NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL BY MAMUHGEENOVELS

NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL

NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL BY MAMUHGEE

MAMUH

[7/10, 9:37 PM] +234 704 076 8969: Mamuhgee 51
Tsayawa tayi cak daga bakin kofar shigowar ganin lafiyayyar santaleliyar mace kwance kan gadon Turakinta tana bacci hankali kwance..

Rigar jikinta ma ta Turakin ce ita datake matarsa tsayin shekaru masu yawa Bata taba Sanya rigarsa a jikinta ba sai gashi yau tana gani ajikin wata…

Wata irin jijjiga jikinta keyi na tiririn dayake tasowa ajikinta tako Ina
Ta tunkari gadon tana fatan ganin fuskar macen dataiwa rayuwarta da Jin dadinta kutse a gurin Turakin..

Bakin gadon ta Isa ta tsaya tsaf
Tafara sauke idonta akan dogayen fararen cinyoyin Laylan dasuke a bayyane zuwa Kan qaton cikinta daya fito sosai….
Tana Dora idonta Kan fuskar dauke idon da sauri tareda saka hannu ta murza idanuwanta tana fatar Kar makanta tasameta daidai wannan lokacin da Komai yake Shirin Shiga tafun hannunta Dan kuwa idonta Bata yarda da abunda suka nuna Mata.

Sake murza idon tayi da kyau ta Kuma kalla taga tabbas Laylah ce a gabanta,

Wani mummanan faduwan gaba ta daki kirjinta hannuwanta da qafafunta na daukan wata irin rawa take kanta yafara juyawa
Ta girgiza Kan da karfi sbd Bata fatan ciwonta ayau itama ya tashi wannan din lokacine Mai tarin mahimmanci gareta
Duk da hakan Bata yarda da lafiyar idanuwantaba sbd zuciyarta da hankalinta sun kasa dauka Dan Haka takai hannu ahankali ta shafa cikin jikin Laylan taji tabbas cikin gaske ne,

Dan sake latsa cikin tayi taji na gaskene ba mafarki ko tunaninta bane Dan Haka ta Dan bubbuga hannun Laylan cikin wani slow da batasan yaushe ya sametaba ita kanta
tasake Dan bubbuga hannun Laylan tana tada ita Daga baccin datake hankali kwance.

Ahankali Laylan ta bude idonta Dake cikeda baccin gajiya zata mayar ta rufe taga fuskar mum daf da tata tana Mata kallon daf da daf,

Murya a cakude Ms Na’ima tace”

Laylah kece dai kokuwa idon ne yakeda matsala????

Wani mummunan tashin hankali da firgici ne ya dirarwa Laylah har Saida mararta ta kulle
A zabure ta tashi zaune daga kan gadon tana kokarin sauka dukkunin jikinta na rawa.

Laylah”

Ms Na’ima takuma ambatar sunan sbd so take tabbas kunnenta yaji muryan idan ta Laylah ce
Aikuwa cikin tsananin rudewa da tsoron daya Gama fiddata hayyacinta da rawar murya a firgice ta amsa tana cewa”

Mum ki……Wani mahaukacin Marin daya sata fadowa qasa Ms Na’ima ta sakar Mata guda biyu a jere take gefen bakinta ya fashe da jini takasa dagowa ta kalli mum din ko motsawa sai hawaye dasuka balle Mata idanuwanta na sauyawa..

Tunda take kalolin masifarta da bala’in data Saba da duk wata haukarta Bata taba Jin abun daya daki zuciyartaba Kamar abin datake gani ayau din,
Idanuwanta ne sukai jajir take agurin suna kokarin cikowa da hawaye ta maidasu da qarfin bala’i sbd ko Turaki Bata taba zubdawa hawaye Dan Haka bazata zubdawa Laylah ba,

Wani haqayi da tiririn masifa da bala’i taji suna kamawa jikinta tako Ina suna saka jikinta rawa hannunta har wani rawa yakeyi takai ta cakumo Laylan tareda shaqure wuyanta da qarfi tana cewa”

Wallahi yau saikin bar duniya shine kadai abinda zai kawo zaman lafiya
Uwarki Zaki bi kafin sauran su biyoki Dan duk Wanda ya hada alaqa dakema saina sakashi tasa masifar shima….

Fizge fizge Laylah tafara cikin tsananin masifa tana neman ceton kanta idonta na tsiyayar hawayen azaba da nauyin damuwa Amma takasa Koda iya motsa hannun Ms Na’ima bare ta ceta kanta..

A haukace takai hannu ta fizgo qaramin agogon dake zagaye da glass ta daga da qarfin gaske ta buga akan Laylan tana cigaba ihun cewa”

Wlh yau saikin bar duniya
Ko gawarki saina Kona da hannuwana,
Wannan cikin saidai kiyi naqudarsa a lahira……..

Rufewa idonta yayi ta ringa dukan Laylan tako Ina tana ihun maganganunda ita kanta bazata tantance metake fadaba sbd yanda har kufan masifa ke fita bakinta jikinta na jijjikar masifa…..

Cikin sauri ya qarasa fitowa daga toilet din Jin kunnuwansa tabbas muryan Na’ima yake jiyo Masa
Daga shi sai farar bathrobe ajiki
A matuqar fusace da qarfin gaske ya fizgo Na’iman daga jikin Laylah data fara galabaita tana hawayen azaba Dan ko kukan bazata iyaba ta jikinta yagama mutuwa da komai…

Fizge fizge Ms Na’ima keyi tana ihun daya qarasa Bata ransa qarshe cikin mummunan bacin Rai ya fizgota ya nufo kofar fita da ita Batareda ya bude Baki yace Mata qala ba Dan iya zafi ransa ya dauka zafi
Bayason aikata abin daba halinsaba na taba lafiyan mace Dan Haka janye Na’iman daga gabansa shine zai basa damar riqe kansa Dan ba qaramin dukan wulaqanci tayiwa Laylahnba…

Fizge fizge take tana qwacewa tana ihun Kiran sunan Laylah
Ta raruma wani qaton flower vase da hannunta daya ta jefawa Laylan tana cewa”

Wlh kin tabo wadda ba’a cin Amanarta tabarwa Allah sai nayi ajalinki harma da gurgun ubanki da uwarki da kowama,
Har Wanda ya daure Miki kikamun hakan bazan ragawa wlh…

Jehota Palo yayi da qarfin gaske ya juya yakoma dakin tareda rufe kofar dakin da key…

Yanaji tanata buga kofa da fashe fashen kayan palon komai tasamu dauka takeyi ta buga a kofar shigowa dakin…

Laylan ya nufa ya daukota gabaki dayanta Yana kallon fuskarta ransa na tsananta baci,
Wani zafi zuciyarsa keyi na fuskarta dayaga gefen bakinta na jini,
Cikin tsananin kulawa yake goge Mata da tafin hannunsa yace”

Are you ok?
Yaya babyn?
Tashi muje asibiti adubaki
Dole zamuga likita yanzun Nan…

Jajir idanuwanta sukai takasa Koda dago Kai ta kallesa bare ta bude Baki tayi mgn sbd radadin da zuciyarta keyi na abubuwan da shikenan sun fito fili Allah ne kawai yasan abunda zai faru Kuma yanzu.

Riga da wandon pyjamas da Abayar datazo da ita tayi sallah da asuba ya saka Mata kafin ya shirya cikin black Rugby’s ya kamo hannunta
Fuskarsa babu alamar rahama ko kadan ya kamo Laylan ya shigar da ita jikinsa har lokacin takasa qwaqwaran motsi bare magana ya bude kofar dakin…

Kallo daya yayiwa yanda tayiwa palon mummunan tashin hankali ya dauke idonsa
Tana ganinsu tayo kansu gadan gadan da qatuwar qwalban glass a hannu ta tunkari ckin Laylah……

Ba zato taji saukar lafiyayyan gigitaccen Mari akan kumatunta daya sata faduwa kwance qasa ya sakar mata…

Sakin hannun Laylan yayi Tareda kallonta fuskarsa a matuqar hade yace”

Wuce kintafi Ina zuwa.

Kamar mai naquda tafara daga qafarta ta wuce gaba…

Ms Na’ima ta Kuma zaburowa tana sake damqar kwalban ta jefawa Laylan ya tare da hannunsa take qwalban ta yankesa sosai jini yafara fita a hannun Amma Bai tsaya duba hakan ba ya kalli Laylah data tsaya cikin tashin hankali tana kallon jinin dake zuba a hannunsa yace”

Kije I will handle this…..

Rike Na’ima data taso tana ihun Kiran sunan Laylan yayi yafara Jan hannunta ya sauko da ita qasa ya fito da ita daga bangarensa ya nufi nata bangaren da ita tanata faman daga murya da fizge fizge Bai tsaya da ita koinaba sai cikin palonta ya saki hannunta tareda kallonta da idanuwansa dasukai jajir da wani razanannan sauti da bai taba fada acikinsa ba yace”

Idan Kika fito daga bangaren nan Zakiga hukuncin dazan iya dauka….

Cikin rufewar ido da masifar dake cin koina acikin jininta ta nufi kofar ko gani batayi tana cewa”

Zandawo kanka idan nagama da qaramar karuwar Dana kawo maka cikin gidana…….

Cikin bacin ransa Dake sake bayyana da kalman datake fada da fushi cikin muryarsa Mai amsa amo yace”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button