KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVEL

Minal ma ta fara kwaikwayanta abin har gwara na Zally domin minal ita nata Kamar agwagwa😂.
Ana cikin haka aka fara ruwa Kamar da bakin kwarya
Yan matanka suka nemi wurin buya domin kada ruwa ya musu duka,
amma sanda aka sami matsala domin ya ca’be musu ado
Abangaren yazeed kuwa parking yayi domin ruwan ya tsagaita ganin zakky baby ta ‘bata masa lokaci gashi ko kulashi batayi Ba balle yasa ran zata bashi hakuri abin sai ya bata masa rai
Yace
Zakky what’s all of this ?
Tace
Meaning?
Yace
first you wasted my time,also came out walking like a snail and you can’t even apologize?
Tace
What wrong have I done that I will apologise? Is it wrong to walk majestically?
Look that’s fashion
She said that Prolonging the fashion
Yace
Fashion my foot,the hell with it
Alokacin ruwan ya tsaya kunna motan yayi
Ayayinda zakky ke Cewa
Look idan ka fito dani just to disgrace me ne am not in the mood please hurry up ma ni am starving gushhh
Wani wawan acceleration ya kwasa ya kure speed din motan shi dama ba mutane akan titin
Alokacin dadai su zaliha sun fito daga Inda suka labe domin su tsallaka titi takalmin minal ya Tsinke tsallakawa zaliha tayi koda ta juya ta hango minal bata tsallako Ba tace Ki tsallako kamin abawa motocin Hannu .
Minal tace ke aradu sai na gyara takalmi na.
Zaliha tace wallahi ko ki tsallako ko in tafi in tafiyata minal tace da nace ki jiranine?
Tsugunawa tayi ta cire takalmin ta fara kokarin gyarawa yayinda zaliha tayi tafiyatta tana mai jin haushin minal din.
Neman kara minal ta farayi bata zamu Ba aiko tana Daga kanta taga wani a tsakiyar titi Dan haka Ba tare da nazari Ba ta hay kan titin domin burinta kawai ta gara takalmin ta.
Alokacin kuwa aka bada Hannu kuma daidai lokacin fada ya kaure tsakanin zakiyya da yazeed CeCe kuce suke tayi yana hankalinsa kenan daga titi yana Cewa zakky don’t try me this evening
Minal kuwa ta dauko karanta tana kokarin gyara takalmin tare da tafiya a hankali akan titin domin itama ta tsallaka taga mota a guje yana iyowa kanta
Duk kayan cikinta sanda suka kada.
Daidai lokacin yazeed ya lura da ita kokarin kaucewa yayi ya fada cikin wani Dan rami Wanda ruwa ya taru kuma ya daki motan wani
Tun daga sama har kasa yawatsawa minal ruwa ta sule ta fadi kasa yayinda mai dayan motan ya fito………………….
Hahhhh finally
This is my sallah gift to u guys hope you like this chapter
NOTE:
All pictures of characters shown here are not related to the story.
Kindly share, and comment thank you
Much love
4th June 2019
Mzz untichlobanty💕
[1/11, 1:33 AM] Mzz_Untichlobanty💞: ðŸ†ðŸ†KURUCIYAR MINALðŸ†ðŸ†
By miss untichlobanty
ðŸ€ðŸŒ¹CHAPTER 9🌹ðŸ€
Juyowa yazeed yayi ya kalli zakiyya yace oh gush,look at the mess you cause!
Minal ko lokacin da ta d’aga idonta taga Wanda ya watsa mata ruwa ya juya yana magana da wata(saboda motar Ba ita yake using ba babu tinted)abin ya mugu bata haushi
Minal ta fara magana a hankali lallai ma mutuminnan ya watsa mini ruwa sannan ya tsaya magana da budurwarsa?
Mikewa tayi zata zazzaga masa rashin mutunci daidai lokacin me motan nan ya fito yazeed dake shirin fitowa shima yace bawan Allah kayi hakuri….
Mutumin ne yayi saurin katseshi ta hanyar Cewa wa make gaji Kamar captain yazeed murmushi yazeed yayi yace nine Dan Allah a Duba ma asarar da Nayi sai inbiya ga card dina ya fadi hakan yana kokarin bawa katinsa mutumin yace ka barshi kawai yallabai ai paint nema ya Dan kurje Gaskiya Muna alfari dakai a ka sannan Allah ya kara yi maka jagora yazeed yace ameen amma dan Allah ko wannan ne ka karba mutumin yace waneni ranka shi Dade kuda kuka bamu rayuwarku Dan kukaremu shine har sai na karbi kudinka Dan ka gurjemin mota?ai kake wallahi Ba Komai sai alolacin ya lura da zakiyya cikin fara’a yace ina wuni madam ? Ya tsine tayi kamin kasa kasa tace lafiya tana mai kauda kai.
Dariya mutuminne ya dauke yace ranka shi Dade zamu iya yin selfie? Murmushi yazeed yayi yace Ba matsala. Quick selfie mutumin ya musu sannan ya Shiga motarsa yana mamakin abinda zakiyya tamai dukda ko bai Santa Ba amma da alamu tanada alaja da yazeed din.
Yazeed ko da ya mance da ya watsawa minal ruwa dukda ko laifinta ne tana tafiya ahankali akan titi amma shima harda laifinsa daya biyewa zakiyya ya kunna motarsa zai wuce minal tayi saurin riko hannun kofar
sauke glass yace baiwar Allah dan Allah Kiyi hakuri ban lura bane wallahi hankalina ne ya sauke Daga titin amma kema hada laifinki kina tsallaka titi bakya kallo ki kula Dan Allah
ya fadi haka yayinda ya zabgawa zakiyya harara yana kokarin Ciro kudin a aljihunsa.
ganin zakiyya ta fashe da dariya, abin ya kara bawa minal haushi
Su watsa mata ruwa amma ko su kallo Inda take yarda wani tsayawa Suna surutu da photo da wani mutumi sai kace Yan film bayan sun gama Iskancin nasu zasu ta fita rikosu shine ya wani kwame a mota yana bata hakuri
Sannan budurwarsa tana mata dariya
kwafa minal tayi kamin ta kama kwankwaso ta fara jijjiga tayi kicin kicin da ido
Tace wallahi Allah ya isa na ya za’ayi Ku watsan ruwa kuma kunai mini dariya
Babu abinda yazeed ya tsana Kamar ayi masa Allah ya isa
Hakan yasa shi mugun mamaki amma ganin fiskanta kwalliyar ta cabe bakinnan sai yalki yake Kamar tasha man gyada
Abin ya basa dariya amma ya shanye,50k ya miko mata yace gashi ki siya sabulu kije a Duba ki kiji kanwata ?
Minal tace me kuddin zai min kuma babu wani batun Kanwarka ni karkayi min zakin baki Dan bazaiyi aiki Anan Ba. Ta fadi hakan sannan ta murkutsa baki
The girl is now getting on his nerves
He just pressed his car accelerator trying to leave
Not yet Mr.yazeed abdulmajeed
Wani tsalle minal ta daka ta sake rike hannun kofarsa
Zakiyya babu abinda take sai dariya Dan ita ganin clown takeyiwa minal,fadan nasu yana kayatar da ita hakan yasa ta dauko wayarta ta fara video.
Malam ya zaka watsamin ruwa ka kusa bigeni har na fadi kasa amma ka hakimce a mota kana miko mini kudi me zanyi da kudinka?ai fitowa zakayi ka Duba Lpy ta.
Fitowa yayi a harzuke
Kusa da ita yazo ta daga kanta
Wai Wai Wai wannan dakyar in takai kafadansa ma tabdi
Ai bata lura gardi bane wannan sai sai basamude ma ai da batayi masa rashin kunya ba
ta wuce abinta salin alin babu wata hayaniya yanzu wannan Idan ya mata naushi daya ai har lahira.
Gaskiya dukda tana jibgar maza bazatayi koda kuskuren tunanin dukan shi Ba balle ta aikata
Yazeed yace ke wa kikeyiwa fitsara?
idonta ya ciko da hawaye a take tsoro take kar ya daketa Dan taga ya dunkule Hannu jikinta na rawa ta girgiza kai
Yace Nayi kama da sa’anki?
Tace a’a
Yace shine kike min rashin kunya
Tace ai kai ka jawowa kanka kana Abu Kamar baksan darajar dan Adam ba
Ya dalle mata baki da yatsansa
Tace Allah ya isa na wallahi bazan yafe makaba kuma bullukutut bakar mutuwa.
Yace ke zan canja miki halitta fatace Bismillahi
Daga hannu yayi Kamar zai mareta dashi bata dukan mata tace wallahi kana marina zan kira Yan sanda kaga wayata?
Yazeed yace to sai me dankin kirasu?
Tace sai en sandan su kama ka
Yace idan ni kakansu nefa?
Tace sai sojoji su kamaka
Yace idan ni ubansu ne fa?
Tace da gaske nake fah zan kirasu inka tabani
Ya matso kusa da ita yace Bismillah
Tace a ah fa
Ya kara matsowa yace ki kira mana! Ya fadi hakan da kakkausar murya
cire dayan takalminta tayi ta rike a hannun dan ta lura zaliha da haske ta tafi tun dazun ta tafi tun dazu