NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL BY MAMUHGEENOVELS

NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL

NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL BY MAMUHGEE

****Washe gari tunda safe Anne da kanta ta shirya gurin tafiyarwa dasu Na’iman breakfast Wanda su halima suka hada tunda safiyar Dan akai asibitin.,

Sai data duba Laylah Dake kwance tana bacci ta shafa kanta ahankali cikin kulawa da kauna sbd tasan Laylan Bata cikin kwanciyar hankali na wannan abun daya faru kafin ta juya ta fice Suka wuce asibitin itada halima aka bar Ruky sbd Laylah.

Cikin bacci taji qamshinsa na shigar Mata hanci
Ta dan motsa Ahankali tareda Jan numfashin kadan hancinta yasake shaqar numfashin ta bude idanuwanta ahankali tareda saukewa akan fuskarsa..

Zaunen yake bakin gadon Yana kallonta cikin nutsuwa da tsananin sonta dayake bayyane akan fuskarsa da yanayin kallon dayake Mata.

Ajiyar zuciya ta sauke ahankali tareda lumshe ido ta bude ta kallesa hawaye na ciko idanuwanta na kewansa dama kewan kwanciyan hankalinsu ta bude Baki muryarta na rawar son yin kuka tace”

Abbah.

Lumshe fararen nasa idon yayi shima sbd yayi kewan Jin sunan abakinta Dan Haka yakai hannu ahankali ya Kama hannunta ya tayar da ita zaune ajikinsa hannuwansu sarke da juna.

Kallonta yayi cikin kulawa da azabtar da zuciyarsa keyi akan rashin ganinta da jinta ya shafa fuskarta tareda taba cikinta dage gabansa cikin muryarsa data kashe jikinta da sonsa yace”

Lafiyanki kalau kuwa??

Gyada Kai tayi tana kwantar da kanta jikinta ta zura hannuwanta ta rumgumesa tana rufe Ido.

Babyn fa?
Ba damuwan komai right?

Sake gyada Kai tayi Ahankali kafin bude Baki cikin sautin kulawa tace”

We miss you Abbahh.

Hannunta yakai bakinsa yayi kissing ahankali kafin ya shafa fuskarta ahankali Yana cewa”

I love you.

Ajiyar zuciya ta sake ahankali tareda sake lafewa jikinsa,
Sun Jima a hakan Saida kowannensu yasamu nutsuwar zuciya data ruhi kafin ta dago da idonta ta kallesa A natse tace”

Yaya jikin Mum?
Hope bata samu rauni ko matsalaba a koina?

Jinjina Mata Kai kawai yayi Ahankali Yana cewa”

Ba matsalar komai bane hayaqin ne yaso yayi Mata illa Amma tana lafiya.

Ajiyar zuciya ta sauke tareda tasowa daga jikinsa ta zauna daidai ta sauke Kai ahankali tareda sake riqe hannunsa Dake cikin nata murya a Sanyaye tace”

Abbah please kabarni naje gida.¿
Mum na buqatan abata space tayi digesting wannan abun,
Ranta ya baci Sosai sbd yanda abun yazo Mata nakuma fahimci Jin zafinta sbd yanda nakejin zafin kishinka na tabbatarda idan nice mutuwa zanyi Abbah idan ka tafi gurin wata,
Dan Haka mum na buqatan abarta abata guri da lokaci ta Gama daukan dumin abin kafin ta sauko…

Dan Allah kabarni naje gida Nima zanfi samun nutsuwa kwana biyu..
Please Abbah.

Girgiza Mata Kai yayi Kai tsaye tareda cewa”

Bazaki ko’inaba kina hankalina zai rabu biyu.
Ki jira idan kin haihu zakije gidan kafin ki koma US.

Riqe hannunsa tayi hawaye na ballewa daga idanuwanta tana kokarin tausar zuciyarta Amma takasa sai kawai kuka Mai qaramin sauti ya balle Mata.

Abbah bazai gane halinda zuciyarta take cikiba,
Tana tsananin sonsa Amma take nesanta kanta dashi sbd tashin hankalin da ake ciki,
Idan tana gidan bazasu taba samun damar magance komaiba har a zauna lafiya,
Gashi saidai taji qamshinsa kawai idan yashigo gurin Anne
zuciyarta na galabaituwa da hakan Wanda shima tasan Yana damuwa da hakan shiyasa bama zai iya tsayawa ayi gyaran ba,

Ita kanta kullum da kwanan tunanin Yana tareda mum Na’ima take
Shedan ya Hana zuciyarta sakat Dan Haka takeson tafiya gidan.

Kukanta yasashi zuba Mata ido Yana kallonta cikin qunci da damuwar ganinta ahalin ya janyota jikinsa ahankali ya rungume sbd baisan Me zai fada mataba,
Hankalinsa bazai taba kwanciya ba idan Bata kusa dashi ko Dan sbd irin wannan fitintinun na Na’ima..

Ahankali ya dagota daga jikinsa tareda Kai bakinsa yayi kissing idonta Dake tsiyayar hawaye ya kalleta ya bude Baki cikin Taushin murya yace”

Ya isa hawayen,
Zakije gida Amma Na’ima na Jin sauki aka dawo da ita gida Zaki dawo kin yarda?

Gyada Kai tayi tana tsayar da hawayenta cikin sanyin jikin kewarsa da zatai.

Kallon kyakkyawar fuskarsa tayi tana Jin dumin hannunsa daya sauka cikin rigarta ya Dora Kan cikinta..

Lumshe ido tayi Ahankali tareda Kai hannuwanta biyu ta kamo fuskarsa takai bakinta Kan NASA ta Dora tareda Kama lips dinta ta tsotsa kafin ta zira harshenta cikin bakin ta kamo harshensa shima ta fara tsotsa.

Lumshe ido yayi tareda matso da ita jikinsa sosai ya karbe kissing din yanayi.

Sosai sukai kissing juna kafin ya saketa Suka ya miqe tsaye tareda daukanta yakaita toilet.

Da kansa ya tayata brush tayi tagama tayo wanka ya tayata shiryawa cikin doguwar riga purple Mai haske suka fito shirye tsaf suka nufa dining.

Suna zama Anne na dawowa Dan Haka kusan atare sukai breakfast din tana Binsu da kallon ikon Allah sbd gabaki daya yau Kam sun manta da Jin nauyinta sbd kewan junan da zasuyi…

Duk tabi tayi wani sukuku komai batajin dadinsa Jin takeyi tamkar zata rabu da ‘barin jikinta,
Ga fargabar abinda zata tadda acan,
Ga fargabar yanda zata hada Ido da mahaifinta da qaton ciki a gabanta.,
Dan Haka duk tabi tayi sanyi.

Baiso tafiyar tata ba Amma damuwarta akan son tafiyar yasa yabarta taje din saidai yasan kwana uku zatai zaizo da kansa ya taho da ita yakuma sanarda Mahmoud ba maganar saki har abada a tarihinsa da matarsa Zainab LAYLAH.

Anne dataji maganar tafiyar Bata hanaba sbd Laylan dama tana buqatan matsawa daga wannan fitintinun kafin asamu a sauko da Na’iman sbd wannan damuwar da tashe tashen hankulan zai iya kawo musu damuwa akan cikin Laylah
Basa fata,basa buri Allah dai ya saukar musu da ita lafiya.

Dan Haka itace da kanta ta qarasa hada kayan Laylan sbd tuni A Abdoul ya siya musu tickets itada Ruky Dan Haka qarfe biyu da mintuna aka kaisu airport Suka wuce kafin Turakin yasamu komawa asibiti.

*Yamma sosai jirginsu ya sauka suka fito Ruky na janyeda akwatinta
Ita hanbag ce kawai rataye a hannunta qarama.

Anty Sa’adah ce tazo daukansu Airport din da lafiyayyar motar Abbansu E-class da Turakin ya siya Masa.

Takowa suke ahankali zuwa gurin motar bayan Anty Sa’adah din ta tarbosu ta zubawa Laylah Ido cikin tsananin farin ciki da murnar ganinta da lafiyayyan cikinta dake bayyanarda tayi gaba yanzu saidai abita da kallon burgewa,

Fatarta da yanayin rayuwarta sun sauya gabaki daya tako Ina,
Komai nata Mai tsari da kudi ne na masu da akwai,
Kallo daya zakai Mata kasan Matar babban mutum Mai abun duniya ce sbd komai nata ya nuna Dan Haka sai murmushi anty Sa’adah keyi tana cewa”

Laylah zamtowa uwa shine babban abin farin cikin danake tayaki murna akansa yanzu.

Dan dago Kai tayi ta kalli Anty Sa’adah din dake tuqi tana maganar sai taji nauyin maganar ta kamata ta saki murmushin yaqe batareda tace komaiba.

Fira suke sama sama har Suka Kama ha Yar gidan qatoton gidan Turaki Dake garin ta waiwayo ta kalli Sa’adah a natse tace”

Anty Sa’adah gidan Zan zauna gurinku.

Dariya anty Sa’adah tayi tana karya kwanar titin da zasu shiga da motar tace”

Tun dawowarmu Muna sabon gidan Abba Turakin sbd wancan namu An rushe ana sabon gini.

Shiru tayi daidai Lokacinda suka iso bakin tangamemen gate din gidan Sa’adah tayi horn Mai gadi ya wangale musu gate din Suka shige.

Gabantane yafara faduwa tana shiga wani yanayi na fargaba duk da ta Saba da komai na dangin Momy Amma wannan karon Jin take fargaba Tai Mata yawa sbd batasan Yaya zasu karbi lamarintaba da cikin dake jikinta ita da akaje da ita da sunan riqo gata tadawo da cikin Mai gida a jikinta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button