NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL
NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL BY MAMUHGEE

Batada karfi ko tunanin tsayawa musu Dan Haka ta juya Takoma ciki mararta har murdawa takeyi sbd tsabar dacin zuciya da damuwa Mai qarfin gaske data shigeta.
Kusan koina batada farin jini qinta suke kamar tabar duniyar su daina ganinta.
A Palo Momy kuka takeyi sosai Mara sauti Wanda yasa jikin Laylah qarasa yin sanyi hawayen dake idonta Suka fara saukowa suna gangara,
Tasan radadi da ‘dacin kalaman dasuke fadawa Momy tun ba yanzuba basa fadar kalma Mai Dadi akanta sbd batada abun duniya,
Sun kasa barinta taji ta runguma kaddarar rayuwar aurenta koyaushe cikin sakata qunci suke fa kalamansu.
Batada iko ko damar bin gaban momyn sbd kada ta qara Mata quncin zuciya ta sanadin ganinta tunda ko yanzu itace silar da hakan tafaru.
Daki tashige cikinta na juyawa tareda Mararta sake ciwo kadan kadan.
Zama tayi bakin gadon da anty Sa’adah ke kwance har lokacin tana bacci cikin nutsuwa
duk hayaniyar da akai Bata tayar da itaba bayan Kuma batada wani nauyin bacci.
Bata iya sauya kaya ba sbd juyawar dataji cikinta yakuma Yi Dan
Abaya kawai ta dauro akan doguwar rigar Dake jikinta Mai qaramar hannu.
Tareda Ruky ta fito suna Isa jikin motar Abba yace Ruky tayi zamanta sbd Turakin nema da kansa ya karba tukin A Abdoul zamansa zaiyi gida su sake gaisawa da Abbansu Sa’adahn.
Kallonta abbanta yayi cikin kulawa da qauna Mai tsanani yace”
Zainab¿
Dakatawa tayi tareda waiwayowa ta kallesa da Idanuwanta dasukai jajir saidai takasa amsawa,
Zuciyarta nauyi take Mata sai kawai hawaye Suka gangaro Mata ta kallesa cikin kauna ta mahaifi.
Laylah ki kula kinji,
Allah yasa muji alkhairi,
Karki damu da maganganunsu komai lokakacine dashi idan Kika tafi Babu Mai sake ganinki acikinsu.
Karki damu kinji?
Ahankali jiki amace ta gyada masa Kai tareda shigewa motar suka fice daga gidan yana kallonsu.
Hannunsa daya yakai ya riqe hannunta Dake aje Kan cinyarta zuciyarta wani irin nauyi da harbawa take mata dayasa takejin rashin nutsuwa Sosai.
Kasa dagowa ta kallesa tayi saima mutuwa da jikinta yayi har suka Isa lafiyayyar 5star hotel din daya sauka suka Isa qaton dakinsa dake floor din sama karshe.
Zaunar da ita yayi kafin ya zauna gefenta sai alokacin ta dago ta kallesa ya Dan rintse manyan idanuwansa dasuka sauya haryanxu Basu koma yanda sukeba sbd har lokacin zuciyarsa radadi da zafin abinda akai Mata sukeyi.
Kasancewarsu Mata Kuma harkan family yasa Bai tunanin daukan matakiba ko kadan saidai Kuma tabbas bazata sake zuwa duk inda dangin momyn sukeba,
A qataice za’a Samar Mata da nata gidan daban ta yanda idan tazo zata ringa zama acan kafin tagama kwanakinta ta tafi duk da ko zuwanma bayajin akwai ranarsa kusa matuqar ta koma.,
Shi gabaki daya wannan yawon ya ishesa tattara matansa zaiyi yakoma US hankalin kowa ya kwanta.
Dr Amatullah ce tazo har hotel din taduba Laylah Babu wani matsalar komai sai damuwa data sakawa kanta Wanda ya hawar da bp dinta shine yasakar Mata cin Dan ciwon Mara gashi Daman cikin yashiga wata bakwai yanzu.
Bayan tafiyar Dr Amatullah magani kawai ta iya Sha taso zuwa gida Amma ya hanata saita cire Mata kayanta da yayi sukai sallar magriba,
Daqyar ta iya Shan tea kawai sbd hakanan komai batajin dadinsa zuciyarta takasa samun nutsuwa
Suna Gama sallar isha baccin Dole ya dauketa sbd cikin maganin da aka Bata hardana bacci sbd yanayin datake ciki duk tabi takasa samun nutsuwa.
Qarfe biyu da mintuna ashirin cif na dare baqar motar Honda ta Parker bayan gidansu Abban daga nesa.
Haj Zinat ce zaune aciki tareda Na’ima data Gama bankawa wasu irin mahaukatan qwayoyi masu qarfin gaske dasuka qarasa buga qwaqwalwar Ms Na’ima gabaki daya sai abinda Allah ya rage..
Tana cikin motar zaune yaran datazo dasu Suka fita Suka tunkari gidan.
Babbar katangace kewaye da gidan gakuma security electric wire Dake zagaye da katangar Amma Haka Suka zagayafa suka fara disconnecting CCTV cameras Dake zagaye da bayan gidan kafin suka kame katangar Suka fada gidan sbd qwararrine a harkar na karshe.
Mintuna kusan goma Sha shiga da fadawarsu gidan wuta ta tashi take koina tafara ci Kuma tako Ina.
Masu gadin gidan guda biyu Koda suka Ankara Suka firfito tuni wutar takama sosai Tako ba halin tunkarar ciki Dan Haka Suka fito waje suna neman daukin jama’a a fito.
Yanda wutar ke ci sosaine yasa jamaar dasuka fara firfitowa ihun neman agaji da taimako.
Momy da Allah yasa tanada rabon fitowa Daren a gurin Abba ta kwana sbd tashiga quncin da Bata taba Jin zuciyarta tashigaba a ranar,
Maganganun Yan uwanta sun Kama sakata cikin tsananin dacin zuciya da kunci Wanda yasa Abba da kansa ya kirata dakinsa ya zaunar da ita tareda qasqantar da kansa yabata hakuri sbd koma menene shine suke ganin ya cutatar da momyn.
Yanda ya qasqantar da kansa yakuma Bata zabin idan shine matsalarta da baqin cikinta idan tanaso zai sauwake Mata taje ta shirya da Yan uwanta idan tanaso.
Kalmarsa tasata sake Shiga mawuyacin halinda yakaisu ga shiryawa a Daren harma ya sauke Mata haqqinta na aure da sukafi shekaru masu yawa Basu samuba.
Wutar zafi da tsananin hayaqi ya sanya Abban fara farkawa yaga wutace takeci harta fara shigowa dakin dasuke sosai.
Tayarda Momy yayi yace tayi maza idata keda lafiyayyan kafafu ta fita takira su Sa’adah su fito.
Gigice Momy ta tashi tana tarin hayaqin daya fara fin karfinsu tana kokarin kamasa su fita ko Babu kujerarsa tunda Amma yayi Mata nauyi Dan haka yace ta sakesa taje ta dubo su Sa’adah idan wutar batakai can ba.
Kasa tafiya tayi tabarshi Dan Haka tafara jansa cikin wutar cikin tsananin azaba wutar Dake cinsa din suna kaiwa kofa ya turata waje da sauran qarfinsa daya rage.
Kokarin dawowa takeyi Amma wutar taci karfi ita kanta take kanta yafara juyawa sbd haqayqi da zafi Bata gani batansan inda kanta yakeba Haka taita jefa qafa har wutar taci karfinta ta Fadi a inda take.
Wuta Kam sosai takecin gida tako Ina ba damar Shiga ceto sbd tagama mamaye koina na gidan…
Kallon Ms Na’ima Zinat tayi bayan tasake wani mamalacin murmushin kawarda matsalar Laylah a rayuwarsu tace”
Na’ima kinga ga wutar gidansu Laylah can tanaci suna konewa jeki ki tabbatarwa idonki.
Bude mota tayi tareda janyo Na’iman ta fito Kai Tsaye kuwa ta nufi gidan ta wuce jama’a tana cewa”
LAYLAH Kinga sakamakon cin Amanar da kukaimin Nan….
Turaki nawa ne Ni daya bazai taba zama nakiba kije lahiranki ke daya…..
Kallonta jama’a Suka fara cikeda son tabbatarda abinda take fada sbd kuwa idan itace jefata zasuyi a wutar kafin fireservice sugama kashe wutar….
Juyawa tayi tabar gurin da sauri kamar yanda Zinat ta sanar da ita karta Bari a kamata aikuwa tana zuwa da gudu ta fada motar suka ja sukabar gurin,
Murmushi Haj Zinat tayi sbd dama burinta da amfanin tura Na’iman sbd aganta asamu shaidar itace ta kunnawa gidan wuta,
Itace tayi kisan kenan Kuma takardunta na hauka bazata taba bayyanardasuba sbd kafin agano Na’iman batada lafiya ta Jima a gidan yari ko lahira shikenan ta rufe babin Turaki da matansa duka,
Dukiyar Na’iman dama tajima da zama tata, batada sauran wata matsala a rayuwar Kuma.
MAMUH
[7/10, 9:38 PM] +234 704 076 8969: Mamuhgee 56
Cikin bacci Kiran A Abdoul yashigo wayarsa,
Baya kwana da waya a kunne Amma ranar mantuwa ta sanyashi kwana da wayar a kunne.