NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL
NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL BY MAMUHGEE

Mum ma dataji yanda ya Kira sunan Laylan dakatawa tayi daga shigewa ta waiwayo tana kallonsa.
Sai daya aje tab din hannunsa gefe ya dago ya zubawa laylan su a fuska ganin lipstick dinta data shafa Yana Nan daram a bakinta har lokacin kamar ma lokacin ta shafa,
Ya gangaro da idanuwansa Kan suturar jikinta,
Skinny jeans ne ajikinta da doguwar pencil gown Wanda take tsage gefe gefe daga qasa har zuwa gurin qugunta sai Ana ganin jeans din ta inda yake yanken…
Siraran cinyoyinta lafe jeans din yake jikinsu sai silky scarf datai rolling dashi akanta ko wuyanta ba Sosai ya sauka ba…..ya dauke idanuwansa dasuka sauya take da wani bacin ran fitarta daga kanta…
Gabanta ya sake mummunan faduwa tana cigaba da shiga sanyin jikin ganin yanayinsa.
Kai tsaye batareda yakuma kallon gefentaba yace”
Meye time yanzu?
Bana fada karki Kuma fita idan ba school ba?
Akwai school ne yau?
Girgiza Kai tayi tana sauke kanta qasa jikinta na mutuwa da ganin bacin ransa.
And menene wanann a jikinki da Kika saka Kika fita dashi?
Wannan kayane?
Hawayen idonta dasuka taru ne Suka gangaro ta bude Baki ahankali tace”
I’m sorry Abba,
Zan kiyaye Inshallah bazan karaba.
Miqewa yayi yabar gurin batareda ya tanka hakurinta ba ya wuce sama.
Da mamakin Mai girman gaske Ms Na’ima tabi bayansa da kallo har yashige kafin ta maido kallonta Kan Laylah Dake tsiyayan hawaye sosai tadawo gabanta tace”
Baby kinwa Abbanki laifine da bana Nan harya hanaki fita anyhow yanzu?
Laifin me kikai?
Kinje yawone kinyi dare sosai ba?
Girgiza Kai tayi Ahankali hawayenta na sake gudu tace”
Siyayya naje tareda Sofia mukai dare shine yace karna Kuma zuwa koina sai school.
Da mamaki Ms Na’ima tace”
To ai wannan baya cikin dalilin hanaki fita gskia,
Ina nakejin Hana fita a turai saikace Muna Nigeria,
Lallai wannan saidai ke Amma Kam Ni ba magana irin wannan a tarihina….wuce kije daki Zan magana dashi anjima idan mun kwanta Zaki cigaba da fitarki koina kikeso,
Zan lallasar Miki shi anjima idan naje……
Maganar mum din ta qarasa dama lissafinta taji nauyin zuciyarta na tsananta yanda mum din keta nanata idan taje sun kwanta..
Dan Haka juyawa tayi tabar gurin ta nufi dakinta tashige tareda rufo kofar sai lokacin taji kuka na son zuwar Mata Amma ta danne ta qarasa tsakiyar dakin ta aje handbag dinta tareda cire kayan jikinta suka tayi wurgi dasu ta shige toilet.
Wanka tayo tana fitowa sallah kawai tayi ta Haye gado ta kwanta tareda dunqulewa ta rufe ido saidai zuciyarta Dake cikin Hali na qunci Babu yanda zata iya bacci musamman da kunnuwanta Suka jiyo Mata karar rufe kofar bedroom din mum data San sama zata gurin Abban koba komai tafiya tayi ta dawo yau Kam Dole gurinsa zata kwana ga gyara anyo masa…..
Wasu hawaye ne Suka gangaro gefen idonta ta rufe idon tana sake duqunqunewa cikin bargo zuciyarta na Mata nauyi.
MAMUH
NOOR ALBI Na kudi ne pay at +234 903 234 5899
[7/10, 9:36 PM] +234 704 076 8969: Mamuhgee 41
Girgiza Kai tayi cikin neman dawowa daidai Dan Bata Gama fahimtar takardar ba Dan Haka ta dunqule takardar tareda qarasawa kujerar Dake dakin ta zauna ta aje handbag dinta gefe kafin tasake ware takardar da kyau tafara karantowa tun daga sunan asibitin kalma bayan kalma harta Kai qarshe ta jinjina Kai tareda sauke numfashi a bayyane tana cewa”
Yaqi ga Mai yinka…
Kokarin daukan wayarta takeyi ta dauka hoton takardar Kiran Ms Na’ima yashigo wayar saidata sake sake numfashi Mai zafi Dan kuwa yanda takeji Kamar tayi Ido biyu da bomb ta latsa makunninsa asibitin gabaki daya ta buga
Bare Na’ima da zata fadawa zancen yanzu Dan Haka kallon Mai aikinta tayi tareda daukan Jakarta ta Ciro kudi masu yawa tace’
Kira securities din Dake waje maza.
Aje jakar Sa’adah nafisar tayi tareda nufar kofa ta fita da sauri.
Shigowa sukai ba jimawa
Dayan idonsa na Kan kudin Dake hannun Haj Zinat wadda a matse take da kowa ya watse abarta a dakin
Dan Haka ba Bata lokaci ta damqa musu kudin tace su tafiyarsu zata kula da sauran aikin kulawan Sa’adah din.
Dayake idonsu da zuciyarsu na Kan kudin Basu tsaya batawa kansu lokaciba Suma Suka karba Suka tafiyarsu.
Bayan tafiyarsu kallon nafisa tayi tace”
Fita waje kiban guri nayi mgn.
Ficewa tayi tareda Jan kofar.
Wayarta daketa faman vibrating na Kiran Ms Na’ima ta kalla tareda dagawa Kai tsaye tana gyara zama.
Cikin qaguwa da takaici Ms Na’ima tace”
Wai Zinat bazaki fadamun yanayinda yarinyar takebane?,
Idan batada alamar mutuwa ki biya ko nawane likitocin asibitin su Mata allurar qin tashi ta tabbata akwance na huta Dan jikina naban itace aka gani tareda Turaki L.A,
Zuciyata zafi take zancen Nan ya dagargaza hakurina wlh…
Na’ima ki nutsu ki saurara abinda yafi Wanda kikaji abakin khairat Chiroma,
Wannan yarinya dai ta tabbata itace atareda Turaki a L.A,
Gatanan a cikin Jakarta wlh nasamu sakamakon tana daukeda ciki harna wata hudu….
Dan shiru Ms Na’ima tayi na seconds kafin ta Dan gyara murya tace”
Ban fahimtaba,
Meye Kuma sakamon ciki ajikinta harda wasu wata hudu akai..
Kutumar ubanta zakicimun agurin na tafiyar datai da mijina tin kafin wannan maganar da kike ta tabbata Dan kuwa kasheta zanyi duk ta dauka cikin mijina…..
Na’ima maganar zahirin da gaske nake Miki akan abinda idona Suka ganemin Wanda tabbas takardar Babu qarya acikinta,
Wannan yarinyar cikine a jikinta
Na watanni hudu koma fiye…
Yawun da Ms Na’ima zata hadiye tayi numfashi ta nema ta Rasa abakinta
Gigice tafara taba wuyanta zuwa maqoshinta tana neman yawu Amma ya dauke qaf ta Rasa na hadiyewa….
Laylah data shigo dakinta idonta Suka sauka Kan yanayin momyn da sauri ta qaraso cikin firgici tana Kiran sunanta da Dan qarfi
Amma Ms Na’ima kokarin shaqurewa take sbd rashin yawun dazaibi maqoshinta yabi ta kirjinta kafin ya Isa cikinta ko zatai rage zafin wutar data taso cikin kirjinta…
Hankali tashe Laylah ta kamota duk da tafi karfinta sbd yanayin jikinta datake ba Mai qiba sosaiba Amma tanada nata jikin ba laifi musamman tunda tabaro Nigeria tana gaining weight ba laifi sbd ta daina dieting datake tuni.
Palo tayo da ita tana kwalawa siddika Kira tana cewa”
Yi sauri kawo ruwan sanyi ba sosaiba abawa mum, inaga tasamu attack ne
Yi sauri…..
Ruwan siddika taje da gudu takawo
Cindy ma da sauri tabiyota da wasu ruwan a qaramin bowl da towel qarami
Cikin sauri Laylah ke Bata ruwa abaki suna wucewa a wahale
Cindy ma cikin sauri take gogewa mum din qafafu da towel Mai sanyi hankalinsu duk a tashe.
Ruwan na bin kirjinta suka shiga cikinta ta dago idanuwanta cikin masifa ta tayi wurgi da robar ruwan gabanta tana miqewa Laylah tayi saurin riqota tana Kiran sunanta cikin tsoro tace”
Mum, mum lafiya kuwa?
Wani abun yafaru ne?
Please mum kina bamu tsoro…..
Wayarta take ware ido nema Dan Haka Bata iya cewa komaiba sai ture Laylan datai da qarfi tayi baya da qarfi tana sakin salati Mai qarfi Dan kuwa kife ta tafi zata Fadi
Da sauri Cindy ta tarota cikin tsananin firgici da tashin hankali…
Kallon juna sukai itada Cindyn lokacinda ta tsayu daidai suka kalli cikin tare jikinsu duka Yana Yar rawa
Take tsoron halin data tashi fadawa data fadin yasata shiga yanayi na tsoron ta dago idanuwanta da tuni Suka ciko da hawaye tabi bayan mum da kallo harta shige dakinta ta rufo…