NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL BY MAMUHGEENOVELS

NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL

NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL BY MAMUHGEE

Qwacewa Na’iman tayi tana cewa”

Bazan iya Bari sai gobe ba wlh ayau saina tafadamin da bakinta yanda ta auri mijina taje tazauna a gidana harta damu wannan cikin…..

Ubantama yau saiya amsamin tambayoyina kafin na qarasa gurgunta rayuwarsa…

Yanda taringa fizgewa tana hauka tuburan sbd qarfin qwayar data Bata yasa Dole tayi Mata allurar wadda zata saukar da ita kafin gobe da safe ta saketa tayi Mata abinda takeso din.

Anan palon tabarta yashe takira siddika tace ta shigar da ita daki.

Cikin kayan Na’iman da aka kawo ta qarasa ta bude ta kwashe duk wasu dukiyar manyan sarkokin gold dinta dasu diamond ta zuba Jakarta ta fice dasu daga Gidan.

Daqyar siddika ta iya Jan Ms Na’ima tana hawayen azaba da baqin cikin halinda suke ciki sbd tabbas tasan tana gamawa da Ms Na’ima Dole zata kawar da ita tunda tasan sirrin komai,

Ita bazata iya gudu ba tunda Haj Zinat din taje har garinsu ta daukota Dan tayiwa Na’ima aiki takuma ringa daukan Mata rahoton komai dakomai na rayuwar Ms Na’iman musamman akan yanda take Bata qwayoyin dasuka juyar Mata da qwaqwalwa tsawon shekarun tana juyata sai abinda tace tayi,

Dan Haka tasan Kota gudu Bata tsiraba saima sake bawa Haj Zinat din damar kawar da ita Dan Haka bazata gudu ba zata ceto kanta da Ms Na’ima ko zasu samu rayuwar kwanciyar hankali da ‘yanci agaba.

Tana Kai Ms Na’ima daki ta fito ta nufi dakin Haj Zinat dayake tasan inda take aje takardun shaidar haukar Na’ima dakuma takardun maganin datake Bata harma Dana allurar da wani likita yake batasu
Tun farko shinema yake yiwa Zinat aikin komai na juyar da qwaqwalwan Ms Na’ima.

Dauke takardun tayi duka ta fita da sauri..

Harta Kai kofar dakinta ta tuna da Babu ranarda Zinat Bata duba takardun Kuma ta tabbarda dasu zata tafi duk inda zasu goben
Dan Haka da sauri taje ta debo wasu takardun makarantar ‘dan Haj Zinat din data gani a Palo taje ta Sanya Mata ta fito da sauri.

Daukan takardun tayi ta daure cikin leda kafin takaisu can baya cikin sharar kitchen ta Sanya tadawo ciki jikinta na zuciyarta suna rawa tana fatan kada wannan abun datai ya kashesu gabaki daya itada Ms Na’iman agurin zinat,
Dan Haka har dare yayi Haj Zinat tadawo hankalinta ba’a kwance yakeba zuciyarta bugawa takeyi da qarfi matse take da goben tayi su tafi itama ta tafi gidan AB TURAKI RES takaiwa Anne takardun sbd tasan bazata iya samun ganin Turakin Kai tsayeba ta isar Masa takardun.

Har akai sallar asuba siddika na zaune tana yawon bandaki sbd tsoro da jiran wani tashin hankali daga Zinat Amma shiru
Dan haka tana Gama sallah ko wanka batayiba ta fito tana aikin kaida kawo na aiki a kitchen ko zataji wani zancen Amma shiru duk da hakan hankalinta har lokacin a matuqar tashe yake.

Qarfe goma Suka fito Haj Zinat shiye tsaf cikin wani arnen tsadadden lace brown sai handbag dinta da takarman Dior sai qamshi take zubawa.

Ms Na’ima kuwa doguwar Rigar Dubai ce ajikinta ta wani tsaddaden material blue fuskarta ta fada sosai a dare daya sbd qwar da aka Bata Mai tsananin karfice wadda har lokacin ajikinta Bai saketaba saima tsananin juyar Mata da qwaqwalwa datake qara Yi Amma allurar da akai Mata yasa Bata iya komai sai jikinta a sake sake take ba qwari sai sun Isa zata banka Mata wata qwayar abun ya tashi.

Dan Haka ko breakfast Basu tsaya sunyiba Suka fice zuwa airport.

Suna fita da awa daya siddika ta Isa dakin Haj Zinat ta hau bincike jikinta na wata irin rawar tsoro da tashin hankali ta ringa watsi da Kaya tana bincike dakin.

Daqyar tagano jakar data fita da ita jiyan da gwalagwalan Ms Na’ima tadawo da ita Kila ba’a siya yanda takeso ba Dan Haka Bata tsaya Bata lokaciba ta dauke jakar ta fito ta nufi kitchen ta zazzage kwandon sharar ta dauki ledar takardun ta fito sanyeda doguwar Riga da qaramar hijabi ko ganin gabanta batayi Sosai
Har saidata ga anason Gane Bata hayyacinta tukuna tayi kokarin saita kanta ta dauka drp din mota zuwa Gidan TURAKI.

*Cikin kwanakin datayi a gidan tasamu kwanciyar hankali da nutsuwa
Hakama anty Sa’adah zuwan laylan yasa tasamu kanta cikin wata sabuwar rayuwar kwanciyar hankali da nutsuwa sbd zuwanta yasa shaquwa da sabuwar kauna ta qaru tsakaninta da Abbansu sbd dama ba wani shaquwa tsakaninsu Sosai.

Momy gabaki daya tun zuwan Laylah ta Rasa walwalarta ta zaman gidan
Koyaushe Bata zama gida,
Abba baida magana saita Laylah da cikinta,
Ga yarta da abban sun koma tamkar wasu bayin Laylan hidimarta kawai suka sani,

Ta bangare daya ma Sa’adahn batada lfya tana fama da yawan habon jini koyaushe Amma taqi tsayawa suje asibiti sbd idan adacan zafi ne yanzu suna rayuwar AC koina tayaya za’ace zafi ne tafi kyautata zaton Dan kanoma ne sbd idan yayiwa mutum tsanani yakan saka hakan wani lokaci…

Ita babbar damuwarta kada ya taba lafiyar Mara Kota mahaifar Sa’adah
Ganin yanda takewa Laylah ta tabbatarda tanajin tsananin kewar inama zatai auren ta Haifa nata ‘yayan.

Yau tunda safe ta shirya itada Sa’adah Suka nufi asibiti sbd Abba da kansa yace Sa’adahn taje asibiti.

Daga Laylah sai Ruky da hadiza Dake aiki ne a gidan ko Abban bayanan ya fita tareda Abdullahi zuwa tsohon gidansa da ake gini.

Zaune take Palo sanyeda doguwar Riga Mai qaramin hannu sai farar hula akanta
Fuskarta tayi fresh sbd hutu.

Furar dataji Madara d fresh nono takesha cikin cup tana duba wayarta dataketa Kiran Abbahh Bata shiga,

Yau tun safe take kiransa takasa samu..

Hankalinta baya Kan tv Dake aiki Yana Kan wayar hannunta Dan Haka ko dataji sallama bata dagoba sai data aje wayarta Dake hannunta gefe tareda kallon kofar tunaninta su Anty Sa’adah ne suka dawo.

Cup din hannunta ne ya subuce Mata lokaci daya tana sauke kafarta data miqe daga Kan table dake gabanta gabanta yayi mummunan faduwa ta miqe tsaye tana kallon umma Jamila dake gaba Haj Karima na biyo bayanta sai Anty fatima.

Cak umma Jamila ta tsaya tana kallon fuskarta da kyau sbd kwanakin tana fama da Ido ta waiwayo ta kalli Haj Karima Dake qarasowa ciki idonta akan cikin Laylan itakuma tace”

Haj karima wannan Kuma dai gata Kamar ‘yar Mahmoud da kishiyar zainab kokuwa idon ne?

Anty Fatima datake qanwarsu tace”

LAYLAH?????

Qarasowa suka fara Yi umma Jamila na sake qure kallonta akan Laylan da mugun mamaki tace”

Harda tsarabar cikinta tadawowa Mahmoud gashinan ajikinta.

Wata muguwar dariya Haj Karima tasaki tana nufar kujera ta zauna tace”

Allah sarki,
Shikuwa Mahmoud ahaka zai qare daga haihuwar ‘yar da ba’a tabbatarda aurensa da uwartaba sai samun jikan wata hanyar.

Hannu umma Jamila takai ta janyeta da qarfi ta watsar gefe tareda zaunawa tana cewa”

Can ya matse musu idan shege dari zata Haifa su Suka sani,
Fata dai wlh baza’a haifawa zainab shege acikin gidaba,
tunda bin baza ta zaba taj ta bisu can kowama ya huta.

Tashi tayi daga jefar da ita da umma Jamilan tayi tareda Dan sauke Kai cikin girmamawa ta gaidasu Amma Babu Wanda ya kalleta bare ya tanka
Ta juya tabar gurin jiki Amace ta shige daki.

Tana shiga su Momy na shigowa
Tun a haraba da Momy taga motar umma Jamila tasan suna gidan hankalinta yaso tashi Amma Kuma ta Dake tunda ba ruwanta da shaanin Laylahn ita yanzu ta yarta da aka dinga diban jinin Dan gwaje gwaje take.

MAMUH

[7/10, 9:38 PM] +234 704 076 8969: Mamuhgee 55
Momy na shigowa palon ta kallo daya tayiwa fuskokinsu ta dauke Kai tana qarasowa ta zauna tareda bude Baki a sanyaye ta gaidasu sbd ganin yanda umma Jamila ke Mata kallon datasan maganar da za’a fada Mata bamai Dadi bace.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button