NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL
NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL BY MAMUHGEE

Kamata Haj Zinat tayi ta kaita dakinta ta kwantar Kan gado tana kallonta cikin sabon tashin hankali.
Allurar Jakarta da zata dauko saikuma ta fasa sbd Bata cikason yiwa Na’iman allauraba Idan abun ya taso Dan likita yabasu tabbacin tayi sabo da alluran idan abun yazo allurar kawai zata kwantar dashi.
Tana tsaye akanta har ta rufe idanuwanta dasukai jajir ahankali sai baccin wuyar wahala ya dauketa.
Ajiyar zuciya ta sauke sbd tasan kafin tasamu damar wani masifar tashin hankalin sai ankwana biyu
Dan Haka ita zatai amfani da wannan damar tasa siddika tasamo Mata tabbacin komai tunda siddikan tayi sabo da Laylan Sosai.
Fitowa Palo tayi ta zauna zuciyarsa na dugunzuma cikin zurfin tunani da rashin madafa,
Akaro na farko da mamakin duniya ya sakata kasa tunanin komai,
Tabbas wlh tanada babbacin Turaki nada alaqar da cikin,
Kuma alamun kuru kuru sun nuna shi da Anne sunsan da cikin Koda bana Turakin bane kuwa.
A gidan ta wuni sai dare ta wuce tabar Na’iman a kulawan siddika bayan tayiwa siddika bayanin abunda suke buqatan son sani game da komai na shaanin.
****Laylah kuwa tun bayan fitar mum Anne da kanta takaita har dakinta ta zaunar da ita tareda kwantar Mata da hankalinta dataga ya tashi kafin ta fito tabarta ta samu nutsuwa tukuna.
Ta Jima zaune tana kokarin nutsar da kanta din Amma takasa samun nutsuwar
Haka ta miqe jiki a mace ta Isa toilet tashige tayo alwala tafito tafara yin sallah.
Tanaji wayarta na ringing Amma takasa dagawa Dan tasan bazai wuce anty Sa’adah ko Abbanta ba kokuma Turakin sbd sune kawai masu numbern tunda sabuwace Abba ya siya Mata a Lagos.
Abinci Aka kawo Mata dakin aka jere Amma daqyar Anne tasata taci abincin kafin tafara Dan dawowa daidai.
Maganin ciwon Kai Tasha ta kwanta aka barta tayi bacci ko zata samu nutsuwa
Dan Haka tana kwantawa ta rufe Ido Amma Babu baccin dayakeda Shirin zuwar Mata Haka dai tayi lamo tunanin duniya suka rufo Mata har baccin dolen gaske ya dauketa.
Sai magriba ta farka ta tashi Ahankali ta nufi toilet tafarayin wanka da alwala ta fito tayi sallah ta Sanya farar doguwar free Riga Mai kyau Mara nauyi sai qaramar hula akanta red da slippers da Bata taba yawo ko cikin inane ba slippers ta fito tana sanyayyan qamshin turaren Creed.
Direct Palon Anne ta nufa tana kokarin kashe wayar dake hannunta data Gama magana da Anty Sa’adah.
Kai tsaye da siriyar sallama ta shiga palon batareda tayi tunanin samunsa acan din ba
Suna hada Ido ta dauke idonta ta nufi gurin Anne kanta aqasa ta gaidata tana kokarin juyawa ta koma Dan tanajin idanuwansa akanta gakuma Anne agurin.
MAMUH
[7/10, 9:37 PM] +234 704 076 8969: Mamuhgee 49
Kiran sunanta Anne tayi lokacinda tanjuya zata koma,
Cikin kalawa a natse tace”
Komawa Zakiyi ki kwanta ne? Jikinki zaiyi ciwo da kwanciya
Ba’a son Mai juna biyun da musamman yafara nisa da rashin motsa jiki kinji?
Zo ki zauna tare damu ba wata magana muke ba zance ne kawai
Halima tana shirya abinci a dining idan tagama saimuje muci tare duka harda Abbanki tunda nasan zuwa yanzu Na’ima kila ta kwanta..
Tafada hakan ne Dan kawar da rashin fahimtar zancen sbd tasani shima Turakin yasani harma da Laylan tunda itama ta wani fannin tasan mum Na’iman ko yunwa zata kashe Turakin yau bazaici abincin dazai fito daga garetaba dukda dama mafi akasari idan sunan gurin Annen ake Kai Masa abinci kokuma wasu lokutan tareda Annen yakeci anan bangarenta sbd rashin zaman Ms Na’iman dakuma rashin kusancinsu wancan lokacin Dan Haka ko yanzun bawani sauyi aka samun ba.
A sanyaye ta dawo ta zauna gurin Anne Dake binta da kallo cikin kulawa tana Mata sannu Kamar Mai ciwo harta zauna Kan qaramar sofar Dake gurin.
Murmushin karfin hali ta sake tana amsawa Annen sanmun datake Mata kafin ta Dan dago batareda ta juyo sosai ta kallesaba da Taushin murya tace”
Abba Ina wuni¿
Ahankali ya dauke idanuwansa daga kanta ya maida Kan wayarsa Dake hannunsa cikin nutsuwa ya amsa Kai tsaye duk da Idanuwansa akanta suke tun shigowarta,
Hakama irin kallon daya ringa jifanta dashi yasata duk kasa sakewa sbd ganin kaman Anne zata iya ganin abinda yake faruwa.
Fira Anne ke janta sama sama cikin kulawa tana tambayarta abubuwa dasuka shafi lafiyarta idan tanajin matsala.
Girgiza Kai tayi cikin nutsuwa tace”
banajin komai.
Kina zuwa asibiti ne acan USA din?
Kokuwa haryanzu bakya shan kowane magani?
Bakya Kan kulawan kowane likita kenan?
Gyada Kai tayi tana cewa”
Naje asibiti so daya acan.
Kallon Turaki Anne tayi Wanda yayi tamkar baya palon sbd gabaki daya ko inda suke Bai kallaba duk da hankalinsa na kanta Yana jiran yaji amsar dazata bawa Annen da kanta,
Da magana Annen zatai Masa sai taga yanda gabaki daya hankalinsa baya kansu saita qyalesa kawai sbd cikin Kam Dole itace zata tsaya gurin kulawa da wasu abubuwan na Laylah tunda batada uwa
Batada Mai fada Mata yanda komai yake,
Shi Kuma Turakin ba komai zai saniba sbd manyancin shekaru dakuma yanda yake a miskilance,
Gashi lokaci daya ta fahimci rabon ne kawai yazo Amma Babu shaquwa ko kusanci a tsakaninsu ko kadan.
Halima ce ta shigo ta sanarda sungama gyara komai a dining
Ta juya Takoma.
Anne ce da Laylan Suka fara fitowa suka nufa dining din har Saida suka zauna kafin shi yafito ya doso dining din idanuwansa akanta yanda lokaci daya kamarma ta rame sbd firgicin data shiga na wuni daya.
Jin idonsa akanta yasata dagowa a kasalance ta kalla hanyar tahowar tasa Suka hada Ido tayi wani iri da idonta Kamar zata sakar Masa kuka…
Kallon da yayi Mata na tabbas zata kwana gurinsa idan tana cikin damuwa yasata maida hawayenta tana dauke Kai daga kallonsa daidai qarasowarsa ya zauna a tsanake Yana ajiye wayarsa gefe.
Batareda da ya dagoba daga kallon dayake bin abincin Dake jere a dining din yacewa Ruky data kawo madarar Laylan da suna isowa A Abdoul yasiyo su yakawo yabawa halima aka Kai kitchen, ita Ruky tasan yanda zata dumamawa Laylan takawo Mata,
A kame cikin nutsuwa da sauti Mara qarfi yace”
Akawo fruits marasa sanyi sosai.
Yes sir.” Tafada cikin girmamawa ta juya bayan ta aje cup din madarar Mai dumi gaban Laylah Takoma kitchen.
Tana komawa kitchen ta sanarwa halima Dake jera kayan da aka gama aiki dasu gurin zamansu tace”
Shine zai Sha kokuwa Anne?
No Madam ne zataci.
Tanacinsu tareda dinner ne kokuma lunch.
Ok, ki bude fridge ki dauko ki hada a guri ki Kai bangama wannan aikinba tukuna.
To” tace tana juyawa ta nufa fridge din.
Ko da Ruky takawo fruits din Laylan Bata fara cin abinci ba Amma dai ta zuba white pasta da kidney veggies souse.
Ana aje Mata fruits din tafara cinsu a natse sbd Jin tasamu yar nutsuwa da kwanciyar hankali ganinta tareda su biyu din,
Duk tsanani tasan Anne bazata Bari mum ta iya yimata wani abuba duk da shima tasan bazai Bari din ba Amma Kuma mum din matarsace bazai tauyeta da yawaba tunda ko yayyane anyi Mata ba daidaiba.
Babu Mai magana a dining din har suka gama,
Shine yafara kammalawa ya miqe tsaye bayan ya goge Baki da tissue ya kalli Anne yayi Mata Saida safe yabar gurin bayan yayiwa Laylan kallo daya.
Itama tana gamawa daki ta nufa bayan tayiwa Anne Saida safe.
Sallar isha tayi ta sauya Kaya zuwa kayan bacci ta zauna ta Jima tana waya da Anty Sa’adah kafin ta kashe ta kwanta da tunanin Turaki cikin ranta bayan ta duba saqon ” Take care Baby ” daya Aiko Mata.