NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL BY MAMUHGEENOVELS

NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL

NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL BY MAMUHGEE

Ita kanta Sa’adah jikinta mutuwa ya sakeyi akan na zazzabin data dawo dashi na dibar jininta da aka ringa Yi dakuma kaida kawo,
Daqyar ta iya driving dinsu Suka dawo gidan.

Cikin sanyin murya ta gaidasu ta juya ta nufi dakinta ta shige.
Gabaki daya jikinta a mace yayi yayi Sanyi sosai hakanan yau zuciyarta take sakayau Bata Jin nauyin komai Kamar wadda ba zuciyar a kirjinta.

Laylah na zaune tashigo Bata iya cewa komaiba ta wuce toilet tayo wanka da alwala tafito daureda qaton towel ta shirya cikin Riga da skirt na atamap ta Sanya qatuwar hijab ta tada sallah.

Tana idarwa hadiza ta shigo ta kawo Mata abinci Amma Sam batajin cin abincin
Ruwa kawai Tasha ta Haye gado ta kwanta tareda rufe ido koina na gabobin jikinta suna Mata ciwo.

Cikin kulawa Laylah tayi Mata sannu tareda gyara Mata rufarta Jikinta na sanyi tace”

Anty Sa’adah ko dai zaki koma Abuja ne saikiga likata acan?

Girgiza Kai tayi tana cewa”

Bafa komai bane Momy ce itama duk tabi ta daga hankalinta.

Wani sanyayyan murmushi Laylan tasake ahankali Jin abinda anty Sa’adahn tafada,
Ahankali tace”

Momy Dole zata damu tunda bakida lafiya Kuma jikinki ya nuna hakan.

Yanda Laylah tayi mganar cikeda sanyin jiki Dana murya yasa anty Sa’adahn bude idonta ta zubawa Laylahn sbd tajiyo ‘dacin rashin mahaifiya acikin sautin maganarta.

Ahankali ta bude Baki tace”

Laylah kinsan cewa kinfimu gata dagani har Momy?

Rashin mahaifiya bashine rashin uwa ba,
Kina tareda soyayyar mahaifinki tun lokacinda kike qaramarki cikin Hali na maraicin uwa,

Kin taso cikin Rashi na makusanta Amma Kuma nida Momy mun rayuwa cikin Yan uwan da makusantan Amma Kuma a qasqance sbd ganin Ana tallafe damu,

Ki godewa Allah da wani kadaicin da wani rashin makusantan alkhairi ne tunda gashi yanzu daga mu din har makusantan mu muna qarqashin inuwarki,

Wani gatan da Jin dadin da Turaki ya sakar Mana bana kusancinsa da Abba bane kawai na girman dakike dashi ne a zuciyarsa..
Dan Haka Laylah ki daina Jin daci arayuwarki Dan bakida maraici yanzu.

Murmushi Mai ciwo Laylah tasaki tareda maida hawayen dasuka ciko idanuwanta ta bude Baki akaro na farko datai maganar maraicinta na rashin uwa tace”

Anty Sa’adah duk gatan dazan samu a duniya zanso inada mahaifiyar da zata kalleni tasan ciwona da damuwata saidai Allah Bai kaddareni da samun wannan gatanba saiya bani wani gatan na daban…

Tashi zaune anty Sa’adah tayi tana kallon fuskarta tace”

Laylah maraicin mahaifiyar data haifeki kawai Zakiyi sbd Babu Wanda zai taba maye gurbinta Amma na tabbata Anne da abbah turaki bazasu taba Bari kiyi wani maraicinba har lokacinda Momy zata bude Miki zuciyarta ki Shiga ta karbeki amatsayi na ‘ya..

Wani sanyayyan murmushi takuma saki hawayen datake riqewa Suka ga gangaro Mata sbd tasan qaddararta da Momy Allah Bai rubuto musu zama makusantaba.

Murmushi Sa’adah tayi tana cewa”

Kina mamaki ne?
Inshallah wata Rana zaki samu gurbi Mai girma a azuciyarta.

Shiru kawai Laylah tayi Bata sake cewa komaiba har bacci ya dauke Anty Sa’adahn
Ta zuba Mata idanuwanta dasukai ja sbd hawayen datayi.,

Anty Sa’adah zuciyarta Mai tsafta ce shiyasa take ganin Momy zata kaunace kamar ‘ya wataran,

Ita basai momyn ta karbetaba ahakama tana kaunarta sbd itace mahaifiyar Anty Sa’adah.

Wayarta Dake gefenta takuma dauka ta saka Kiran Abbahh Amma still Bata shiga,

Hakanan takejin kadaici da maraici na shigarta Dan Haka ta koma Kan kujera ta zauna rakube tana kallon fuskar Anty Sa’adah Dake bacci cikin nutsuwa da kwanciyar hankali.

Hayaniya ce ta kaure a Palo ba zata ba tsammani sai ganin umma Jamila tayi akanta tana dago fuskarta kuwa ta kifa Mata wasu fararen Marika a jere tareda finciko ta tayo Palo da ita jikin har wani irin rawa yake tana cewa”

Nafada nakuma fada wannan itace muguwar qaddarar rayuwarki Zainab Dake da ‘yarki Kika qi Jina ga irin kyakkwan sakamakon data nuna na cewan ita jinin Mahmoud da uwarta ne,

Mahmoud ne da matsiyacin Kawun can suka daure gindi akai wannan gagarumar cin amanar ta sauyawa Sa’adah Miji a daurawa wannan maciyar Amanar butulu wadda Bata gade alkhairi,

Tsawon shekaru Muna dakon aure Sa’adah keyi shine sai yanzu kike sanar damu riqonta akeyi a gidan turaki¿
Kutumar uban riko duk inda yake
Wlh yau Mahmoud saina wanke Masa allon rashin mutinci.

Haj Karima dataga mutuwa tsaye da baqin cikin zamtowar Momy Yar uwarta murya cikeda baqin ciki tace”

Allah ya Isana tsakanina Dake zainab,
Wlh ban dauka lalacewar da mutuwar zuciyarki yakai wannan zarafinba Dan kuwa ke ko ajikin danginmu kinfi kowa zama asararrar,

Miji ya cuceki ya aura watacan daban bada saninkiba harda haihuwar asara Amma Kika kasa rabuwa dashi saima zaman jinyar nakasasshe,
Keda yarki kuka Gama zama ‘yan maula shine yanzu anyi wannan Cin Amanar an rufemu kema Kika biye aka ringa binmu da kallon shashashu gamu Yan iskan iska wato,

To wlh kuwa Zainab daga yau babuni Babu ke,
Dan kin Haifa mace mun nuna munasonta muna fatar tayi aure gidan hutu taj dadi shine muka zama makiyanki kika biye musu aka rufe mu wato mu makwadaita..

Tsabar baqin ciki daya Gama rufe idon umma Jamila sake fizgar Laylahn tayi batareda la’akari da cikin dake jikinta tayo palon waje da ita inda ta tabbatarda Mahmoud na Nan

Ido rufe ta saki Laylahn agabansa tareda kallonsa cikin tsananin baqin ciki da bacin rai tace”

Mahmoud kaji kunyar duniya saura ta lahira wlh,

Duk cin Amana da quncin daka saka zainab akan uwar yarinyar Nan Bai issaba ta kashe rayuwarta gurin jinyar Maci Amana irinka duk da hakan Bai isaba shine yanzu aka tozartata ta hanyar aurar da ‘yarka ga Wanda kakeso bayan Sa’adahn ce babba qarshen wulaqantawa kowa na Mata kallon Matar aure sai yanzu ace wannan ce Matar ita riqonta akeyi…
Shin Mahmoud kana ganin Sa’adahn ta cancanta hakan daga gareka?
Kokuwa ita ‘yarka bace musani wannan ce kawai yarka???

Abba shiru kawai yayi Mata baice komaiba sbd jikinsa da yayi Sanyi da abinda tayi din gaban Wanda yakeda matuqar mutunci da girma a idonsa Kuma uban ‘dan cikin datake kokarin aibantawa.

TURAKI kuwa Dake zaune tareda Abban shigowarsa kenan
LAYLAH daya riqe jikinsa Lokacinda ta sakota zata Fadi yake kalla idanuwansa sun sauya take saidai yanayin Shirun da Abba yayi dakuma Laylan da idanuwanta suke rufe tana tsiyayar hawaye batareda ta iya dagowab ya sanyashi dakewa kamar baya gurin ya miqe tsaye da kyau sai alokacin ta waiwayo ta kalli Wanda ke zaune Tareda Abban batace komaiba ta juya ta fice tana Jin zuciyarta Kamar zata tafashe tsabar baqin cikin dasuke ciki yau.

Mahmoud ya haifar musu masifa
Ya haifar musu bala’i.

Acan cikin Koda ta iso Momy kuka takeyi sosai na irin cin zarafi da maganganu masu dacin gaske da Haj Karima ke fada Mata,
Umma Jamila Jin tayi ta tsani momyn da Sa’adahn gabaki daya Dan Haka komai bazata iya cewaba ta fizgi Jakarta tayi gaba tana cewa”

Har ababa bazaki sake ganinaba a gidanki zainab,
Kin zabi namiji kinbar Yan uwanki Zaki Kuma ganin sakamon da Zaki samu daga garesa.

Fita sukayi Haj Karima kuwa duk wata alaqarta ta yanke da momyn daga ranar taje sunbarwa Mahmoud ita.

Bayan fitarsu sakinta Turaki yayi Ahankali tareda kallon fuskarta a shaqe ya iya cewa”

Je ki shirya kifito zamuje ganin likita.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button