NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL
NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL BY MAMUHGEE
I dare you…..ki fita kofar Nan idan kin Isa…
Kafar ta nufa batareda ta tsaya saurarensa ba Dan kuwa Bata Gane komai bayan ganin Laylah a hannunta…
Haj Zinat data iso gidan a gigice da wani irin sauri tayi saurin riqeta ta dawo da ita tsakiyar palon cikin tsananin firgici da ganin irin tashin hankalin Dake gudana….
Jini a jikin Turakin na hannunsa dayake fita duk ya Bata jikinsa Dana Na’iman
Hankali tashe take kokarin riqe Na’iman tana cewa”
Na’ima Dan Allah ki nutsu ayi Abi komai a hankali…..
Gabaki daya ciwon Na’iman yagama tashi Babu yanda zata iya tarota Saida Allura Dan gashi ita kanta Na’iman tajiwa kanta ciwuka da glasses Dan Haka ta riqeta da qarfi tana Kiran sunanta.
Juyawa yayi ya fice batareda yabar bangaren gabaki daya.
Kai tsaye bangarensa yakoma ya sauya Kaya yafito yana Kiran Laylah a waya ta fito zuje asibiti.
Sai alokacin ta iya fasa kuka Mara sauti sosai tana Jin rashin dadin zuciya,.
Kashe wayarsa yayi tareda nufo Sashen Annen Yana kiran dr Meenah a waya yace tazo gidan yanzu.
Kuka take sosai ko daya shigo dakin
Tana hada Ido dashi tasake Jin radadinta na qaruwa sbd ganin yanayinsa tasan baya cikin dadin zuciya da kwanciyar hankali shima
Ga rauni a hannunsa.
Zaunawa yayi gefenta tareda Kama hannunta ya riqe kawai batareda ya iya cewa komaiba sbd Sam ba Dadi cikin ransa,
Baisan Na’ima d iya duka wannan tashin hankalin ba,
Baiyi tunanin zafin zuciyarta yakai hakan ba,
A qataice baiyi tunanin iliminta da wayewanta zasu Bari ta iya wannan abin ba.
Isowar Dr Meenah yasashi fita yabasu guri.
Kallonta Dr Meenah tayi tana son tambayarta lafiya Amma sbd Turakin Dake jiran aduba aga lafiyanta Dana cikin yasa tayi abunda yakawota Kai tsaye ba Bata lokaci.
Fitowa tayi Tai Masa bayanin Babu wata matsalar kawai raunin bakintane daya fashe sai fuskarta data dan kumbura tayi ja sbd kyawawan Marin da Ms Na’ima tayi Mata
Haka Yan ciwukan kawai tayi Mata treating ta tafi.
Bazai iya barin sashen Annen ba sbd Bata Nan Na’ima zata iya zuwa Dan Haka Yana fitowa ya tabbatarwa dasu halima karsu Bari kowa ya shigo Sashen idan ba Anne ce tadawoba ya juya ya fice.
Koina na palonsa a hargitse yake sbd Babu abinda Na’iman ta ragawa duk tabi ta fasa komai Dan Haka a palon qasa ya tsaya Dr faruk yazo gida yaduba nasa raunin akai dressing tareda abubuwan dasuka kamata ya tafi.
*Allura Haj Zinat ta fidda Jakarta da sauri tayiwa Na’iman da sauri sbd yanda jikin Na’iman ke rawa sosai da tashin hankalin datake ciki..
Tana yimata allurar dukkanin jikinta yayi Sanyi ya saki
Ta jata zuwa bedroom dinta ta kwantar Kan gado
Sai alokacin Ms Na’ima tasake wani irin kuka Mai tattareda ciwon da zuciyarta ke Mata.,
Ba’a taba cin Amanarta ba arayuwarta sai yau,
Cin Amana mafi muni Laylah tayi Mata Bayan tagama sanin duk duniya Babu abinda tafi tsana irin cin Amana da zafin kishinta akan Turaki..
Kuka take Yi sosai hawaye na gangara gefen idanuwanta suna Isa har kunnunta
Radadi da zafin datake ji tamkar zasu qarasa Zauta Yar sauran hankalin data rage Mata cikin qwaqwalwa..
Ita kanta Haj Zinat damuwa da baqin ciki Mai girma tashiga ganin yau Na’ima ce ke kuka Haka,
Tabbas al’amarin ya baci Dan Na’ima Bata kuka sbd Allah ya Ara Mata dama dakuma lokaci tana yanda takeso sai yanzu da babban alamari mafi girman mamaki daya samesu..
Allah yasa ba darasin duniya zasu fara ganiba Dan basa fata.
Jin tayi ita kanta wata irin tsana mafi girma da nauyi ta Laylah na sake mamayeta,
Badan sanin girman power da Turaki yakeda itaba da ayau ko ita da kanta saita dauka mataki mummunan gaske akan Laylan…
Ko ahakan tabbas saisun dauka fansar wannan Cin Amanar da wannan toazarcin….
Sam Na’ima batajin zafi ciwukan Dake jikinta da fuskarta datai jajir sbd Girman Marin datasha,
Zafi zuciyarta ke Mata sosai,
Bata taba dauka abin zaizo ahakan ba sbd Koda Zinat ke fada Bata taba yarda da hakan zai tabbataba LAYLAH DA CIKIN TURAKINTA ajikinta,
Abokin mahaifinta, mijin Yar uwarta hakama mijinta ita uwar datai Mata riqon da Matar ubanta batai Mataba…
Yanda Na’iman ke kuka sosai ya Kuma tada hankalin Zinat jikinta duk yabi ya mutu sbd a fili yake bayyane alamarin daki Na’iman sosai sbd Bata taba kawo hakan zai faruba.
Daqyar allurar ta sanyata baccin qarfi da yaji tanayi tana fizga kadan kadan Kuma badan idonta ya daina tsiyayar hawaye ba.
Fitowa Palo Haj Zinat tayi ta zauna tareda Shiga tunanin mafita dakuma yanda zasuyi ta tafi da Na’ima gidanta su samu zuwa ganin likitanta Dan wannan karon abun yayi nisa saisun hada da ganinsa
Daf Na’ima take da bayyanarda haukarta afili asani…
Daga lokacinda Turaki yasani ta tabbata ko ganin Na’iman bazai Bari kowa yasake yiba sai ya nemar Mata lafiya,
Itakuma idan tabari ta warke sarai yanzu suna cikin gagarumar matsala sbd ba kudi a hannunsu sosai,
Komai nasu yayi qasa sbd wainnan fitintinun dasuketa faruwa
Komai tsaya Mata zaiyi.
MAMUH
[7/10, 9:38 PM] +234 704 076 8969: Mamuhgee 53
Suna Isa asibiti aka karbi Ms Na’ima aka karbeta tareda shigewa emergency da ita sbd ta shaqa hayaqin sosai gashi har lokacin Allurar da akai Mata Bai saketaba jikinta a mace yake Sosai fuskarta da jikinta sunyi duhun hayaqi daya Bata jikinta.,
Zama Turakin yayi a office din Dr faruk daya bude Masa Dan ya zauna anan,
Sai alokacin ya sauke numfashi tareda kallon A Abdoul daya shigo office din da wayarsa a hannu sbd shi yabaro tasa wayar.
Kai tsaye A Abdoul wayar Anne yafara Kira dan sanar dasu Inshallah komai yafara daidaita tunda anshiga da Na’iman gashi dama ba konewa tayiba kawai dai hayaqin ne yashiga cikinta.
Wayar Annen Bata shiga Dan Haka saiya kalla Turakin a hankali ya sanar Masa.
Gyada Kai kawai yayi hankalinsa na rabuwa biyu kowanne da damuwa,
Laylah yakeji wadda ya tabbatarda hankalinta ya tashi Sosai ga yanayinta
Sam baya son abinda yake daga hankalinta gashi ba waya bare ya kirata,
Wayar A Abdoul bazataiji wani dadin wayar da itaba Dan Haka zai hakura harya koma gidan…
Bangare daya Kuma Na’iman ce da matsalolinta,
Tashin hankalin kishinta yayi yawa,
Sam takasa saduda akan lamarin gashi tana neman halaka kanta sbd tunanin banza,
Sam yakasa gane ace Mai cikakken hankali ne zai cinnawa kansa wuta sbd kishi,
To idan ta mutu ai tayi abanza kenan tunda Wanda take kishin tabarsa da wadda take kishin itama,Dan Haka gskia lamarin nata yayi Muni..
Tana warkewa zai maidata Lagos idan Kuma Nan takeso LAYLAH na haihuwa zata koma US ita tabar Mata Nan.
Sai Asuba Ms Na’iman ta dawo daidai bacci Mai nauyin gaske ya dauketa
Suna kokarin baro asibitin Haj Zinat ta iso cikin tsananin firgici da tashin hankali tana ganin Na’iman tafara kuka tana riqe hannunta.
Ganin zuwanta yasa Turakin samun saukin barin Na’iman tareda siddika Dan Haka ya wuce yabarsu agurinta.
Yana tafiya Haj Zinat kallo daya kawai tayiwa siddika datake firgice har lokacin ta Dan jinjina Mata Kai.
Siddika dai Bata samu damar cewa komaiba sbd hankalinta bai gama dawowa jikintaba,
Saura kadan yau tayi kisan Rai takeji,
Meya kaita wannan aikin rashin Imanin akan kwadayi?
Yanzu da Ms Na’ima ta mutu koda ba’a ganesu ba tasan wlh shikenan haukacewa zatai nauyin Rai data kashe bazai bar qwaqwalwartaba.
Hawaye ne Suka ciko idanuwanta jikinta na sake daukan rawa Amma Ta hadiyesu sbd Kar Haj Zinat tagani tasan zuciyarta ta raunana ta illatata gudun kawo Mata matsala,Dan hak ta hadiyesu tareda maidasu suka koma tana kokarin nutsar da kanta.