KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVEL

murmushi takaici yayi domin Indai wannan alkawarinne to an karyasa tun kafin adaukesa yace Allah ya bada ikon dainawan,kuna batawa kanku rayuwa ko bakusan Cewa duk abinda mutum yayi yana kuruciyar shi zai bishi har girma ba ko kunaso idan kun hayayyafa acewa yaranku kun taba busa wiwi ?girgiza kai sukayi yace Idan yaranku suka sha Ku ya zakuji hada baki sukayi wajen Cewa bazamuji dadi ba yace Idan Baku sani bama Ku sani wannan shaye shayen yana haifar da tabin hankalin,lalacewar koda da zuciya kuma tsaf zai kashe mutum. Ku a haka zaku hadu da Allah? Kuma kuna tunanin Idan an tafi a haka ba matsala?Ba Arabic Ba bokon?Allah ya Shirya….

Tafiyarsa ya cigaba dayi yana mai fada akan yadda matasa ke bata rayuwarsu.

Majalisar su malam yakubu zai wuce sukace salamu alaikum baban kowa barka da war haka murmushi ya soma musu sannan ya mika musu hannu sukayi musabaha.
Malam isa mai wankin hula ne yace ya naganka haka ne ? baban kowa yace kaide bari yaran yanzu basu rabuwa da kayan bakin ciki yanzu na…..

Malam saminu ne yazo yana girgiza kai alamun alajabi jikinsa a sanyaye ya zauna
Baban kowa yace haba malam saminu ya haka zakazo ka zauna bako sallama? inkai kayi haka ‘yan’yan mu kuma yaya zasuyi ?

Malam saminu ne ya cire hularsa ya ajiye kana yace wato wani abune yayi mugun jijjigani, Wai yar gidan malam ado salma akayiwa fyade saboda sakacin maihaifiyarta. fita tayi bayan magariba ba’a saniba uwar kuma da bata ganta Ba bata nemeta Ba sai da taga kusan goma ya wuce shine ta Sanar da malam adon. neman duniya an mata ba’a ganta Ba yau da asuba aka yadda ita koda aka kaita asubiti likitoci nata kokarinsu amma ina. yanxu yanzunnan rai yayi halinsa,Allah ya mata rasuwa!

Shiru wajen ya dauka kamin caaan malam sambo Wanda tun dazu baiyi magana ba yace Wai salma dai guda Dana sani yar shekara 6?itafa wannan salmar dai inji malam saminu
Salati suka rafka jikin kowa yayi mugun sanyi kamar an musu duka.
Allah sarki salma yarinya mai hankali da Shiga rai. Allah yaji kanta bari anjima sai mu hadu muje muyi masa ta’aziya nan dai suka Dan tad’a kamin malam Yusuf yayi gidansa.

Koda yake tafiya a hanya sai surfo masa gaisuwa ake ta ko’ina manya da yara. Atakaice de baban kowa mai jama’a ne.

Yana isowa kofar gidan sa, basheer mai shago yace baban kowa ina wuni,Lpy klau basheeru ya shagon?basheer yace Alhamdullah baban kowa yace masha dafatan dai yauma minal bata taba kowa Ba Dan yau da safe tace Mani Wai tun jiya akace suje su karbo sakamakonsu. Basheer yace Gaskiya baban kowa yau minal bata yi hayaniya da kowa Ba hasalima ko fitowanta bangani wadda nima abin ya bani mamaki da alamu dai kawattamu ta natsu(haka basheer din ke kiranta domin ya kasance abokin ya abubakar ne tun yarinta shiyasa ma yayiwa baban kowan karya Dan kar yasa wa ransa damuwa sosai)
Baban kowa yace to Masha Allah haka akeso ai ni bara in Shiga Daga ciki ko? Allah yayi albarka basheer yace amin.

Minal na zaune tana yanka kubewa taji sallamar mahaifinta hantar cikinta ne ya kada da gudu ta mike har tana tuntube a 360 ta fada daki,garin sauri ta barar da yakuwar da take yankawa innace ta haba er lele lafiyarki kuwa zaki barar mani da……

Bata ida maganar ba baban kowa ya shigo yana cewa inata sallamma Baku amsa ba Kamar ba kowa a gidan inna tace yi hakuri malam sannu da dawowa Wlh wannan yarinyarnance ta fada daki da gudu har tayi Mani bari banjika ba yi hakuri bara na kawo ma ruwa
Takalmin sa ya cire ya zauna a tabarmar dake shinfide a tsakar gidan yana Cewa halan wayanta aka kira take wannan gudu , inna dake shirin bude randa domin sachet watern su ya kare tace anya kuwa?hira fa muke daga jin sallamarka ta rusa da gudu Kamar taga aljani,baban kowa najin haka jikin sa yayi sanyi bayason irin faduwsrnan da yarda keyi a makaranta domin Hanson tayi karatu ta inganta rayuwarta

Yace takarbo sakamakon jarabawar tasu kuwa inna tace eh ta karbo dazu gasucan yana kan yana kan taaga(window),tashi yayi jiki babu kwari ya dauko ya Duba aiko Kamar yadda yace ne ankuma na 48 tazo acikin su 52 a Dan fusace yaje kofar dakin yace aminatu me kikeyi acikin dakin nan,minal tace Riga make canjawa yace inba so kike na Shiga Ba maza ki fito tace baba aradu Babu Riga ajikina wanka make shirin yi yace Kamar da haske rabon da Kiyi wanka keda kanji Ba tare da dance Kiyi Ba yanzu shekaru 6 kenan amma shikenan ni bara in dubo sakona waje.

Oya show some love
By voting,
liking,
sharing
and
commenting

Tnxs for reading

26th April, 2019

Mzz untichlobanty💕
[1/11, 1:09 AM] Mzz_Untichlobanty💞:

🏆🏆KURUCIYAR MINAL🏆🏆

🌹by mzz_untichlobanty🌹

🍀CHAPTER 3🍀

Sanda ta kara kusan 5min sannan ta leko da kanta duk ta hada gumi saboda rashin gaskiya

Saukan rankwashin da tajine yasa ta sankare a wurin na wani sakanni.

Durkushewa tayi a wurin tana tutturo baki kamar zai taba kofa.
Baba ne yace rufi min baki kamin in kara miki,maza tashi.

Mikewa yayi tana zuzzunburewa tace haba baba ko Dan wannan rankwashin da kake samani kamar abinci Ba dole na KASA kokari Ba kana taba min CPU na bakasan Cewa itace masarrafin Dan Adam ba?

yace yimin shiru kamin in da’da maki wani yar kaniya kawai,me kwakwalwar kifi Allah dai ya bude maki wannan toshesshiyar kwakwalwar taki.

kuka ta fara yi tana buga kafa ni Gaskiya baba kwakwalwata ba a toshetake baaa😭 inna tace ni yimin shiru karki taramin makwabta ehe.

Murya ta kara baba yace bari kiga ikon Allah mikewa yayi ya dauko sanda.
yanda Kasan Anyi ruwan sama an dauke tsit ta shanye kukan da takeyi tana tsitstsilla idanu tare da sheshsheka baba yace banson jin sheshekar nan. Ki natsu bari inga tsiyar da kika shukowa mutane wannan karan.

Mutum bashida aiki sai fada ni Nayi mamaki ma yau kusan sati 2 ba’a kawo kararki Ba.
Turo baki tayi duk yasha mai sai yalki take tace yo ai dannayi mafarkin na mutu ne kuma ko yanxu ma Ba fasawa nayi Ba.

Kallonta baba yake har ta ida maganan ta already ya Ciro takalmi Dan haka ya lafta mata.

papers din ya fara dubawa yaga  subjects 2 ne takeda A amma saura Wai sai a slow saide rubutun nan war inka gani zaka dauka wata Dr ce tayishi sai ka karantawane kaji Kamar kayi kuka.

takaicin rashin kokari na diyartasa abar kaunarsa ne ya taso mai.

Kansa  kawai yake girgizawa saboda takaici bazai musaba Idan akace masa Dan primary five ma yafi yar tasa kokari.

Tsawa ya daka mata ke zonan !
Simi simi taje ya kalleta sannan yace yanxu ke ahakan zaki tafi makarantar gaba?ki Duba fa gododuwar banza da wofi. Murmushi tayi
inna tace Allah zanci mutuncinki ana miki fada kina dariya saboda kin daina mutane ko? Tace Toh Toh Toh ni inna me Nayi ? Dakuwa inna ta mata tace kaniyarki kikayi

tace to yi hakuri bazan kara Ba shikenan aiko?yauwa inata Dan Allah ki siyan awara?harara inna ta banks mata tace ba’a siya dinba
Baba dake jinsu  ya tattare takardun yana cewa ace mutum anmai repeat har sau biyu amma bai gyara ba nasan duk ajin keda zaliha kun fisu girma amma kanku Kamar kifi har gara ita akanke.
antara dakikai biyu a aji daya bakuda aiki sai ciye ciye kuma da kunada kokarinku tunda kuka fara Hulda da wannan fatiman shikenan lamuranku ya tabarbare.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button