NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL
NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL BY MAMUHGEE
Cikin son Kai qarshen matsalarsu kowa ya huta Haj Zinat tace”
Zan Kira khairat mugun bincike za’ai Mana asan koma wacece daga Nan sai asan matakin dauka…
Cikin zafin Zuciya Na’ima tace”
Bazan iyaba kasheta zanyi har ita har cikin..
Idan kin kasheta acan saikiyi bankwana da Turakin da kikai kisar dominsa Dan kina gidan yari ko lahira zai aura wata Matar.
Zinat meyasa bakya fadar alkhairi yanzu koyaushe muguwar data kikemun,Wai ko mun fara samun matsala ne?”” Tafada ranta na baci Sosai akan baqin datake ciki.
Cikin takaici itama Zinat din tace”
Aiki da hankalinkine bakyayi koyaushe irin Haka ta taso kedai maganarki kisa,
Kinsan hukuncin kisane?
Kin aikata Abu Dan wani Amma kinaji kina gani za’a rabaki da duniyar Kuma Babu abunda zaiyi miki,
Ni bana komai ba lissafi kin sani,
Inada ‘yaya idan Ina rufe Ido Ina biye Miki gurin yin komai da tuni mun Jima da zama Yan gari a lahira,
Dan Haka bazan biye Miki mu hau jirginda ba saukaba sai filin Danasani da lahiraba Dan hake kema ki nutsu cikin ruwan sanyi zamu zuba rashin arzikinmu batareda mun barwa kanmu abun fada ba.
Naji zancen ya Isa Haka sbd Zinat yanzu kin daina gane ciwona,
Kedai idan magana Bata fitowar kudi bace batada babban mahimmanci agurinki,
Yanzu kisa Fahad yamun komai cikin gaggawa inason komawa,
Tunda Turaki ya fara fadar I love you kinsan Yana gap da gane mace ciki da wajenta da halayensu da kyau Wanda kema kinsan hakan nada barazana agun mu daga lokacinda yafara karantar son dukiyarsa a jinina yake.
Zamuji da wannan idan mungama da wannan babbar matsalar dake gabanmu Dan Nima ko a mafarki bana Mana fatan wata macen da haifawa Turaki ‘yaya idan bakeba to kowama bazai masaba a zauna ahakan yafi tunda kunada ‘yar riqo.
MAMUH
[7/10, 9:37 PM] +234 704 076 8969: Mamuhgee 42
Yasan Ms Na’ima Bata Nan ta tafi Nigeria sbd ta sanar Masa da suna waya akan zata tafin, Bai Saba hanata fita ko tafiyaba shiyasa baice komaiba Bayan Allah yakai lafiya Dan fitarta Bata fada Masa dama tafiyarce dai wasu lokutan take sanar Masa bayan tagama tsara abarta.
Hutawa yayi sosai bayan dawowarsa wannan tafiyar sbd sakewar dasuka samu dagasu saisu sai Cindy wadda take tamkar secretary din Laylah Dan yanzu maganinta ma Sofia ta damqa Mata ita ke Bata anan gida tana Sha Amma a dakinta yake boye sbd gudun tsautsayi.
Samun wannan sabuwar damar dasukai yasa suqa qarasa lalacewa juna Dan kuwa yanzu tamkar wasu chewing gum suke musamman da cikinta yaqe qara Masa Jin nutsuwa da ita duk da baisan tana daukeda cikinba,
Itama cikin yasa taqarasa lalace masa,
Babu inda basa shaaninsu musamman dayake ba sauran wata kunya a tsakaninsu bayan kamewarsa Dake motsawa wani lokacin musamman idan Yana tuno Amininsa sai yanajin wani iri duk ranarda shaidar abinda ke faruwa tsakaninsu ta fita wato ciki idan tasamu.
*Babbar ranar farin cikinta tasameta ne lokacinda Abban ya sanar Mata an sallami abbanta sbd saukin daya samu Yana iya magana yanzu harma da motsa jikinsa yayi komai
Tafiya ce kawai bayayi yanzu Yana Kan kujera sai antura Amman tafiyarma zaiyi ahankali wata Inshallah.
Rumgumesa tayi tana kukan farin cikin samun lafiyar abbanta,
Jin takeyi inama zata zauna guri daya da abbanta,
L.A Suka tafi inda mum tuni ta wuce samun labarin tsautsayin Sa’adah Dan Haka ba kowa agurinsa Saida suka Isa,
Harhada komai sukai Suka Gama duk wasu formalities na sallamar Suka tarkata suka kaisa wani lafiyayyan hotel da Turaki yasa A Abdoul yayi Masa booking.
Acan suka barta ta wuni da abbanta suna magana akan yanda zamanta yake da Ms Na’ima cewan batasan ita Matar Turakin bace.
Abba Bai wani ja zancen da tsayiba sbd yanda zancen ke sanyata kasa hada ido dashi,
Hakama shima zancen baya Jin sakewa acikinsa tunda ‘yarsa ake magana da Amininsa dayasan haryanxu baigama karban aurenba,
Ya riqeta ne saboda inganta rayuwarta harma data ‘yar uwarta,har abada bazai daina gode Masa akan hakanba,
A taqaicema ya karba auren ne sbd halinda shi yake ciki yanzu kuma tabbas bazai takura Aminin nasaba zai basa tabbacin zai iya sauwakewa Laylan aurensa tunda ba Kamar taimakone yayiwa Wanda yake halin ciwo da rashin gata,
Yanzu Kuma alhamdllh yasamu lafiya, Kuma Laylan tasamu ilimi Mai zurfi ko ahaka zasu iya tallafar rayuwarsu.
Da wannan tunanin Abban ya yankewa kansa shawaran idan ya natsa bayan komawarsa guda zai bawa Turaki damar ya sallami Laylan tunda dama Babu Wanda yasan da aurenta dashi Kuma yasan bazai taba karbanta amatsayin matarsaba sbd shi da Zainab Dan ‘yarsu tamkar ‘yarsa daya haifane.
Sai dare A Abdoul yazo ya dauketa suka koma gida sbd Turakin Bai dawo gurin abbanba barinta yayi ta sake da mahaifinta suyi magana yanda yakamata sbd a kusancinsa da ita yagama fahimtar irin girman kauna dake tsakaninta da Abbanta Wanda duk ya kalli hakan ranarda ya biyawa Mahmoud sadakin zainab take Fado Masa Rai irin yanda suke tsananin son junansu baitaba saka ran ya biya sadakin da za’a hadu a Haifa Masa Mata bane…
Bayan sun kwanta tana cikin jikinsa kwance da wata qaramar fingilalliyar rigar bacci data Gama barkewa ta Samanta sbd irin yamutsar dasuka Gama Amma dayake tanason bacci da rigar sbd rashin nauyinta yasa ta maidata ahakan sbd saman ne ya Gama fincike hannuwan rigar dasuke sirara.
Cikin sigar roko da Yar yarinta ta bude Baki ahankali tace”
Abba, zanbi Abbana Nima Dan Allah naje Nigeria..
Ahankali ya lumshe fararen idanuwansa masu Dan girma ya budesu akan bakinta da yayi maganar kafin ya bude Baki ahankali cikin nutsuwa yace”
No.
Marairaice murya tayi tareda sake shigewa jikinsa tana zagaya hannuwanta zuwa bayansa tasake Dan rugumarsa Suka manne fiyeda yanda suke tace”
Please Abbahhh.
Nayi kewan gida,dasu Anne,
Inason bin Abbana gida Dan Allah.
Zakije Amma ba yanzu ba saikin Gama exams dinki tukuna na wannan session din,
Karki manta kina last year dinki.
Sanyi jikinta yayi tace”
To waye zai kaisa gidan tunda momy ta tafi?
Tare zamu tafi Inshallah gobe Zaki koma Atlanta daga Nan zamu wuce ki zauna gida kiyi karatun exams.
Sanyi jikinta yakuma yi ta kallesa tana Jin kewarsu duk su dukan shida abbanta tun Basu wuce ba ahankali da sanyin murya tace”
I will miss everyday Abbah….
Please kadawo da wuri tunda mum tace ba yanzu zata dawoba zanyi kadaici da yawa bakanan mum batanan ga abbana ma ya tafi.
Kissing lips dinta yayi ahankali tareda gyada Mata Kai batareda ya bude Baki yayi maganaba Dan kewarta zaiyi Kamar sabuwar haihuwa yasani shima saidai ba Daman nunawa shiyasa yake wahala yanzu duk yayi tafiya sbd rashinta Yana azabtar da zuciya,Ruhi da gangar jikinsa.
Da Dan zazzabi ta kwana sbd kadaici data fara tun lokacin da Yar damuwar zuwa gidan dataso Yi,
Har asuba jikinta akwai zafin zazzabi irin Wanda yake Dan damunka Ahankali ahankali,
Da safe guraren 10 Da kansa ya shiryata cikin kayan sanyi da qatuwar jacket Suka Fito yakaita tayi bankwana da abbanta Amma Bai shigaba a mota ya tsaya sbd idan yashiga bazai iya fitowa kaita airport da kansa ba saidai A Abdoul yakaita Dan Haka Bai shigaba Ita kadai tashiga tareda A Abdoul Suka Gama suka fito.
Tunda suka Kama hanyar airport take kwance jikinsa Yana kissing hannunta akai akai har Suka Isa airport din A Abdoul yafita motar yabarsu.