NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL
NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL BY MAMUHGEE
Kasa tafiya tayi da kanta sbd ta firgita sosai itama Dan Haka hannun Cindy ta Kama suka Isa har cikin dakinta ta zauna bakin gado tareda cewa Cindy takawo Mata ruwa Mara sanyi.
Ruwa Cindy takawo Mata Tasha kadan ta Haye gadonta ta kwanta sai Alokacin tasake Ajiyar zuciya tana Dora hannunta Kan cikinta daya Dan taso.
Ms Na’ima na shiga daki ta dauki wayarta Dake yashe tsakiyar dakin ko gani Sosai batayi ta Danna Kiran Zinat.
Zinat data kasa barin asibitin sbd yanzu Kam aiki yadawo musu sabo,
Dan kuwa aikine gagarumi ya taso musu bayyanar wannan cikin.
Tana dauka tace”
Na’ima Shiga wannan halin na some some ba naki bane yanzu,
Menene abin Yi Dan Kiran da waccar tsohuwar najadun keyi yasa Dole ansanar da ita yarinyar na asibiti Dan Haka inaga…….
Zinat Ina hanyar zuwa,
Acikin Daren Nan zanyi booking ticket nadawo nayi maganin matsalar Nan kowa ya huta Dan idan bada hannuna nayi sanadin cikin yarinyar Nan ba bazan iya nutsuwaba,
Zinat kafin ki wuce Anne tazo inason kisa ai Mata allurar wata masifar koma wace iri ce Dan wlh zuciyata wuta takeci,
Turakin da akansa nake duk wani Abu danakeyi,
Yaushe Turakin ya samu lafiyar duka duka da har wata zata rigani daukan cikinsa¿
Shin yaushema har Suka sabane har Haka tafaru Banda labari?Tabbas nayi sake Amma wlh sai tayi Dana sanin kallonsama amatsyin Miji bare hada shimfida dashi.
Kashe wayarta tayi tareda .
neman numbern A Abdoul tace tana buqatan ticket na zuwa Nigeria cikin gaggawa.
Bai tsaya tambayar komaiba tunda ba huruminsa bane Dan Haka yace to tareda bincikawa ta waya ba Bata lokaci yayi Mata komai kwana biyu kafin tafiyar.
Kamar zata Ara hauka taji daya kirata ya sanar da ita sai Bayan kwana biyu Dan Haka duk saita qara Shiga bacin Rai Dan kuwa Bata taba Jin Dana sanin baro Nigeria ba sai lokacin.
Acan Nigeria a asibitin kafin Haj Zinat ta san abin Yi akan Sa’adah din Anne ta iso asibitin Dan Haka Dole ta fuske Akan itace takawo Sa’adahn asibitin harma ta biya komai tana jiran isowarsu ne dama.
Anne Bata nuna komaiba saima jinjina Mata tayi da kokarin datai na kulawa da Sa’adah kafin su zo duk da aranta tabbas tasan da wuya idan tsautsayin ne sbd tasan halayensu ita da Aminiyar tata na boye Dana bayyane.
Duk yanda taso samun ganin likita ko nurses din dake kulawa da Sa’adahn Bata samu dama ba Anne ta toshe koina ta hanyar dauke Sa’adah daga asibiti ta aka maida wata Dan Haka damarsu ta lalace saidai ta jira isowar Na’ima su San abin Yi tun kafin cikin yawuce lokacin illatawar.
Laylah kwana biyu gidansu baya cikin kwanciyar hankali sbd gabaki daya sun Rasa gane Kan mum
Ta birkice gabaki daya laifi kadan fadan gaske take rufe mutum dashi har ita Laylan Yar gaban gashinta Bata ragawaba saima tsanarta datake ji ta wani bangaren tunda sun hada jini da Sa’adah duk ba komai yasa batama kawo alaqarsu araiba sanin irin muguwar qiayyar Dake tsakanin Momy da Laylah da uwar Laylah tasan ba lallai akwai qauna a tsakaninsu ba tunda Laylan bamai surutu bace Dan hakanema batasan irin kusanci da qauna Mai qarfi Dake tsakaninsu ba,ita koyaushe kallon ba wata alaqar a tsakaninsu sbd qiyayyar Momy akan Laylan.
Kama kanta tayi daga kusantar inda mum din take sbd fushinta a kusa yake yanzu,
Ba ita kadaiba har su siddika da Cindy a kame kowa yake da gudun bacin ranta.
Makaranta ma idan Laylah ta tafi dai kusan magrib take dawowa gidan Sam gidan ba Dadi koina kayi motsi masifar mum ce ke ci ga Abban Bai dawoba bare ya iya sanin matsalarta ko zata sauko dan Haka kowa ya kame kansa Ana kaucewa fushinta.
Sai datai kwana biyar kafin tasamu wuce Nigeria data matsu Bata isaba Dan har wani tsalle zuciyarta take na zaquwa sai dataga jirgi ya saukar da ita airport din Lagos tafara jinta daidai,
Bata kwana agarinba ta hau wani flight din ta isa Abuja kafin ta sauke ajiyar zuciya tareda Jin nutsuwa da kwanciyar hankali sun shigeta.
Asibiti anso sallamar Sa’adah bayan tayi kwana biyu taji sauki sosai saidai test din da akai Mata wasu suna nuni da wata matsalar Dan Haka ba Bata lokaci Suka sake diban jininta Dan yimata wasu test din kafin aka sallamesu kafin result na test din su fito.
Bayan dawowarsu gida tayi waya da Laylah wadda ba’a fadawa abunda yafaruba sbd karta damu,
Itakuma Sa’adah abin dayasa ta nace akan Kar afadawa Laylan sbd yanayinta da lafiyarta..
Ms Na’ima ko data iso Nigeria anriga an sallami Sa’adah daga asibiti Dan Haka tana isowa Bata shigo gurin Anne ba sai data kwana ta wuni tagama danne kanta da zuciyarta sbd karta Bari Annen tagane tasan da komai sbd tunda Sa’adah ta dawo gida bazata iya komai akantaba Kai tsaye Saida wata dabarar.
****Tafiyar mum da kwana uku Abban yadawo daga tasa tafiyar murna gurin Laylan Bata boyu ba musamman dayake mum Na’ima da siddika tadawo Nigeria tunda itace Mai aikinta Koda yaushe Dan Haka Yana dawowa da kanta ta fito da gudu tayi kansa
Ba Bata lokaci ya dauketa Kan jikinsa Yana kallon haske da cikar data qara Bai sauketa koinaba sai palonsa na sama Yana kallon fuskarta datasha simple makeup sai qamshi takeyi,
Ga wata qaramar chiffon free half gown a jikinta data qara Mata kyau kaman yarinya Yar Sha uku.
MAMUH
[7/10, 9:37 PM] +234 704 076 8969: Mamuhgee 43
Yana ficewa Momy taqi waiwayowa ta kalli Yan uwanta da duk anbi anhansu gane komai,
Sunanson nuna mrnarsu da farin cikin wannan samu daya samesu Amma Kuma ganin daga uban gayyar Turakin ya fice baice komaiba hakama Anne takasa cewa komai Dan itama kanta duk da tana zargin cikin idan bana Laylan bane Amma Kuma da wuya hakan ta faru, ita Tama Rasa tunanin kamawa,
Abbansu Sa’adahn ma kasa Kama kowanne tunanin yayi Dan Sam Bai kawo ma Laylah a zancenba tunda yasan karatu takeyi tukuna,
Kuma Turakin ma baida ranar amsarta amatsayin Mata shiyasa ma zai nema sallamarta daga Turakin Dan gudun shiga haqqin takurawa Amininsa.
Momy ce kawai tunanin farko daya shigeta shine tabbacin cikin Laylah ce take dauke dashi ba kowaba, sbd sanin barewa bazatai gudu ‘danta yayi rarrafeba,
Ms Na’ima tayi babban kuskuren daukan riqon Laylah sbd batasan cin Amana a jininsu yakeba.. yanzu gashi itada Yan uwanta za’a kunno Mata masifa Dan kuwa su umma Jamila Allah kawai yanda zasu dauka wannan al’amari da aka rufesu baibai tsabar son Rai da cin Amana irin na Kawu saidu daya daura auren.
Anne Bata Gane sauran zancen da ake a dakin sbd hankalinta gabaki daya baya Kai tunani take shiga daban daban na wannan takardar…
A saninta babu wata Mrs AB TURAKI Bayan Na’ima da Laylah,
Babu Kuma wata tsautsayi ko kaddaran dazai kawo sakamakon awon cikin Na’ima hannun Sa’adah,
Laylah ce kawai duniya sukeda kusancinda al’amari irin wannan Bata zaizo hannun Sa’adah…
Idan Natane to shi wannan ciki Kuma….. Lumshe ido tayi Ahankali tana cire zancen cikin kanta gabaki daya Dan kuwa bazata taba Gane komaiba ayanzu zata saka ido taga Inda ciki zai bullo daga Mr Turakin koma wacece acikinsu.
Gida ta miqe ta wuce tabarsu suna buqatan kebancewa da Momy Suma Amma ta Hana kanta sakat da aikin hidimarta Sa’adah da zata bawa tea Mara zafi Dole Suka tafi Suka barta ba Dan sunbar zancenba Wanda Dole ayisa ai.
Saida suka wuce kafin Abba ma ya fito ya wuce da drivernsa da motarsa da aka Ware Masa.