NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL
NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL BY MAMUHGEE
Babban sashensu Suka nufa Kai tsaye Laylan na tafiya jiki mace zucuyarta bugawa kawai takeyi Amma a natse take Kamar koyaushe.
Babban palon Suka fara shiga da sallama Wanda shine palon farko kafin kashiga kofar da zata kaika palon abbansu da bedroom dinsa da toilet dinsa aciki,
Gefe daya Kuma hanyace da zata kaika wani palon da dakunan Momy Dana Sa’adah suke ciki kowa da toilet dinsa sai wani qaramin dakin kusa da lafiyayyan kitchen dinsu na gidan masu abun duniya Wanda yake na Mai aikinsu ce hadiza.
Suna shigowa babban palon da Abban Dake zaune suka fara cin Karo Yana karatu a jarida idonsa sanyeda farin medical glass ya dago cikin tsananin farin cikin zuwan laylansa ya kallesu Yana sakarwa Laylah murmushi fararen haqoransa a bayyane Dan Bai lura da cikinba farko sbd idonsa akan fuskarta ya sauka Yana cewa”
Barka da zuwa Laylan……
Cikin dake gabanta ya sanyashi qarasa kalmar a rarrabe Yana kallon cikin dakyau.
Tabbatarda cikine a jikinta ya sanyashi kallon Sa’adah daketa washe bakinta cikin farin cikin murnar zuwan ‘yar uwarta taga yanda Abban ke raba Ido jikinsa na neman yin sanyi tayi saurin cewa”
Abbah wancan takardan Daman na Laylah ne su Anne sun sani Suma tun lokacin..
Akaro na farko da Abban yaji kunyar yarsa Laylan Dan shi kunyama abin yazo Masa dashi sbd yagama sakawa ransa Raba auren sbd zaunawa yayi yai tunanin Turakin bazai taba karban Laylah Amatsayin matabe duba da shaquwarsa da Zainab uwarta dakuma duba da shine yabiya sadakin aurensu Dan Haka tako wane bangare Laylah dai bazata taba wuce wani matsayinba Bayan na ‘yar cikinsa dazai ringa kallonta…..
Yanzu Kuma ga wannan al’amari ya bullo,
Kenan Koda yayi Masa maganar rubuwar shine yasa Bai Masa amsaba Kuma tun lokacin yake ignoring calls dinsa koma ya dauka baya Bari suyi doguwar magana sbd karya Kuma kawo masa zancen rabuwar kenan¿?
Wani murmushin farin cikine ya saukar Masa,Allah sarki Turaki nawa Ashe ‘yar Zainab ce zata zama uwar yayansa shiyasa Allah ya kaddaro musu duk wannan qaddarar sbd wannan Rabon na haihuwa tsakanin Turakin da Laylah.
Kallon Laylah yayi da duk tagama muzanta jikinta yayi Sanyi cikin farin ciki yace”
Qaraso gurin Abbanki Mana Laylah..
Allah sarki Laylan Abbah,
ALLAH na gode maka daka ingantamun rayuwarsu kafin nabar duniya nagani.
Jiki mace har idonta na cikowa da hawayen kunya ta qaraso gurin Abban ta zauna ya riqo hannunta Yana kallonta yafara jero Mata addua tareda sannu da hanya.
Cikin Jin nauyi take amsawa tareda gaidasa.
Shigowar Abdullahi ne cikin farin cikin zuwan laylan ya qaraso Yana Mata sannu da zuwa yana kallonta cikeda kulawa da kauna.
Duk yanda takejin nauyin Saida suka matsa Suka rage Mata Jin nauyin tafara sakewa kafin suka tashi sukayi ciki.
Momy na zaune a Palo Kan lafiyayyar sofa tana waya da tsadaddiyar wayarta sbd yanzu Kam duniya tafara zauna musu tunda Turaki ya sake musu abun duniya suna Jin dadinsu shiyasa yanzu gidan koyaushe Yan uwanta suna hanyar zuwa.
Batasan da zuwan laylanba sbd Sa’adah Bata sanar Mata ba tunda itama yau din tasamu labarin zuwan na Laylan bayanma sun Isa airport kafin su baro A Abdoul ya sanar Mata.
Ido ta zubawa Laylan akaro na farko tayiwa cikinta kallon mintuna kafin ta dauke kanta daga kansu tana kokarin cigaba da amsa wayar saidai Sam taji takasa wayar ta kashe tareda aje wayar gefe tana sauke numfashi….
Momy Ina wuni?” Muryar Laylah data qaraso gabanta ta fada cikin sanyin murya.
Shiru tafara Yi kafin ta daga Kai ahankali batareda ta juyo ta kalli Laylan ba.
Sanin Babu abinda zata qara amsawa koda takuma wata gaisuwar yasa Sa’adah janta Suka nufi dakinta dake tsare da komai na Jin Dadi da kwanciyar hankali.
Zaunawa tayi bakin gado tana sauke numfashi sbd kwanciyar hankalin data gudo Nan Dan tasamu batajin zata samu din sbd kewansa da tunaninsa bazasu Bari ba.
MAMUH
[7/10, 9:38 PM] +234 704 076 8969: Mamuhgee 54
Wanka tayi tareda alwala ta fito daureda towel Mai girma kanta sanyeda hula ta qaraso kujeran dakin ta zauna tareda daukan wayarta dake Hasken shigowan Kira Kuma vidcall ne Dan Haka ta waiwaya ta kalli kofar da anty Sa’adah ta fice kafin ta dauki kiran.
Kallonta yake yanda koyaushe fatarta take fresh,
Ya maida idanuwansa ahankali ya kalli wuyanta dayaga kaman yayi tsayi ya Dan dauke idonsa akai anatse yace”
Haryanxu kinajin damuwa ne?
Yaya gidan?
Zaki iya zama?
Ba matsalan komai?
Ajiyar zuciya ta sauke tareda kallonsa tana kokarin sake fuska sbd tasan tambayarsa ta yanayin rayuwarta dasu Momy yake mgn akai sbd duk da Bata taba sanar dashi irin Rayuwar data taso acikiba sbd koma yayane bata buqatan kowa yasani idan har ba Momynce ta nuna irin zaman dasukeba sbd har abada ita bazata daina daukan momyn matsayin uwa ba.
Sai data nuna Masa Babu komai hankalinta yafara kwanciya tukuna Suka Gama wayar tasamu ta shirya cikin doguwar Riga da hula Mara nauyi sai qamshin turarenta daya Gama cika dakin har Yana Isa Palo da sanyin qamshinsa Mai nutsuwa.
Sallah tayi tana idarwa Ruky da aka sauke dakin hadiza Mai aikinsu tashigo dakin daukeda fruits da aka shiryawa Laylan masu sanyi da tsafta ta aje Mata tareda kallonta cikin girmamawa tace”
Ma za’a dafa madaran ne?Naga basu dashi a fridge na duba.
No kibarshi Fruits dinma sun Isa Inshallah.
Ok Ma.
Juyawa tayi ta fice daga dakin daidai anty Sa’adah tashigo Mata da abinci lafiyayye data dafo Mata da kanta tana cewa”
Ko a aje Miki a dining abincin?
Murmushi tasake tana cewa”
Anty Sa’adah abincin mafa basai kin dauko da kankiba Ruky zata dauko,
Dan Allah ki daina aikin
Gatanan ta ki ringa sakata zatayi komai.
Abincin tafara daukan spoon ta saka cikin plate din fried rice da aka sakawa hanta da qananun Naman kaza sosai ta diba kadan tana kaiwa bakinta tafara ci ahankali sbd ba wani sosai takeson Naman kazaba tunda tasamu cikin Amma sbd kokarin anty Sa’adah taci sosai ba laifi tana gamawa suka fito A rakube ta wuce palon abbanta sbd ganin Momy Dake zaune palon tana amsa waya sbd Yan uwanta yanzu kowa yanayi da ita tunda sunyi arziki.
A palon abbanta tayi dare suna magana tsakaninta da Abbanta ya tambayayeta yanayin zamanta da Ms Na’ima yanzu datasan komai.
Sanar dashi komai tayi saidai Bata sanar Masa yanda Ms Na’iman ta gansu da Abban ba.
Sosai Abban yayi Mata nasiha Yana sake tunatar da ita mahimmanci hakuri da tawakkali akan komai tunda gashinan hakuri da barwa Allah komai yakawo haske da sauyi Mai girma a rayuwarta.
Ko data dawo ciki kowa ya shige Dan Haka Kai tsaye dakin anty Sa’adah ta Isa ta tube tayi Shirin bacci ta Isa bakin gadon ta kwanta gefe daya tana Dan dafe cikinta dake motsi.
Washe gari tunda safe kamar yanda ta Saba tana budurwa Bayan sallar asuba ta fito ta nufi dakin Momy tayi knocking ahankali tareda Murda kofar tashiga taganta zaune Kan daddumar sallah ta qarasa har gefenta ta Danyi kasa da kai kadan sbd bazata iya durqusawaba cikin ladabi da girmamawa tace”
Barka da asuba Momy,
Antashi lfy?
Batareda ta waiwayo ta kalletaba ta gyada Kai ahankali alamar amsawa tana cigaba da Jan carbin hannunta.
Juyowa tayi ta fito sbd tasan iyakacinsu kenan.
Daki Takoma ta zauna bakin gado tana kunna wayarta da Abbahh ya koya Mata kashewa duk zata kwanta daga bayan Nan sbd Kar aringa damunta alokacinda take bacci ga yanayinta Kuma.