan kuwa ita kadaice takeda matsayi dabam dabam fiyeda daya agunsa kaf rayuwarsa,
Tana matsayin kyakkwan rabo na alaqar aure daya qulla tsakanin Aminsa da ‘yar uwarsa dayakeda aminci sosai da ita,

Tanada matsayi na ‘yar daya biya sadakin mahaifiyarta da hannunsa,

Sanadin haihuwarta ya Rasa lafiyarsa ta zamtowarsa namiji,

Akanta ya warke Wanda Allah ya yanke hukuncin akanta zai fara sanin mace shiyasa aranarda tazo duniya ranar ya Rasa lafiyarsa harsai data girma ta zama cikakkiyar mace a qarqashinsa,

Ga matsayi na Matar da igiyoyinsa uku na aure suke kanta,

Itace macen data fara saninsa Kuma mace daya data fara daukan cikinsa duk da ya bare ko ahakan yasamu tarihin yasamu rabo a duniya na ciki….

Kwantar da kanta datai a kansa Dake wuyanta ya sanyashi bude idanuwansa ya zuba Mata Yana kallon bakinta Dake saiti da nasa suna shaqar numfashin juna light kiss yabata Kan lips dinta kafin ya tayarda ita cikin nutsuwa yace”

Zamu fita,
ki shirya.

Gaban mirror suka nufa Yana tsaye bayanta ta shirya cikin doguwar Annah Hariri Abaya wadda shine yayi Mata odarsu jiya ganin duka kayanta qananune Babu na zuwa gurin abbanta.

Makeup tayi daidai yanda ta saba bakin Nan yadauki hot red lipstick qamshinta Dake tashi ajikinta shi kadaine yake jinsa sbd ya hanata sanyawa da yawa matuqar zata fita sbd jiyan a asibiti duk inda ta motsa qamshinta kawai ke tashi yana birkita kansa.

Fitowa sukai ga breakfast Nan jere a dining Wanda A Abdoul yayi ordar
Suka zauna taje ta dauko duk wani abun buqata sukai breakfast din suka fito suka nufa asibiti.

Shiru sukai a motar hannunsa na riqe da nata kowa na tunanin yanda zai hadu da Abban musamman a yanayin dasuke ciki kallo daya Abban zai musu zai iya gano abinda yake faruwa da ita da Abba Turakin..

Tunanin hakan ya hanata nutsuwa da sukuni,
Tsananin kunyar Abban da momyn ma takeyi tanajin Kamar zasu Gama gano abinda yake faruwa da ita.

Ahankali cikin nutsuwa ya waiwayo ya Dan kalleta Yana maida hankalinsa Kan wayar dayake tabawa da hannu daya cikin muryarsa mai nutsuwa da kamewa yace”

All ok???

Numfashi ta Dan sauke jikinta na mutuwa tace”

Tare zamu shiga gurin Abban?

Tambayarta ta sanyashi Dan kallonta kadan tareda basarda yanayin yace”

No,zamu ajeki idan nadawo Zan shigo.

Ajiyar zuciya tasauke ahankali Jin abinda yace shima Daman bazai iya Shiga da itan ba kunyar Amininsa yakeji,
Bazai iya kallon cikin idonsa ba bayan abunda ya tsakaninsa da ‘yarsa yanzu duk da bazaiji komaiba idan shikadai zai tunkari Mahmoud dinba,
Da ita dinne bazai iya fuskantar Amininsa ba da baya iya boyewa kowane sirrinsa Amma yanzu Kam Banda wani.

Parking driver yayi A Abdoul Dake gaba gefen driver ya fita yabasu guri.

Hannunta Dake cikin nasa yayi kissing ahankali tareda furta”

Take care.

Gyada masa Kai tayi Ahankali tareda budewa ta fito suka wuce ta qarasa ciki fuskarta sanyeda sunglasses na Prada sai heels Dake qafarta da handbag din LV.

Kai tsaye dakin abbanta ta nufa cikin sa’a tana knocking kofar ahankali ta Murda ta tura Momy Dake zaune tana Masa waya shigowarta kenan ta dago Suka hada Ido.

Faduwa gabanta yayi ganin Momy
Ta sauke idanuwanta qasa dama ta zare glass Dake idonta tun data iso kofar dakin.

Ahankali taqaraso gefen momyn tareda sunkuyawa cikin tsananin girmamawa anatse tace”

Momy Ina kwana?

Wayar datake kashe batada ikon fita tabar dakin tunda Laylan tariga tashigo Kuma ga Abban idonsa biyu tun shigowar Laylah ya zuba Mata idanuwansa Dake bayyanarda tsananin farin cikin da zuciyarsa take ciki na ganinta gabansa ayau din,
Hannu yakeson miqa Mata Amma ba Hali Dan Haka wani sanyayyan murmushi ne mamaye Kan fuskarsa datai haske sosai na ciwo dakuma hutawa da fatarsa keyi.

Batareda Momy ta juyo da kyauba ta kalleta ta amsa gaisuwarta tana koma gefe ta zauna Kan lafiyayyar sofa Dake dakin ta dauki news paper tana dubawa sbd itama zamanta a turai tasamu cigaba na wayewar Kai da zurfafa Dan iliminta sosai ba laifi duk da matsi da takurawar dasu umma Jamila dasu Haj Karima sukai Mata Akan tadawowarta Nigeria sbd suna buqatan Shiga jikin Sa’adah sosai Amma ba dama sbd koyaushe cewa ake Bata qasar itama duk sukai waya da ita Bata Nan koyaushe cikin tafiye tafiye take Dan Haka sunsan ko zata Bari sushiga arzkin gidan AB TURAKI sai uwarta data haifeta tadawo Nigeria tunda ita sunada dama da ikon juyata son ransu,
Ita kanta momyn ta matsu a sallami Abban su tattara sukoma Nigeria ayita aqare su umma Jamilan Susan bada Sa’adah aka daura aurenba.

Jikinta sanyi yayi da yanayin momyn Dan kuwa har gobe har ranarda numfashinta zai barta bazata daina Jin kauna ga girman Momy a rantaba,

Idanuwanta ta maida Kan abbanta Dake sakar Mata murmushi taji wasu hawayen farin ciki na cikowa idanuwanta ta qarasa gurinsa ta rumgumesa Yana zaune
Ahankali hawayen idonta Suka gangaro takira sunansa cikin wata murya dake bayyanarda irin kewarsa datai tace”

Abba nayi kewarka,
Abban kullum da kewarka na tashi na wuni na kwana.

Murmushinsa qara fadada kawai yakeyi yanajin inama zai iya rungumarta shima,
Wani irin kauna yakewa Laylah fiyeda kansa da duk abin dayakeda a duniya,
Qaunarta daban take a Zuciya da rayuwarsa,
Bazai taba kaunar laylansa da kowaba sai Sa’adah wadda yake kaunarta sosai saidai tausayin maraicin Layla da rayuwar data taso ciki yasa qaunarta ta dara ta Sa’adahn cikin ransa bawai Dan fifikon ganin damaba kawai.

Sun Jima ahakan cikin tsananin kewan junansu kafin ta sakesa ahankali ta dago tana kallonsa idonta har lokacin da sauran hawaye tasaka fararen yatsun hannunta Dake sanye da zoben white gold guda biyu marasa hayaniya ta share hawayenta tareda sakin murmushi tana sake kallonsa tace”

Abba Allah yabaka lafiya naji muryanka kaman yanda kowa ke ji muryan mahaifinsa,
Naji ka Kira sunana da bakinka ka sanyani wani aikin.

Kyakkyawan murmushi yasake Mata Yana Dan rufe ido alamar ranar na zuwa Inshallah.

Momy na zaune har lokacin tana jinsu Bata waiwayo ta kallesu ba,
Haka ta wuni tana zaune maqale kusada abbanta har yamma,
Abinci ma aranar itace ta basa sbd tayi tsananin kewar hakan sai gap da magriba Anty Sa’adah ta iso Kuma daga airport direct asibiti tazo Dan Haka tana shigowa da tsananin murna na farin ciki taso tarbanta saidai ganin Momy na zaune Kuma ita ta tarba Yar tata shiyasata dakatawa Bata Isa gurin Sa’adah din ba saidai daga inda take cikin takaita bayyanarda farin cikinta sbd gudun batawa Momy Rai tayiwa anty Sa’adah din barka da zuwa tareda miqewa ta janyo Dan qaramin akwatinta na lv guda daya data zo dashi takai gefe ta aje.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button