KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVEL

Juyawa tayi tace Allah Alhaji na? Yace kwarai ma kuwa yanzu yadda zamuyi dasu Dan nima a shirye nake tsanani dai ace wuta za’a samu toh ni ALHAJI TUKUR GADON ?AYA na bada ticket din aljanna ta Dan in kuntata ma ahalin ALHAJI ABDULMAJEED UMAR. Dariya suka fashe dashi tace kaga mu hanzarta domin na koma gida daga nan suka shiga aikata ashararancin su.

WANENE ALHAJI TUKUR GADON KAYA? WANI ATTAJIRIN MAI KUDI NE WANDA SUKAYI TASHE TAREDA ABDULMAJEED WATO BABAN YAZEED INDA YAKE DAUKE DA MUGUN HASSADA MA ABDULMAJEED SABODA YA FISHI YIN NASARA.
DA FARI JEEDMAR A BAUCHI SUKE DA ZAMA TAKURAR DA TUKUR GADON KAYA YA MUSU YASA SUKA KOMA GOMBE NAN MA YA BISU,SUKA LULA ADAMAWA,YA BISU SUKAYI KANO, YA BISU SUKAYI, SOKOTO LOKACIN AN HAIFI YAZEED AMMA YA BISU NAN MA SAI SUKA KOMA ABUJA TOH ANAN NE SUKA ZAUNA NA SHEKARA 4 KAMIN YA SAKE BIYOSU SUKA KOMA KADUNA ANAN NE AKAYITA TA KARE TUNDA ABDULMAJEED DIN YA MUTU BA SHIKENAN BA? TOH ASHE
DAI BAI HAKURA BA GASHI KUMA YA SAMU WACCE TA FISHJ DAUKAN ZAFI LAMARIN SAI YADDA ALLAH YAYI.

Ina mai lallashin ku na rashin jina da kuka yi abubuwa ne suka Dan taso min da fatan za’a min uziri?

Shin me zaku iya cewa gameda batun Alhaji TUKUR GADON KAYA? Ya kuke ganin lamarin nan zai kaya a tsakanjn su ?

Shin in karar da littafinnan da wuri ko kuma acid gaba da gashi?

TAKUCE KARAMARSU BABBARSU wato

Miss_untichlobanty ?

14th February, 2020

??KURUCIYAR MINAL??

?by miss_untichlobanty ?

?CHAPTER 75?

Sauri minal keta yi tana tsallake steps da bibbiyu saboda lattin da sukayi domin yau jirginsu zai daga zuwa Abuja inda zasuje baban jeedmar group kuma anan ne za’ayi meeting din tallafawa yazeed kamin government ta wankesa.

Bude Mata kofa kurtu yayi ta shige luku ya finciki mota. Ba bata lokaci jirginsu ya daga sai federal capital territory of Nigeria.
Koda suka isa yazeed bai tsaya isa gida ba direct jeedmar group ya nufa. Sunayin parking ya fito cikin kwarjini da haiba yana? takunsa mai daukan hankali gwanin ban sha’awa. Dukda cewa a cikin damuwa yake hakan bai hana kyawunsa fitowa ba.

Ezekiel da lukman kawai aka bar masa a matsayi escorts dinsa sai masu gadin gidansa shima an rage wasu daga cikin su. Haka masu yin hidima duk an rage masa kuma duk munafurcin Alhaji tukur gadon kaya ne.
Tun daga bakin kofa ake gaishe sa tare da bada buda hanya yana zuwa bakin kofan shiga kofan yace “new individual detected please wait ……” scanning iris dinsa yayi kamin yace “welcome president it was nice you visit kindly put your thumb”
Saka thumb din nasa yayi take kofar ta bude masa gaba daya directors sun jeru Dan haka yana shigowa suka bi bayansa.?
Files suka fara miko masa ya daga musu hannu. Suna shiga gaba daya uncles din nasa suka Mike Yana zama suma suka zazzauna. Yace good day to you all ! As we already know we are here to discuss…….. nan ya musu bayani ya sanar dasu duk abinda yake wakana sannan yace zasuyi signing contract before abubuwa su wartsake masa zasu dinga bashi 10% percent na eibar da suka samu idan companies dinsa suka dawo zai biya su.

Abinda ya basa mamaki shine yanda sukayi caaa! Sukace Sam Sam basusan wannan labarin ba. Daga karshe ma watsewa sukayi ba’a gama meeting din ba hakan yasa ran yazeed ya baci kuma ya tabbatar da cewa hatta dan uwanka zai iya cutarka sannan sai ka shiga matsala zaka gane masu sonka.? Fita yayi suka tafi ainihin family house dinsu dake central area, hmm ba’a cewa komai domin yafi na Kaduna kyau masha Allah tabarakallah.

A parlour ya samu minal ga abinci an kawo Mata amma ta kasa ci tayi jungum jungum. Umma hanifa dattijuwa ce kuma me aikin su yazeed ne tun suna Abuja ganin batada kowa na dangi sai Allah yasa koda zasu bar Abuja basu sallame ta ba, sai suka barta yaci gaba da zama a gidan tana gyarashi kuma ana biyanta kudinta har yau sannan ba ita kadai bane akwai maids guda goma.
Gaishesa sukayi kamin suka watse, gaisawa sukayi da umma hani kamin ta basu waje saboda ta fahimci yana bukatar hakan.

Riko hannun minal yayi zuwa daki duk ta kagu taji yadda aka kaya suna shiga tace da fatan komai lafiya? Ajiyan zuciya kawai yayi, hakan yasa ta fahimci me yake nufi baki ta basa kamin ta dauki musu abinci yace AI bazai ci yasani ko akwai poison ta masa pancake kawai aiko haka akayi.

Kwanciya yayi bayan yayi sallar azahar ta ja masa bargo kamin ta koma kan couch ta fara nazarin yadda lamarin zai bille. Zaro ido yayi tare da murmushi alamar idea tazo Mata hakan yasa ta nufi jakar yazeed ta dauko paper da pen ta fara rubuta list. Sallan la’asar aka Kira hakan yasa ta tasheshi tana mai cigaba da rubutu. Daukewa yayi tare dayin bismillah yaga tanata rubutu baibi ta kanta ba yayi alwala ya fito still tana rubutu.

Sansadowa yayi ya warce papers tare da cewa me ki keyine? baby. Turo baki tayi tare da kokarin kwance paper dinta canja hannu ya fara yi sanda ya bata wahala kamin ya bata. Yace list din menene wannan tace list din kayan abinci ne. Dafatan akwai space a group building yace eh tace masha Allah daga gobe zamu fara saida snacks and desserts sannan zamu dinga yin contract na? abinci. Murmushi kawai yayi sannan ya tashi ya fice da sauri domin idonsa ya ciko da kwalla kar minal ta gani. Ita ko jikinta yayi sanyi ta dauka idea dinta ne bayaso hakan yasa ta yaga papern sannan ta fada gado ta fara kuka. Ace mijinta yana matsanancin hali kuma bazata iya taimaka wa ba?

Yazeed kam kukan farin ciki ne ya kama sa da nadaman yadda ya dinga treating dinta, Allah yasha dashi da ace ya sake ta da yayi baban asara. Komawa yayi yaga tana kuka yasa yayi saurin karasawa bakin gadon tare da fadin baby na lafiya kuma juyawa yayi ya kalli kujeran da suka zauna yaga ta yaga papern. Da sauri ya kwaso su kamin ya dawo gefenta ya zauna tare da fadin ya haka ? Me yasa kika yaga mana plan din? Cikin shessheka ta tashi tare da cewa na dauka bai maka bane ace kana da kudi kana da group ince maka ka fara saida abinci dukda cewa quantity da quality me kyau ne kuma naga cewa ba’a daukan shawaran Mata.

Murmushi yayi ya goge Mata hawaye tare da cewa wa yace miki na Rena shawaranki ? AI sana’a bata kadan albarka kawai ake nema. Batun shawara kuwa kin fini karfin tunani ma amatsayinki na mace. Murmushi tayi tace Allah? Yace kwarai kuwa mata ta sannan ya rungume ta.

Pieces din paper din ya bata kamin ya fita ya karbo glue ya like musu takardan sannan ya janyota suka baza shopping din kayan abincin su Dan da zafi zafi ake dukan karfe.
Gidan radio da talabijin aka sanar AI kan kace me wannan sun Sami order yafi dari saboda ana matukar son yazeed. Minal sanda ta tsorata ta fara? darewa tana ganin bazata iya ba yazeed yace karka damu zasu dinga Tahowa da masu aikin gidan su sai su dinga tayata, kuma ai shima yananan.

Haka suka dawo gida sunyi likis ranan da wuri suka kwanta 9pm a gado ta musu.

Kirrrrrr!kirrrrr!kirrrrrr!

Tsaki minal taja tare da sake shigewa jikin yazeed. Bacci sukayi bayan sunyi sallan subh sai suka saita Alarm din 6:30am suka saita dan shirya tafiya aikin su akan? lokaci, badan ranta yaso ba ta tashi suka shirya sai jeedmar group sai dadi takeji.

Direct area dinsu suka tafi banida girma office 3 ne a ciki ba manya sosai ba sai kitchen da reception. Aiki suka fara minal da yazeed na girki saura na packaging da branding. Sallah da cin abinci kawai suke tsayawa yi. Masu delivery nata yi. Ga orders 3 na biki yazeed in yayi aiki sai ya dawo ya goge wa minal gumi sai yaci gaba. Haka suka yi ta yi har yamma tukunna suka tafi gida gaba daya sunyi likis wanka da ruwan zafi sukayi, tare da sallah da cin abin ci. Sai gado a kwana a tashi cikin sati daya aiki ya fi karfin Dan mutum ga riba sun tara sosai kawai sai suka siya engine. Sosai sukayi dedicating time dinsu suna aikin su.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button