KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVEL

Aranta Addua take tana cewa Allah indai Kaine Allah ka dawomin da farouq Dina jin shiru yasa ta yarda da maganar ummi. Allah sarki anan ummi ta daura ta akan keken bera.

Tun daga lokacin idon zakiyya ya bude ta bankare itama abin kuwa ya kara karfi ne bayan ance an nemi mardiyya an rasa. Tundaga lokacin ta sauya saide dukda haka bata taba yin zina ba.

Bayan watanni aka gano ummi nada ciki. Hakan yayi sanadin zuciya mahaifinsu ta buga. Hajiya badawiyya kuwa tasa aka barar da cikin. Wasa? wasa islamiyar ma suka watsarta bokon ma zakiyya ce ta karashe ummi daga ss2 ta tsaya._

Koda zakiyya? ta gama bada labarinnan ta jikawa minal Riga da hawaye.? Lallashinta minal tayi kamin suka cigaba da sabgoginsu.

Koda zakiyya ta tambayi yazeed bai hanata zuwa gidansu summy ba domin dadi yaji atleast ta shiryu.

Jibi nayi saiga summy ta tazo daukan zakiyya aiko suka wuce gidansu su summy tunda suka shiga zakiyya yaji hankalinta bai kwanta ba. Drinks aka kawo Mata tasha kadan daganan summy tace “Muje ko? Tana dakinta ne” binta zakiyya tayi a baya haka dai har suka isa zuwa dakin suna shiga summy ta rufe kofa tare da wulli da key din. Kallonta zakiyya tayi tace ban gane ba Menene? kuma haka? A zafafe sumaiya ta hada bakinta Dana zakiyya atake zakiyya ta shiga wani yanayi saboda drink din data sha………

TOH FA! SAI KU BIYONI A CHAPTER NA GABA DOMIN JIN YADDA ZATA KAYA A TSAKANIN SUMAIYA DA ZAKIYYA.

NA GODE SOSAI DA HAKURINKU NA RASHIN JINA 2 DAYS. INA MATUKAR YINKU IRIN TOTALLY DINNAN.

TAKUCE KARAMARSU BABBARSU

miss Untichlobanty ?

26th January, 2020.

??KURUCIYAR MINAL ??

?by miss Untichlobanty ?

?CHAPTER 70?

Rufe ido zakiyya tayi sakon da sumaiya ke aika Mata na ratsa and then it click to her Cewa wannan abin zunubi babba.
Babu shiri ta hankadeta tare da cewa me haka sumaiya ina maman taki?. Dariya summy ta sheke dashi tace shegiya ni. Ji muryarki yadda kike magana kamar yar kwaya tsabar jarabar Dana tado miki, wa yace miki inada uwa? Matsowa tayi kusa da ita tana yauki tare da shafo Fuskar zakiyya tace haba my zaky basai mun tsaya muna ja inja ba. Mari zakiyya ta yarfa Mata tace kin bani kunya wallahi am ashamed ashe ke fasika ce ban sani ba?kazama,dakikiya kuma jahila? Ke nayi miki kama da yar iska ne? Dariya summy itama tayi tace hmmm lallai ma zakiyya bakisanni ba.

Marinta ta Rama tare da cewa ince ke wayaiya gaki matar manya ko? Kiyita dressing kina bude tsiraici, toh kin budo ni kuma na gani kuma ya min,kuma sai na samu. Tsaki zakiyya taja ta dauko key din da summy ta ajiye ta bude kofar tana kokarin fita summy tace me zakice idan nace kina sa kafarki wajen dakinnan zaki rasa uwarki.
A zafafe zakiyya ta juyo tace ke banson hauka kina jina ko? Karki kuskura kisa uwata a shirmennan naki. Dariya summy ta fashe dashi da kaji amon sautinta babu imani a cikinsa. Tace uhmm su hajiya zakiyya manya!dariya ta kuma fashewa dashi sai lokacin zakiyya ta lura cewa summy ta girmeta sosai,sannan ko dacewa basuyi a matsayin kawaye ba. Zuwa yanzu daga skin tight sai bra ne a jikin summy Wanda zakiyya bata ma San yaushe ta cire kayan ba. Kallon jikinta yayi taga hijab dinta ne ya yamutse.

Kauda kai tayi daga kallon summy dake tunkarota hannunta rike da tablet, nuno Mata video call ne. Mamanta ne a daure a wani store ta jigata sosai da alamu duka aka Mata bakinta har yau yake tsiyayarwa. Tace zakiyya ki taimaka ko me sukeso kiyi musu. Zasu kasheni ke daya zaki iya cetona. Ki taimaka ko biya musu bukatarsu ! Karki tuna abubuwan danayi miki a baya nasan ban kasance uwa ta gari a gare ki ba. Nayi miki alkawari bazan sake ba zan nuna miki soyayya ta uwa wacce ko wacce a diya ke bukata…

Lokacin zakiyya ta Dade da jikewa da hawaye itakam ta shiga uku tana tsaka me wuya ta bangare daya ran mahaifiyarta dayan bangare kuwa hakkin Allah. Shiru tayi tana tuno maganganun da tayi da minal wata kila zata samu mafita a ciki.
Summy tace kamin na kirga 3 ki yankee shawara. Bindiga aka saita Akan mommy take ta fara cewa don Allah Allah zakiyya dan Allah.

Summy tace 1…………. dogon nazari zakiyya ta fara shin mommy ta cancanci ta sabawa Allah saboda ta cecota? Idan ma ta ceceta akwai probability cewa bata tuba. Toh amma uwa ce fa uwa?

Summy tace 2………. yanzu idan tana cikin sabawa Allah ita da mommyn suka mutu dukansu fa ? Asara bibbiyu kenan. Kai Anya kuwa momy ba so take ta danna kaina a ruwa ba in mutu ina madigo ta mutu tana mushrika? Ajiyan zuciya ta sauke tunowa da yadda mahaifiyar Tata ta dinga bin bokaye har kwanciya tayi dasu duk saboda ta hana mahaifinsu yi Mata kishiya.

TAUUUUUUU !! Taji hakan yasa ta tsorata sosai ta saki tablet dake hannunta summy tayi saurin cafewa tare da cewa ke ya haka zakiyi min asara. Kallon cikin wayan tayi tace wow ji yadda kwakwalwarta ya fito. Don Allah ku fasamin cikin ko naji dadi a raina. Saukar bullet kakeji tace ku cire hanjin ku saka roba zan aikashi wani gur koda ta juyo ta kalli inda zakiyya take tuni ta sume. Tabe baki tayi tace ke kika jiyo dama nima ba bukatarki nake ba. Wayarta ta dauko ta danna Kira ringing 4 yayi kamin aka dauka. Tace hmmm AI tayi taurin kai Dan haka dayan option din mukabi. Allah keson ya ceci Aurenta. Kyaci tayi tace wallahi madam naso ace ta bada hadin kai na rakashe kuma wallahi na saita camera din yadda zai daukemu dakyau da kawai sai mu rife fuskana my sambadawa mijin. Tsaki aka ta dayan bangaren tare da cewa barta hakan ma ya isheta zamuyi tunanin wani abin. Dariya ta kyalkyale dashi tace zakiyya wallahi ko kinki ko kinso sai kin rsbu da yazeed.

Summy tace ma ya zamuyi da ita? Tace Kira su kyankyaso kice su dauketa su yar a wajajen gidanta amma karsu karasa saboda kinsan security din wajen. Suyi using wayanta suyi contacting din wani yazo ya dauke ta sai su ajiye Mata a wajen. Summy tace okay amma kamin a mayar da ita zan iya ……… kingane AI.

Ta dayan bangaren tace ke banson shashanci ku miyar da ita nace bakisan inada kishi ba ko? Sgagwaba dummy ta fara tace kai my luv kishin ruwa fa zan mayar kinsan yanzu bakyanan kuma kinsan yadda nake. Ajiyan zuciya madam din ta sauke tace wallahi kamar kinga zuciyata nima na takura da bakyanan amma soon?kinji ko? Summy tace okay sannan suka kashe wayar.

Haka ko akayi aka yarda zakiyya tare da kiran number din minal saboda shine last call dinta. Nan fa minal ta diburbuce gashi yazeed ya tafi aiki. Ta dinga kiransa baya picking saboda yana meeting. Gashi duk sojojinsa da ta sani ya tafi dasu kuma bataso ta fadawa mom hankalinta ya tashi. Fitowa tayi Joshua yana ganinta yace ma barka da fitowa tace yauwa so nake ka kaini……….

Nan ta kwatanta masa yace ya gane,haka ita da tala suka dauko zakiyya niki? niki, sojojin zasu sa Masu hannu tace su barshi tala ma ta isa. Bayan sun dawo suka kaita dakinta daidai lokacin yazeed yayi calling back. Dauka tayi tanata kuka hankali? yazeed a take ya tashi tun kamin ta fada mai matsalar. Tambayan duniya yayi Mata tace sai ya dawo zata fada mai. A Emergency ya dawo gida daga shi sai luku. Koda ya iso already idonta ya kumbura,riko hannunshi tayi har dakin zakiyya salati ya fara tare ta cewa me ya sameta haka ya naga goshinta a fashe? Bayanin abinda ta sani minal tayi. Take ya bada order yace a duba anguwar gaba daya daga sunga basu yarda da mutum ba a kamoshi kawai ko Waye sannan ya Kira dr Muhammad. Bayan ya dubata yace firgici ne yasa wutanta daukewa, amma zata iya tashi at any momen…… bai karashe ba sukaji ta fashe da kuka kanta sukayo baki daya. Yin duniya anyi taki yin magana kuma taki daina kuka saboda a firgice take.
Gaba daya ranan dakyar suka karashe, hatta su sahir ko wasa basuyi ba kowa cikin damuwa jugum. Mom kam kasa magana tayi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button