NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL
NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL BY MAMUHGEE

Dayake baccinsa baiyi karfiba sbd Laylan daketa firgita cikin bacci gabaki daya ta kasa kwantar da hankalinta Kan abunda yafaru..
Daukan wayar yayi da mamakin ganin Kiran karfe hudu saura na dare.
Cikin tashin hankali da firgici duk da Yana kokarin controlling kansa Amma yakasa akaro na farko daya fasa kuka arayuwarsa gaban Turakin yace”
Turaki wutan gobara ya tashi a gidansu Sa’adah,
Abbansu da Sa’adah da sauran masu aikin duk sun…. Kasa qarasawa yayi sbd kuka Mai qarfin gaske dayake Yi…..
Da sauri Turakin ya miqe Yana zare Laylah daga jikinsa ya sauka daga Kan gadon Yana cewa”
Innalillahi wainna ilaihirrajiun,
Innalillahi,
Ganinan zuwa yanzu,
Masu kashe wutan sunzo?
Dan Allah ayi gaggawar fidda kowa daga gidan ganinan zuwa yanzu.
Jallabiya fara qal ya janyo ya saka Yana kokarin daukan keys ya fice Laylah Dake kwance tana jinsa ta tashi zaune gabaki daya jikinta yagama mutuwa ta kallesa daqyar ta iya hada kalmar”
Gidansu Abbane yakamata da wutan?
Dakatawa yayi batareda ya waiwayo ba yace”
Ki jira zanje na dubo.
Ficewa yayi yabarta zaune takasa ko qwaqwaran motsi sbd jikinta yagama Bata gidansune gobarar,
Wanna quncin dataketa faman ji tun safiyar ranar na wani abun ne kila zai samesu.
Yaye rufarta tayi tareda zuro qafafunta ta sauko dasu qasa ta miqe tsaye ahankali sbd bayanta dayake riqewa.
Kujera ta nema ta zauna tareda qurawa kofa Ido tana sake Shiga tsoro da fargaba.
Ko daya Isa hankali tashe wutar saura kadan agama kashewa gashi har anafar Kiran sallar fari a wasu masallatan,
Cikin tsananin tashin hankali da firgici daya Shiga shima yake tambayar Ina mutanen Dake gidan…
Momy da Abba da aka samu damar fitarwa da sauran Rai kawai aka nuna Masa sauran kuwa Babu Wanda Allah yayi zai fita wutar.
Wani mummanan jiri ne ya debesa aka taso za’a riqesa ya dafa motar Dake bayansa Yana cewa”
Innalillahi wainna ilaihirrajiun
Innalillahi wainna ilaihirrajiun
Ana Gama kashe wutar ba’a samu damar fidda gawar jamaar gidanba saida gari yayi haske sosai aka jeresu su uku.
Momy da Abba sun kone sosai ta yanda gabaki dayansu sun sabule musamman Abba har gwara momyn,
Daukarsu su tun kafin sallar asubar aka nufi asibiti dasu cikin gaggawa.
Sauran gawarsu Sa’adah ma asibitin aka nufa dasu.
Halinda A Abdoul yake ciki yasa hankalin Turaki sake tashi sbd Laylah komai itama zai iya faruwa da ita tana samun wannan mummunan labarin.
Haka yadawo jikinsa Babu inda baya rawa da tashin hankalin al’amarin…
Yana shigowa tana zaune inda take sallah kawai ta iyayi daqyar tadawo ta zauna tana jiran tsammanin dawowarsa.
Kallo daya tayi Masa ta sauke Kai sbd wata Ajiyar zuciya data tsinke mata batareda tasan Kota mececeba.
Qarasowa yayi ya wuceta yashige toilet yayo wanka sbd kayan jikinsa dasuka naci.
Bayan yafito Babu Wanda yayi magana acikinsu Saida ya shirya ciki suturarsa kafin ya zauna ya kalleta cikeda tsananin tausayinta da sonta,
Baya kaunar dagula zuciyarta da wannan mummunan labarin Amma Kuma Dole za’a a sanar Mata Dan Haka tea tafara Bata ta karba n
Ba musu ta Sha rabi ta aje cup din.
Magani ya sauka ya Bata shima ba musu ta karba ta shanye.
Kallonta yayi cikin kulawa da nutsuwa Yana Kuma kamo hannunta ya riqe Gam cikin nasa yace”
Qaddarar gobarace ta fadawa gidan acikin daren Amma….
Dan shiru yayi Yana jinjina girman munin labarin yace”
Kiyi hakaru ZAINAB bawa baya wuce kwanakin da ubangiji ya dibar Masa…..
Bata motsaba har lokacin idanuwanta na Kan bakinsa sbd tariga da tagama qulle zuciyarta cikin wani Hali na tsananin qunci ahankali ta bude Bakinta daya bushe Nan take tace”
Abbana ne ya rasu?????
Girgiza Mata Kai yayi yana kokarin janyota ya rungume cikin bayyanarda tsananin alhinin wannan tashin datayi gana ‘yayan mutane dasuka kone daga zuwa aiki murya a karye yace”
Abbanki na asibiti tareda Zainab….
Wani mummanan faduwar gabe ya risketa ta janye jikinta cikin mummunan yanayi da rawar da jikinta yafara dauka tace”
Anty Sa’adah ma na asibitin????
Girgiza Mata Kai yayi Kai tsaye yana cewa”
Kiyi hakuri Zainab
Sa’adah Allah ya karba ranta….
Kafin halinda take Shirin Shiga tashiga wani mummanan ciwon marane yataso Mata gadan gadan cikin tsananin azaba da tashin hankali..
Cikin sauri ya riqota Yana Kiran sunta Amma Ina ciwon nakuda ya taso Mata Kai tsaye ba shiri Kuma lokaci baiyiba.
Cikin gaggawa da wani sabon tashin hankalin akayo asibitin da ita itama
Suna dubawa kuwa Suka tabbatarda nakuda ce bakwaini zata Haifa.
Hankalin Turaki Bai taba tashi irin na ranarba sbd ganin bayan duk wannan abubuwan da rashin rayukan da akai ga Kuma nakudarta alokacinda ake cewa cikin Bai Isa haihuwa.
Koda su Anne Suka iso garin hankali tashe tuni Laylan ta haifi jaririyar ‘yarta Yar qarama da ita ansaka cikin kwalban aje yara irinta.
Laylah tasha matuqar wahala sosai gurin haihuwa duk da hakan tana haihuwa abin data fara shine sakin wani tsimammen kuka Mai taba zuciya na rashin Yar uwarta Rabin jikinta datayi,
Kuka takeyi sosai wanda tasaka harsu Annen kuka dasuma dama da kukan rashin Sa’adah sukazo,
Halima tayi kuka har idonta Baya budewa sosai.
A gidan umma Jamila data ringa Suma tana farfadowa Kan rashin Sa’adah da halinda Momy ke ciki akayi jana’izarsu aka kaisu makwancinsu take Kuma aka watse sbd Babu zaman gaisuwar dasu Anne zasuyi.
Iyayen hadiza dasuka zo suma anjaajanta musu wannan babban rashin kafin akayi musu duk wani Abu da akasan ya kamata ayin.
LAYLAH takasa kwantar da hankalinta sbd tasakawa ranta damuwa da qunci sosai.
Halima ma kukan rashin Sa’adah itama bazata iya barinsa yanzuba sbd sunyi wani irin shaquwa da sabo.
A Abdoul ko mahaifiyarsa datazo gaisuwa ta tausaya Masa sosai sbd Allah yasani tasa irin kaunar daukewa juna Kuma ita kanta ta yaba da nutsuwar Sa’adahn.
Anne taso kebewa ta sanarda Turaki maganar Laylah da aka gama tabbatarda itace ta bankadawa gidan wuta Amma ganin yanda komai yake neman cakudewa na halinda Laylah take ciki yasa ta dakata tareda fara Shirin komawarsu duka abuja hardasu Abban da Momy da za’a fitar waje Amma saisun fara Dan samun sauki tukuna.
Suna sauka Abuja daga airport motar asibiti aka dauki su Abba da momy aka wuce dasu
Sukuma da motar gidan Suka tafi Suma asibitin Suka nufa direct aka Kai baby aka Kuma admitting dinta.
Suna Isa gida Babu sauran Bata lokaci Anne ta gabatarwa da Turakin bayanin komai da komai sbd ganin yanda yariga yahau sosai akan tabbacin dasuka samu na Na’ima ce ta tada gobarar sbd wanna karon tabbas zai dawo da ita hankalinta idanma hauka takeyi..
Bayanan Anne da takardun daya gani da bayanin komai yasanyashi Kiran Dr faruk take agurin.
Cikin nutsuwa Dr faruk ya tabbatarwa da Turaki sakamakonsu na alluran da aka samu Sashen Na’iman dama sakamakon qwayoyin maganin allurar dasuka samu ajininta sosai tare Kuma da babbar illarsu ga qwaqwalwarta Dan kuwa zuwa yanzu idan Ana yimata ya tabbatarda qwaqwalwanta yagama juyewa gabaki daya.
Bai taba Jin takaici da baqin cikin kansa ba da rayuwarsa kamar yau daya samu wanna mummunan labarin,
Sakacinsa akanta yasa mummanar kaddarar aminya cutatar da rayuwarta ta hanya mafi Muni,
Meyasa Bai taba tsayawa yayi lamarinta kyakkyawar fahimtaba da zai iya gano lafiyarta da rashinta..