KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVEL

Can mutaneku suka farga dubawan da zasuyi sukaga har ta kwashe kwanikan ta fice. Hannun minal yazeed ya riko ya daurata a cinya yace my minal kenan kinsan nayi missing din lips dinki ko ? Murmushi tayi tana Dan sauke kai tace nima domin ta dan rage jin kunyarsa. Pecking lips dinta yayi yace minali na, tace na’am yazzy baby yace akwai wata magana da nake so muyi. Tace ina jinka yace inasonki kuma kema kin sani saide kaddara ta Riga fata domin bazan danne miki hakki ba. Ki saurareni da hankalin fahimta inaso ki sani wannan Abu daya sameni daga Allah ne, hankalinta ne ya fara tashi ganin yana shirin kuka. Shafa kanshi tayi alamun yaci gaba yace ba… zan iya biyawa mace bukatarta balle ta kai ga a Sami rabo. In hankalin minal yayi dubu toh ya tashi amma sai ta dake tace innalillah wa inna ilaihi raji’un!kayi hakuri insha Allah komai zai daidata. Riko hannunta yayi yace inaso ki amince na rabu dake ki samu wani miji kiyi aure domin ko a musulunci zamanmu akwai matsala. Rungumeshi tayi kam tana kuka tace wallahi idan ka kara tunanin rabuwa dani saina falls maka Mari ko da haihuwa ko babu ni zan zauna dakai har abada. Kuka take sosai domin ta tausayawa yazeed saboda yasan yadda yake burin samun haihuwa. Kuka tasha sosai kamin yazeed yace taje ta kiramai zakiyya.

Koda zakiyya taga idanun minal tun daganan tasan akwai matsala cikin tashin hankali tace minal me ya faru? Fada kukayi?girgiza kai kawai tayi kamin tace yana kiranki sannan ta wuce dakinta.

Sallama zakiyya tayi ta shigo amma me? Yazeed ma dai a wargaje take tunani ta fara to kodai sakan minal yayi?
Jiki babu kwari ta karasa ta zauna. Bayani ya Mata yadda yayiwa minal amma batace komai ba can ta sauke ajiyan zuciya tayi salati kamin tace faduwa ce tazo daidai da zama domin kuwa nima ba Dade inaso inzo muyi magana dakai. Bazan boyeta ba tunda nake dakai ban taba gane cewa banasonka ba saida na shiryu,shi yasa ko jini banson hadawa dakai,ashe duk zamannan da muke kudinka da family name nakeso. Da badan kuskurena ba da yanzu kaga jininka domin ni ke Shan magungunan hana haihuwa a baya koda aka Sami kuskure ciki ya shigeni zubarwa nayi. Ina rokonka sa ka yafemin kusa kurai ba bazan kara ba. Tana kaiwa gabannan ta fashe da kuka hawaye ne ya silalo wa yazeed. Indai hakane toh fa zakiyya ta cuceshi amma ya zaiyi ? Dole ya yafe Mata tunda tayi nadama. Paper da Niro ta miko masa tare da cewa na gode da irin soyayyar daka nunamin. Tabbas baka tauyemin hakki ba kuma kikayi tunanin zan rabu dakai Dan abinda ya sameka ne ah ah zan rabu dakai ne saboda na cutar dakai kuma Allah ya kawo me kula dakai kiyimin izini in rubuta takaddar tunda kai hannunka da matsala. Gyada Mata kai yayi yace sau daya ya sake gyada kai. Abin abin tausayi rungumeshi tayi sukayiwa juna dogon sumbata kamar karsu rabu amma dole ta rabu dashi saboda ta kuntata mai dayawa yanzu itama gara tayita dakon sonshi a boye tunda ta nuna batasonshi kuma karya take dukda ko tanason dukiyarshi a baya suna shima tana sonshi. Kawai de ta biyawa son zuciya ne tare da hudubar Sheridan.

Haka ta fito wujiga wujiga ta shiga nata dakin itama sai kuka. Ashe haka zafin zawarci yake? Yanzu shikenan batada aure? Anya batayi kuskure ba kuwa? Ranan ko abinci bataci ba.

Koda yan uwa sukaji lamarin abun Baiyi dadi ba. Barin ma su inna yanda suka nuna kulawa domin da ace wasu iyayen ne rufe ido zasuyi wuce sai an sako musu yarsu, amma su cewa sukayi tayi Wanda yayi Mata idan tanaso ta zauna indai bazata cutu ba.

Wata rana zakiyya tana kokarin fita aiki domin yazeed ya bata manager of art and designing na company din kaya. Sanye take cikin Arabian gown tayi rolling? domin yanzu shine dressing dinta. Tana sauri bata Ankare ba sukayi gware da Jamal? Wanda keta sauri shima Dan yanzu shi da lukman ke managing companies din yazeed hakan yayi sandiyyan zubewan files dake hannunshi. Tasa hannu zata kwashe shi ma yasa hakan yasa ya riko hannunta a take suka hada ido. Wani yanayi ya fara shiga domin tun kamin yazeed ya auri zakiyya yake sonta domin shi yanason Mata masu kwalisa da wayewa (ba wayewar data sabawa addini ba) tuni boyayyar soyayyar ta yunkuro. Zakiyya kam wani bugo zuciyata yayi Wanda abin ya bata mamaki domin bata taba jin irin haka game da Jamal ba.

Kallon hannun nasu dake hade Dana juna tayi shima ya kalla da sauri ya saka tara da Sosa kai ya bata hakuri. Hakurin itama ta bashi kamin ta fice domin duk wani second da takeyi a wajen bugun zuciyarta karuwa yakeyi.

Koda ta fita motanta kin tashi yayi gashi tayi latti sauran motocin kuma duk sanyi kura saboda hunturun sanyin nan da muke fama dashi, wabi sonja tasa ya wanke Mata tana tsaye sai duba lokaci take Jamal yace kinyi latti ko? Zo muje tare in yaso sai a kawo miki motan kinga dai this is your first week at work. Badan ranta yaso ba haka ta shiga suka fice.

Shiru Motan ya dauka Jamal nason ya Mata magana amma ya rasa mai zakice can yace madam zakiyya yau kinyi kyau. Murmushin take tayi tace na gode dukda ko deep down taji dadi amma ba wannan bane a gabanta. Can yace dan Allah in tambayeke mana tace ina jinka yace wai shin yaushe zaki kara aure idonta ne ya ciko da kwalla Wanda Jamal ya lura dashi hakan yasa yace kiyi hakuri bansan tambayan zai bata miki rai ba. Girgiza kai tayi tace AI babu laifinka daganan kowa yaja bakinshi yayi shiru har suka isa kowa ya wuce office dinsa.

Akwana a tashi yazeed ya daina aiki da keke ya fara using sanda sannan ko ina na jikinsa ya warke sai abinda ba’a rasa ba. Zaune yake kan gado yana nazarinsa minal ta fito daga wanka daga ita sai towel yace my beautiful wife wish….? tare da kashe Mata ido daya sarai ta gane me yake nufi amma tace you wish what. Janyota yayi yace DA SO SAMUNE mu raya sunnah nida ke a daren yau. Murmushin karfafa guiwa tamai tace komai yanada lokaci AI . Shafa kanta ya fara yace yau nayi magana da mashkur kuma yace akwai wani dr daya sani may be he can help, a Germany yake so get ready jibi zamu tafi. Tace okay Toh mikewa tayi ta fara cire masa kaya domin shima yayi wanka. Tsokanarta yake yana fadin iye matar yazeed kefa kiba ma kikayi abinki kamar kazar gona ok? Turo baki tayi tace wallahi karka kara cewa inada kiba idan ba haka ba tam. Yace idan na kara menene hukunci na? Ashararan wasa tamai tace kara ka gani.

Lokacin daga shi sai boxers yayinda take tsaye a tsakanin kafafunsa hannayenta zagaye da wuyansa tunda ta gama cire masa kayan. Gyara zama yayi yace minal yar lukuta. Pecking lips dinsa tayi tace wannan hukun ci da dadi yake kice in yita fada. Ya a
Sake cewa minal mama lutiya wannan Karan kumatunsa tayi pecking, maimatawa yayi Aiko ta fara masa cakulkuli tana cewa wannan shine ainihin hukuncin garin sai ya Rama ya tube Mata towel aiko tayi saurin gyara tare da cewa waiyo. Dariya yayi yace kwantar da hankalin ki ko duka matan duniya zasuyi tsirara babu abinda zan iyayi a halin yanzu. Murmushi kawai tayi kamin ta taimaka mai ya shiga toilet din jacuzzi ya shige abinsa da wandon shi yace ta tsaya a waje ya cire sai ta karba tunda ita uwar kunya ce.
Koda ta karba ta jiya zata fice ya janyota ta fantsama cikin ruwan sannan ya cire towel dinta dayasha ruwa yayi firo dashi. Kokarin tashi takeyi yace bara in zuba ido dakyau kina mikewa inga bulus kinga yanzu rose dinnan da muka zuba akai ya rufa miki asiri. Kuka ta fara mai………

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button